Mun koma amfani da sabuwar manhaja

| Game da manhajar BBC World Service |
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sauke sabuwar manhaja

Latsa nan don sauke manhajar BBC daga Google Play kan na'urorin Android

Latsa nan don sauke manhajar BBC daga App Store a kan iPhone da iPad

Matashiya: Babu manhajar a Birtaniya ko Amurka kuma babu na harshen Ingilishi.

Game da manhajar BBC World Service

Manhajar BBC World Service wani dandali ne guda ɗaya da ke kawo labaran BBC a harsuna da dama. Za ku zaɓi harshen da kuke so domin samun labaran da ƴan jarida na wannan sashen suka shirya muku daga yankinsu da kuma faɗin duniya.

Ku samu labarai daga kafar aikin jarida mai inganci wadda ke fayyace muku komai dalla-dalla, kuma ku lura don gudun faɗawa tarkon yaɗa labaran ƙarya. Ku samu rahotanni da labaran bidiyo kai-tsaye, ku saurari shirye-shirye da rahotannin bidiyo, duk a wuri ɗaya.

Matashiya: Babu manhajar a Birtaniya ko Amurka.

Labaran gida da waje babu nuna son rai, manyan labarai da sharhi

Kanun labarai, maƙala da sharhin masana

Labarai da ɗumi-ɗumi da rahoto kai-tsaye

Ku san abubuwan da ke faruwa a duniya

Ankararwar manyan labarai

Amince domin samun ankwararwa a na'urarku da zaran an wallafa labari.

Game da BBC

British Broadcasting Corporation kafar yaɗa labarai ce ta al'ummar Birtaniya – tana samar da labarai masu inganci, sharhi da nishaɗantarwa a Talabijin, rediyo, shafin intenet da shafukan sada zumunta.

Kafa ce mai zaman kanta wadda ba ta samun katsalanda na siyasa ko ƴan kasuwa, kuma tana aiki ne ƙarƙashin dokar masarauta ta 'royal charter' wadda hakan ke tabbatar da ƴancin kafar.

BBC na da ofisoshi a birane 64 da ke ƙasashe 54.

Mene ne BBC World Service?

BBC World Service sashe ne da ke samar da labarai cikin harsuna 45 har da Ingilishi ta hanyar bidiyo, murya da kuma shafukan intanet. Ta sashen BBC World Service, labaran da kafar ke yaɗawa na isa ga mutane miliyan 503 a kowane mako, kuma ita ce kafar da al'umma suka fi amincewa da ita kuma suke dogaro da ita saboda kasancewarta maras nuna bambanci, a tsakanin kafafen yaɗa labarai.