Me ke haifar da yawan saɓani tsakanin masoya ko ma'aurata?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Sophie Hardach
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Abin da masu ba da shawarar zamantakewar ma'aurata suke so ku sani game da ƙoƙarin ceto dangantakarku da ke gab da rushewa.
Idan ka na cikin wata dangantaka da ba ka samun farin ciki a cikinta, wataƙila kana fama da abin da ake kira "raɗaɗin zuciya".
Yawan faɗace-faɗace masu tsanani tsakanin ma'aurata na iya kawo tangarɗa ga barci da haifar da matsananciyar damuwa. Haka kuma, suna iya sa dukkan na kusa, har da yara, su kasance cikin haɗarin samun matsalolin lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa.
A gefe guda kuma, kyakkyawar dangantaka mai cike da gamsuwa na iya inganta lafiyarka, har ma ta taimaka wajen tsawaita rayuwarka.
A gaskiya ma, masana sun ɗauki alaƙar soyayya ko aure mara inganci a matsayin wata babbar matsala ga lafiya, wadda ta kai ko ma ta fi haɗarin shan taba sigari ko rashin motsa jiki.
Baya ga haka kuma, akwai abin da ake kira raɗaɗin zuciya a ma'anar da aka saba amfani da ita, wato baƙin ciki da wahalar da mutum ke sha lokacin da soyayya ta fara lalacewa ko ta rushe.
To, ta yaya za a sauya dangantaka mara daɗi zuwa wadda take cike da farin ciki da gamsuwa? Kuma shin hakan ma yana yiwuwa kuwa?
Sabbin bincike-bincike da ke ƙara fitowa suna bayar da amsoshi masu ban mamaki ga waɗannan tambayoyi, tare da ƙara wa ma'auratan da suka kuduri aniyar gyara zamantakewarsu kyakkyawar fatar cewa har yanzu akwai yiwuwar kawo sauyi mai ma'ana a alaƙarsu.
Me ya sa masoya ke samun saɓani?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan ka fara sabuwar alaƙa, kuma rigimar farko da ka yi da masoyiyarka ta ɗauki lokaci mai tsawo, mai yiwuwa tun daga lokacin za ka fara hango abin da ke tafe.
Bincike ya nuna cewa batutuwan da ke haddasa saɓani tsakanin masoya ko ma'aurata kan ci gaba da kasancewa iri ɗaya a tsawon alaƙarsu. Ana kiran irin waɗannan matsaloli da matsalolin da ba sa ƙarewa ko kuma matsalolin da ke zama tamkar alaƙaƙai.
A cewar Carrie Cole, wata masaniyar ilimin halayyar ɗan'adam kuma daraktar bincike a Cibiyar Gottman da ke Seattle a Amurka, waɗannan matsalolin da ba a warware ba na iya kasancewa masu alaƙa da harkokin kuɗi, tarbiyyar yara, rayuwar aure, ko yadda ma'aurata ke yanke hukunci da kasafta iko a tsakaninsu.
Sai dai kuma suna iya shafar abubuwan da ake ganin ƙanana ne, kamar tsaftace gida da gyara kayan da aka yi amfani da su.
A wani bincike na dogon lokaci, masanin ilimin halayyar ɗan'adam John Gottman da tawagarsa sun lura da yadda ma'aurata ke muhawara da juna a wata ganawa ta farko, sannan suka sake nazarin halayensu bayan shekaru huɗu.
Sun gano cewa a kusan kashi 69 cikin 100 na lokuta, ma'auratan har yanzu suna taƙaddama ne kan batutuwa iri ɗaya da suka tattauna shekaru huɗu da suka gabata.
Sauran nazarce-nazarce ma sun nuna irin wannan yanayi, inda aka gano cewa wasu muhimman batutuwa, musamman da suka shafi kuɗi, suna haddasa rikici a gidaje ba tare da la'akari da al'ada ko ƙasar da mutane suke ba.
Rikice-rikicen da suka shafi kuɗi ne ma suka fi zama masu tsanani kuma masu ɗaukar lokaci kafin a warware su. Haka kuma, rashin daidaito wajen raba ayyukan gida wani muhimmin abin tayar da hankali ne da zai iya ƙara haɗarin rabuwa ko saki.
Sai dai kasancewar ma'aurata ba su yarda da juna a kan wani abu ba, ba lallai ne ya zama alamar matsala ba.
A wasu lokuta, samun saɓani wani ɓangare ne na koyo da fahimtar buƙatun juna da yadda za a biya su. Bugu da ƙari, ma'aurata ko masoya da ke cikin zaman lumana ma suna samun saɓani kamar yadda waɗanda ba sa jin daɗin zamansu suke yi.
