Dalilai 5 da za su hana Tinubu zuwa wasu jihohin Najeriya kamfe

Bola Tinubu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A Najeriya 'yan hamayya sun fara mayar da martani akan kalaman shugaban kasar da ya ce ba zai iya raka mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na jam'iyyar APC zuwa dukkan jihohin da za su gudanar da kamfen gabanin babban zaɓen 2027 ba.

Wasu daga cikin jam'iyyun sun bayyana matakin da cewa nuna gazawa ce a fili da ke alamta cewa bai cancaci a sake zabensa ba, saboda bai yi wa yan kasar ayyukan da zai iya komawa wurinsu neman kuri'a ba.

Jam'iyyun hamayya suna ci gaba da caccakar shugaban Najeriya Bola Tinubu, bayan da ya bukaci kwamitin yakin neman zabensa su kai saƙon jam'iyyar APC ga ƴan Najeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi a madadinsa saboda ya ce akwai abubuwan da suke buƙatar ya mayar da hankali kan gudanar da su a lokacin da ake yawon kamfe din.

Ga alama wannan batun ya tayar da kura saboda yadda jam'iyyar ADC ta zargi shugaba Tinubu da rashin tabuka komai a matsayin dalilin da ya ce ba ko ina zai je ba lokacin yakin neman zaben.

Dalilan da Tinubu ya bayar

A yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya halartar taron yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohin Najeriya ba saboda dalilai kamar haka:

• Mayar da hankali kan shugabanci: Ya bayyana cewa nauyin dake kansa na shugaban ƙasa ya fi masa muhimmanci, kuma an ba shi shawarar ya fi mayar da hankali wajen gudanar da aikin ƙasa maimakon kashe lokaci a fagen kamfen a ko'ina.

• Samun damar tattaunawa da kuma ci gaba da aiki: Ya yi alƙawarin cewa zai tsara wani shiri na musamman don tattaunawa kai tsaye da 'yan Najeriya maimakon zuwa kowane gangami a kowace jiha da ƙaramar hukuma.

• Ziyartar jihohi 12: Maimakon zagaya dukkan jihohi, an tsara zai ziyarci manyan jihohi 12 ne kawai a shiyyoyi shida na ƙasar don gudanar da kamfen ɗin APC na 2027 (da suka haɗa da Kaduna, Rivers, Plateau, Oyo, Borno, Enugu, Bauchi, Sokoto, Delta, Kano, Adamawa, da Lagos)

• Biyan basukan ƙasashen ƙetare: Tinubu ya bayyana cewa gwamnati tana da wasu muhimmar abubuwa musamman na biyan basukan kuɗaɗe da ya kamata ta maida hankali a kai, saboda haka gudanar da mulki a wannan lokaci yana buƙatar kulawarsa sosai.

• Jan hankalin masu zuba jari: Ya ƙara da cewa ƙasar tana kan matakin ci gaba da janyo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje ne a yanzu, wanda hakan ke buƙatar kasancewarsa a ofis don tabbatar da dorewar manufofin tattalin arziki.

Bayan kaddamar da kwamitin yakin neman sake zaben shugaba Tinubu, ana sa-ran ranar 24 ga watan Oktoba na 2026, ne jam'iyyar APC za ta fara gudanar da gangamin yakin neman zaben a Kaduna.

Me ƴan jam'iyyar adawa ke cewa?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Faisal Kabir, daya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ADC a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, babu wani maganar aiki da ya sha kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da zai hana shi yakin neman zabe saboda duka-duka bai jima ba da ya dawo daga kasar Faransa.

Ya ce," A tsawon wa'adin mulkinsa ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa kasashen duniya, to dan haka mu muna ganin abu guda ne zai hana 'yan Najeriya zuwa jihohi domin yakin neman zabe shi ne bai tsinanawa 'yan kasa komai ba in ban da wahala da talauci ga rashin tsaro."

" To wannan dalilin ne ya sa ya ke tsoro kada ya je mutane su yi masa ihu ko su jefasa koma su yi bore, shi ya sa ya ce zai kauracewa wasu taruka na zuwa yakin neman zabe." In ji shi.

