'Ko su kashe mutum ko mutum ya kashe kansa': in ji wata da ta tsira daga hannun masu safarar kwaya

Wata mata sanye da riga mai ɗauke da hoton mijinta da ya ɓata, tana ɗauke da wayarta mai hoton rigar mijin nata jini.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan uwan mutanen da suka ɓata sun riƙa gano 'yan uwan nasu ta hanyar ganin abubuwan da suka mallaka a sansanin Rancho Izaguirre
    • Marubuci, Darío Brooks
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
  • Lokacin karatu: Minti 6

Karon farko da jama'ar wajen suka fara ganin cikin sansanin Rancho Izaguirre, shi ne lokacin da wasu iyayen wasu yara da suka ɓata suka yi shirin Facebook na kai tsaye daga cikin wurin da ke yammacin Mexico.

Bayan samun makama kan wurin da ke ɗauke da kabarin mutane da dama, kungun mutane sun je sun tone wurin da fatan ganin wata alama ta 'yan uwansu da aka sace.

Abin da suka gani warin takalman mutane masu matuƙar yawa, kayan sawa da na amfani, jakankuna an binne su bayan gamawa da masu kayan.

Ya tabbata wajen kamar mallakar ƙungiyar 'yan bindiga ce ta Jalisco New Generation Cartel (CJNG), inda ake kashe mutane cikin dabara. An kuma gano wajen ne a watan Maris ɗin 2025, wani abu da ya girgiza mutanen Mexico ya kuma ja hankalin duniya baki ɗaya.

"Kamar dai wani wajen ɓautar da mutane ne da wannan gungun kngiyoyin masu safarar ƙwayoyi ke amfani da shi," in ji Sandra Romadia, Wadda ta yi magana da waɗanda suka tsira a littafinta, mai suna The Truth They Tried to Hide at Rancho Izaguirre.

"Abin da masu safarar ke fara yi shi ne yi wa mutane tayin aiki mai sauƙi a wurin. Kamar na injiniyan kwamfuta da aikin gadi da leburanci - kuma suna musu alƙawarin gwaggwaɓan biya. Suna haka ne ta manhajojin Facebook da Whatsapp, da sauran kafafen sada zumunta" kamar yadda Romandia ta shaida wa BBC Mundo.

"Ana yi wa matasa jarrabawa ne a wayoyinsu ko kuma ta hanyar aiken sakon karta kwana, idan aka zaɓi mutum, za a shaida musu za a aiko musu da tikitin motar bas zuwa madakatar mota ta Tlaquepaque da ke (Guadalajara), wadda take da matuƙar amfani - ɗaya daga cikin manyan da ake su a Jalisaco. In suka je mai motar Uber ne ke zuwa ya ɗauke su zuwa ofishin kamfanin.

"Me ke faruwa bayan haka? lokacin da Uber yazo - amma gaskiya abin da yake faruwa shi ne motar ba ta haya ba ce - tamkar sace su aka yi, ana musu kuma barazana da makamai , sannan kuma a kwace wayoyinsu, sannan sai a mayar da su zuwa sansanin Rancho Izaguirre ko kuma sauran wuraren da ake tilasta yi musu atisaye.

"Duk kuma wanda ya nemi ya yi turjiya kashe shi ake."

Hoton takalman mutane masu yawa da aka gani bayan mutane sun kai ɗauki wurin da suke.

Asalin hoton, GBJ

Bayanan hoto, Takalman mutanen da aka sace da kuma wasu kayyakinsu da aka gani a sansanin da aka rika ajiye su.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Waɗanda suka tsallake rijiya da baya sun bayyana mugun halin muguntar da suka tsinci kansu ciki, cikin har da faɗa da junansu da kuma azabtar da juna, ko kuma azabtar da duk wani mutun da ya tsaya kallon abin da yake faruwa.

"Suna kashe wasu mutane, su kori wasu, su ƙona wasu, su ci naman wasu yayin da wasu ke rayuwa cikin ɗaurin sarƙoƙi," in ji Romandia.

"Dolen waɗanda aka kama su yi aiki da irin tsarin da aka samar lokacin da suke son shiga wanka, su sanya wandunansu su cire kayansu, ana sanya su motsa jikin dole ko ko kuma a yi ta dukansu. Sun kuma bayyana yadda suka zama wasu abubuwan nishaɗi ga shugabannin masu sai da kwayoyin,"

"Hanya b iyu ce kawai ta barin nan wurin: ko dai su kashe mutun ko kuma ya kashe kansa," in ji wani da Romandia ta yi magana da shi a littafinta, inda ya bayyana yadda aka riƙa ƙarar da rayuwar matasa a sansanin.

Wani da ta sake magana da shi ya bayyana yadda halin cin zarafin ɗan adam ya ta'azzara a wajen - yadda aka riƙa yaudararsu da kuma tilasta musu shiga ƙungiyar, aka riƙa sace wasunsu tare da azabtar da su - inda ya ce ya yi amannar cikin muatne 100 da aka haɗa su tare ko wadanda suka rayu ba su kai 30 ba.