Abin da bincike ya nuna shi ne cewa babban bambanci tsakanin masoya ko ma'aurata da ke zaman farin ciki da waɗanda ba su da farin ciki ba ya ta'allaka ne ga yawan rigingimun da suke yi.
Maimakon haka, bambancin yana cikin yadda suke mu'amala da juna, ko lokacin da suke gardama ko ma a lokutan da babu wata gardama a tsakaninsu.
Abu huɗu da ke lalata zamantakewa
Halaye huɗu da za su iya "rusa" alaƙa:
A cewar bincike, Carrie Cole ta bayyana wasu halaye huɗu da ke nuna cewa dangantaka na iya kaiwa ga rabuwa. Waɗannan su ne:
- Yawan suka da zargi
- Wulaƙanci da raini
- Kare kai a kowane lokaci ba tare da sauraren ɗayan ba
- Yin shiru ko janye kai gaba ɗaya daga tattaunawa da rikici
Cole ta ce: "Waɗannan halaye huɗu na iya kashe dangantaka." Amma ta ƙara da cewa, idan ma'auratan suna da niyyar gyara zamansu, ana iya magance su.

Asalin hoton, Getty Images
A gaskiya ma, ba dangantaka kaɗai ke fuskantar haɗari ba. Wasu bincike-bincike sun nuna cewa yawan suka da zargin da mutum ke sha daga abokin zamansa na iya kasancewa wata alama da ke ƙara haɗarin mutuwa da wuri.
Rigingimun da suka ƙunshi irin waɗannan halaye, tare da nuna ƙiyayya da tashin hankali, ana kallon su a matsayin rikice-rikice masu lalata dangantaka, kuma a ƙarshe suna iya ƙara haɗarin saki ko rabuwa.
Sai dai a gefe guda, gardama mai ma'ana wadda take gudana cikin mutuntawa, girmama juna, fahimtar juna da neman mafita tare, na iya ƙarfafa alaƙa.
Sake tunani da ƙara tausayi
Wani muhimmin abu a alaƙar soyayya shi ne mutum ya ji cewa abokin zamansa yana sauraren shi, yana fahimtarsa kuma yana nuna masa goyon baya.
Lokacin da mutum yake ganin abokin zamansa yana kula da damuwarsa da bukatunsa, hakan yana ƙara gamsuwa a zamantakewa, kuma yana iya rage wasu matsalolin lafiya tare da taimakawa wajen samun rayuwa mai tsawo.
Haka kuma, nuna alheri da haɗin kai na iya samar da kyakkyawar dangantaka mai ɗorewa. Wani bincike da ya ɗauki shekaru 20 ya gano cewa yanke shawara tare da kuma raba ayyukan gida cikin adalci na da alaƙa da ƙarin farin ciki a aure da rage yawan rikice-rikice.
Har ma yadda ma'aurata ke gardama na iya shafar barcinsu. Bincike ya nuna cewa gardama mai cike da zagi da cin fuska tana haddasa rashin ingantaccen barci, yayin da tattaunawa cikin girmamawa ke taimakawa samun kyakkyawan barci.
Sake gina tausayi da fahimtar juna
Idan kana cikin dangantakar da ba ta da daɗi, sau da yawa yana iya zama kamar ba zai yiwu a daina gardama cikin fushi da ƙiyayya ba domin komawa tattaunawa cikin mutuntawa. Sai dai masana sun ce akwai ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa hakan yana yiwuwa, musamman ta hanyar neman shawarar ƙwararru.
Bincike ya nuna cewa shawarwarin zaman aure ko soyayya na taimakawa kusan kashi 70 cikin 100 na ma'auratan da suka nemi irin wannan taimako.
Irin wannan taimako na iya:
- Magance matsalolin dangantaka
- Ƙara gamsuwa tsakanin ma'aurata
- Rage damuwa a zamantakewa
- Ƙarfafa kusancin zuciya da soyayya
- Inganta lafiyar tunani da ta jiki
Jay Lebow, masanin ilimin halayyar ɗan Adam kuma ƙwararren mai ba da shawara kan zamantakewar ma'aurata, ya ce:
"A mafi yawan ma'auratan da ke neman taimako, tausayi da fahimtar juna sun ragu sosai."
A cewarsa, babban aikin da ake yi a lokacin shawarwari shi ne amsa tambayar:
"Ta yaya za mu sake gina tausayi da fahimtar juna?"
Daya daga cikin alamomin da ke nuna ana samun ci gaba shi ne inganta sadarwa.