Faisal Kabir, ya ce," Babu wani aiki da Asiwaju Bola Tinubu ya rage da zai yi wa 'yan Najeriya wanda a cikin shekara uku da rabi bai yi su ba, domin a cikin shekara uku da rabi ace ba ka yi wa 'yan Najeriya wani abu ba sai a cikin watanni uku ai akwai abin mamaki."

Ita kuwa jam'iyyar NDC cewa ta ke wannan abu ya tabbatar musu da abin da suke zargi, Ibrahim Hussain Abdulkarim makusanci ne ga Peter Obi dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ya shaida wa BBC cewa, suna ganin mutum ne wanda bai yi wa mutane abubuwan da suka kamata ba.

Ya ce," Bai san abin da zai fada ba idan ya je yakin neman zabe, haka su ma 'yan sakonsa ba su fada masa gaskiyar abin da ke faruwa ba, muna ganin abin da ya faru ke nan shugaban ya ce ba zai iya zuwa dukkan jihohi yakin neman zabe ba."

" Da a rinka tafka ana warwara, gara a fito a fada mana cewa wannan mutumin ya gaza ba zai iya ba, kuma muma mun san bai zai iyan ba." In ji shi.

Shirin da jam'iyya mai mulki ta yi na kamfe

Yayin da lokacin gudanar da yakin neman zaben ya fara a hukumance a ranar Laraba, hankula sun karkata kan yadda jam'iyyar APC mai mulki za ta yi amfani da babban tsarinta na siyasa a fadin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya - Abuja domin gudanar da yakin neman zaben.

Jam'iyyar mai mulkin Najeriya ta ce za ta bayyana cikakken shirinta na yakin neman zaben 2027 nan ba da jimawa ba.

Sai dai ta ce ba za ta yi gaggawar fara tarukan gangami ba da zarar lokacin yakin neman zabe ya fara.

Sakataren yada labaranta, Barrista Felix Morka, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, ranar Litinin, bayan wani taron kusan sa'a uku da kwamitin zartarwa na jam'iyyar ya gudanar a hedikwatarta da ke Abuja.

Morka ya ce duk da cewa INEC ta kayyade ranar 19 ga Agusta a matsayin ranar fara kamfe, babu wata doka da ta tilasta wa jam'iyyu fara gangami a ranar.

Ya ce: "19 ga Agusta ita ce ranar da INEC ta ware domin dukkan jam'iyyu su fara yakin neman zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya. Amma babu wata doka da ta ce dole ne mu fara a wannan rana. Abin da doka ta haramta shi ne fara kamfe kafin wannan rana."

Ya kara da cewa APC na ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da 'yan takararta domin tsara wani tsari na yakin neman zabe da zai kasance cikin daidaito a fadin kasar, maimakon yin gaggawar fara gangami.

Yaushe za a fara kamfe a Najeriya?

A ranar Larabar nan ne 19 ga watan Agusta 2026 za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a hukumance a Najeriya, kamar yadda hukumar zaben kasar INEC ta bayyana.

A bayananta hukumar ta ce, daga ranar jam'iyyu da 'yansiyasa za su fara yakin neman zaben har zuwa jajiberin ranar kada kuri'a - sa'a 24 kenan da za a gudanar da zaben na shekara mai zuwa - 2027.

A tattaunawarta da BBC, mai magana da yawun hukumar zaben ta Najeriya, Zainab Aminu Abubakar ta bayyana hakan:

''Kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanadar, sashe na 94, sakin layi na biyu, ya bukaci jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe na zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisu na tarayya, kwanaki 150 kafin ranar zabe.''

''Kuma duba da jadawalin zaben 2027 hukumar zaben ta ayyana yau 19 ga watan Agusta a kan ranar da za a fara wannan gangamin yakin neman zaben wadannan kujeru,'' in ji ta.

Za a yi zaben na shugaban kasa ne da 'yan majalisun tarayya - na dattawa da kuma na wakilai ranar 14 ga watan Janairun 2027, kamar yadda jadawalin hukumar zaben ya nuna.