Ya kuma tuna yadda wata rana yana zaune ya ga wasu tawagar sabbin da aka kawo, a lokacin yana ɗauke da makami a hannunsa " na ji tamkar na yi wani abu domin kare su, amma na gaza yin komi saboda nasan idan na yi wani motsi zan sha duka ne har sai na gaji, dan haka ban iya yin komai ba."

"Dan haka sai ya yi tamkar shi ma wani mamba ne na gungun masu safarar kwayoyin domin dai ya samu ya tsira da rayuwarsa," in ji Romandia, "Amma a zuciyarsa yana ta tunanin yadda abin da zai yi ne ya ceci mutanen ne".

Hoton wani jami'in tsaro a cikin sansanin Rancho Izaguirre

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Satumbar 2024 jami'an tsaron ƙasar sun taɓa kai samame wajen, sai dai a lokacin ba a iya samun hujjar cewa ana aikata wani mugun abu ba a wajen.

Raul Servin mahaifin wani da aka ɗauka ya shaida wa BBC Mundo cewa, bayan sun samu labarin abin da ya faru sun je wurin kuma sun samun konson har sashi da kuma jakar harsashin da wani ƙatoton kabari mai ɗauke da abubuwa da kuma alamun an yi harbin bindiga a wurin.

Amma ofishin babban lauyan gwamnati da ke tafiyar da bincike kan lamarin ya ƙaryata akwai shaidar ana ƙona mutane a wurin ko kuma wurin da ake zubar da sauran sassan jikin ɗan adam.

"Binciken ya tabbatar da cewa ana amfani da wuri ne a matsayin sansanin ba da horo" in ji Ofihsin babban lauyan ƙasa a ranar 5 ga watan Maris ɗin bara.

Tun daga wannan lokacin an kama mutum 47 da ke da alaƙa da sansanin, sannan an yankewa mutane 10 zaman gidan yari na shekara 141 saboda ɓatan mutane da kuma kashe wasu mutane uku a sansanin.

An kama magaajin garin Teuchitlán, inda sansanin yake ana zarginsa da haɗa kai da ƙungiyar.

a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton sansanin da hukumomin Mexico suka gudanar da bincike a kai.

"Kamar dai hukumomi na ƙoƙarin tattare bayanan da ke faruwa ne," in ji Romandia.

"Ko da yaushe ofishin lauyan gwamnati na cewa zai yi bayani kan wannan shari'ar ba tare da ɓoye komai ba, amma ba tare da son tabbatar da cewa akwai wajen ƙona mutane ko narkar da ƙashin mutane ba, ana ganin suna hakan ne domin kar a kawowa binciken tarnaƙi.

"Damuwar shi ne ba sa bayyana abubuwan da ke faruwa ga al'umma. Wani lokacin mai shigar da ƙara na gwamnati Alejandro Gertz Manero ya taɓa tabbatar da cewa an samu wani wajen narkar da jikin mutane a wajen, lokacin da muka ga hotunan da aka sa mun tabbatar da jikin mutane ne a wajen.

"Wasu masana kimiyya sun ce alamu na nuna an zarce shakara sama da 10 ana ƙona mutane a wurin."

BBC Mundo ta nemi tattaunawa da ofishin babban lauyan gwamnatin Mexico kan wannan shari'ar, sai dai har lokacin hada wannan rahoton ba su amsa mana gayyatarmu ba.

Mutane biyu sun riƙe juna suna kuka kusa da sansanin Rancho Izaguirre.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum 16,000 ne aka ba da rahoton ɓatansu a Jalisco kamar yadda hukumomi suna fitar da bayanai

Sama da mutum 130,000 ne aka ba da rahoton sun ɓata a Mexico. Kuma kusan dukkan ɓatan da aka samu ya faru ne a 2007, lokacin da shugaba Felipe Calderon ya ƙaddamar da yaƙi da miyagun kwayoyi.

A lokuta da dama waɗanda aka sacen an riƙa tilasta musu shiga harkar kwayoyin wasu kuma da suka yi turjiya an riƙa kashe su.

Romandia ta yi amannar akwai wasu yankunan Jalisco da ke buƙatar a ƙara gudanar da bincike cikinsu, bayan mutanen da ta tattauna da su sun bayyana cewa akwai ƙarin sansanonin gungun a Jalisaco.

"Matasa ne ke ɓata a-kai-a-kai," in ji Romandia. "A wajena wannan binciken bai sauya komai ba.

"Akwai batun tsangwama wanda yake da muhimmanci a Mexico, mutanen da suka bata aka gansu ne suke fuskantar hakan, saboda ana zarginsu da hannu cikin lamuran gungun da kuma safarar mutane.

"Muna ƙara ganin batutuwa da dama, a 'yan shekarun bayan nan, na ƙananan yara da matasa da kuma magidanta da ake tilastawa shiga lamarin.

"Ana ɗaukar wasu ne saboda iliminsu - musamman waɗanda suke injiniyoyi da magina da jami'an lafiya da dai sauransu.".