"Mutane su iya magana da kuma sauraron juna da kyau. Wannan na iya zama abu mai sauƙi a gani, amma idan dangantaka tana cikin matsala, sauraron ɗayan mutum kan zama abu mai matuƙar wahala."
Ya kuma ce gyaran dangantaka yana buƙatar ma'aurata su dakata su tambayi kansu:
"Me ke faruwa tsakaninmu?" maimakon su mayar da hankali kawai kan kurakuran da suke gani a wurin abokin zamansu.
"Faɗa min wani abu daban"
Carrie Cole ta ce akwai manyan alamu biyu da ke ba ta fata yayin da take aiki da ma'aurata.
Na farko shi ne idan ɗaya daga cikin ma'auratan ya ce wa ɗayan:
"Na fahimci dalilin da ya sa kake ji haka."
A cewarta, wannan yana nuna cewa mutum yana amincewa da ra'ayin abokin zamansa, ko da bai yarda da shi gaba ɗaya ba.
Wata alama kuma ita ce son sanin yadda ɗayan yake tunani.
Ta ce: "Idan har yanzu akwai sha'awar fahimtar juna, to akwai fata."
Ko da suna saɓani, za ka ji ɗaya na cewa:
"Ka faɗa mini ƙarin bayani. Ta yaya ka kai ga wannan ra'ayi?"
A cewar Lebow, idan ma'aurata suna shirye su yi aiki kan matsalolinsu, yawanci ana samun sakamako mai kyau.
Fahimtar burin juna
Don warware matsalolin da suka daɗe suna haddasa rikici, Cole ta ce yana da muhimmanci a fahimci burin rayuwa da mafarkin juna.
Ta bayar da misalin wasu ma'aurata da suka riƙa taƙaddama kan kuɗi.
Dukansu sun tashi cikin talauci, amma hakan ya shafi rayuwarsu ta hanyoyi daban-daban.
Matar tana son samun cikakken tsaro na kuɗi ta hanyar ajiya da tsara kashe kuɗi cikin tsauri.
Mijin kuwa yana son ya more kuɗin da ya samu da wahala, ya saya wa kansa abubuwa masu kyau kuma ya ji yana rayuwa kamar sauran mutane.
Wannan ya haifar da sabani mai tsanani a kan yadda za a kashe kuɗi.
Cole ta ce: "Sun yi shekaru suna gardama ba tare da sun taɓa fahimtar ainihin dalilin da ke haddasa rikicin ba."
A lokacin shawarwari, suka ba juna damar bayyana irin wahalhalun da suka sha a lokacin ƙuruciyarsu da yadda hakan ya tsara manufofin rayuwarsu.
Daga baya suka cimma matsaya kan adadin kuɗin da za su tara a matsayin ajiya da kuma adadin da za su rika kashewa domin jin daɗi.
Cole ta ce: "Sun sami mafita ne bayan sun fahimci abin da ya fi muhimmanci ga kowannensu."
Muhimmancin niyya
Lebow ya ce niyyar ma'aurata na gyara dangantaka tana da matuƙar muhimmanci.
A cewarsa: "Ko da ka samu mafi ƙwararren masani a duniya, idan ma'auratan ba su da niyyar gyara dangantakarsu, sakamako mai kyau ba zai yiwu ba."
Amma idan suna da ƙwazo da niyyar gyarawa, ko da mai ba da shawarar ba shi da ƙwarewa sosai, za a iya samun sakamako mai gamsarwa.
Wani lokaci rabuwa ce mafita
Lebow ya ce har ma ma'auratan da suka yanke shawarar rabuwa za su iya amfana daga shawarwari.
Hakan na iya taimaka musu:
Rage rikice-rikice yayin rabuwa
Kare lafiyar tunaninsu
Kula da lafiyar tunanin 'ya'yansu idan suna da yara
Ya ƙara da cewa duk da cewa saki ko rabuwa na iya zama mai matuƙar raɗaɗi:
"Lokaci ne da mutum zai iya koyo abubuwa masu yawa game da kansa."
Mutane da yawa, in ji shi, suna gano darussa masu muhimmanci da za su amfane su har tsawon rayuwarsu.
A ƙarshe, ya jaddada cewa koyon sauraron juna da nuna tausayi ba ga ma'auratan da ke cikin matsala kaɗai yake da amfani ba.
"Ko ma'auratan da ke cikin kyakkyawar dangantaka za su iya ƙara inganta zamansu idan suka ci gaba da koyon waɗannan dabaru."




























