Me ke yawan gwara kan Kwankwaso da Atiku?

Asalin hoton, X/Multiple
Yayin da ake ta tattaunawa kan yiwuwar haɗakar manyan ƴan'adawa gabanin zaɓen 2027, rikici tsakanin manyan jagororin hamayya na ƙara haifar da koma bayan yunƙurin haɗewar ƴanhamayyar.
Musayar yawun da ta ɓarke a baya-bayan nan tsakanin jagoran kwankwasiyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NDC da kuma jam'iyyar ADC na ci gaba da aza ayar tambaya kan fatan haɗewar.
A wannan wata ne sabon rikici ya ɓarke tsakanin ADC da Kwankwaso bayan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugabna ƙasa na ADC ya zargi Kwankwaso da mayar da hankali wajen sukar Atiku Abubakar maimakon APC.
Lamarin da har ta kai ga kwamitin yaƙin neman zaɓen Atikun ya zargi Kwankwaso da taimaka wa jam'iyya mai mulki.
Sai dai Kwankwaso ya musanta zargin, yana mai cewa shi da jam'iyyarsa ko shi ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsa ta NDC, Peter Obi ba sa yi wa APC aiki, kuma ba za su janye wa Atiku takara ba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, Kwankwaso ya ce maimakon ADC ta mayar da hankali wajen nuna cancanta da ƙwarewar ɗan takararsu, suna ƙoƙarin yaɗa zarge-zarge cewa NDC na yi wa APC aiki, ko kuma za ta janye wa ADC.
Kodayake Atiku da Kwankwaso sun taɓa yin aiki tare a ƙarƙashin jam'iyyun siyasa daban-daban, dangantakarsu ta fuskanci ƙalubale a lokuta da dama, musamman kan batun shugabanci, rabon iko da kuma wanda zai jagoranci ƙawancen adawa.
Lokutan da ƴansiyasar suka soki juna a baya-bayan nan

Asalin hoton, kwankwaso/X
Dangantakar siyasa tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar ta sha fuskantar tangarda a lokuta daban-daban.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun daga rushewar tattaunawar haɗaka kafin zaɓen 2023 zuwa rikicin da ya kunno kai a cikin ADC, ɓangarorin biyu sun riƙa musayar kalamai masu zafi.
Ga jerin wasu lokuta da ƴansiyasar biyu suka soki juna.
- Rikicin haɗakar PDP da NNPP kafin zaɓen 2023
Bayan tattaunawar haɗaka ta rushe, Kwankwaso ya yi zargin cewa wasu jiga-jigan PDP - wadda Atiku ke yi wa takara a lokacin - ba su nuna masa adalci ba a tattaunawar da suka yi da shi.
Duk da cewa bai yawaita ambaton Atiku kai tsaye ba a lokacin, kalamansa sun kasance suna nuni ga tawagar Atiku da tsarin da PDP ta zo da shi.
- Batun takarar 2027
A watan Oktoban 2026, Kwankwaso ya ce ya shawarci wata tawagar Fulani da su roƙi Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a makon da ya gabata yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels.
Ya ce tawagar ta kai masa ziyarar girmamawa ne a gidansa, kuma ya yi amfani da damar wajen buƙatar su shawo kan Atiku ya haƙura da takarar.
- Lokacin da ya ce "Atiku ba shi da wani sabon abu da zai kawo"
A wani martani da ya yi a baya-bayan nan kan zargin da ADC ta yi masa, Kwankwanso ya ce Atiku da ADC "ba su da wata mafita mafi kyau ga Najeriya."
Wannan kalamin na daga cikin mafi tsaurin suka da ya yi wa Atiku a baya-bayan nan.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Jagoran na Kwankwasiyya ya ce "duk da cewa gwamnatin APC ta gaza, ita ma ADC da Atiku ba su da wani kudiri mai kyau na gyaran Najeriya''.
A nasa ɓangare shi ma Atiku da jam'iyyarsa ta ADC sun sha sukar Kwankwaso ko mayar masa da martani kan wasu zarge-zarge da ya yi musu, ga kuma wasu daga ciki.
- 'Kwankwaso ya fi mayar da hankali kan Atiku'
Jam'iyyar ADC ta fito fili tana cewa Kwankwaso ya fi sukar Atiku da jam'iyyarsu fiye da yadda yake sukar APC.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar ya ƙalubalanci Kwankwaso da ya fito fili ya shiga jam'iyyar APC idan har yana goyon bayan manufofinta na siyasa.
A martanin da kwamitin ya yi kan sukar da ta ce Kwankwason ya yi wa jam'iyyar da kuma ɗantakarata, ya zargi Kwankwaso da mayar da hankali wajen sukar Atiku da ADC, maimakon Tinubu da APC.
Kwamitin ya ce kamata ya yi Kwankwaso ya mayar da hankali wajen ɗora wa jam'iyyar APC mai mulki alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki da matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta, maimakon ci gaba da sukar ADC da Atiku.
- 'Kwankwaso ya yi APC aiki'
Kwamitin yakin neman zaɓen Atikun ya kuma zargi Kwankaso da yi wa Tinubu da APC aiki.
Cikin wata sanarwar martani ga Kwankwason da daraktan yaɗa labaran yaƙin neman za ben Atikun, Kola Ogbondiyan ya fitar, ya zargi Kwankwaso da yi wa APC da Tinubu aiki ne a fakaice.
Mista Ogbondiyan ya bayyana kalaman Kwankwason a matsayin waɗanda suka fi kare muradun kansa, tare da cewa suna da haɗarin ƙara rarrabuwar kai a tsakanin jam'iyyun adawa.
Shin Atiku da Kwankwaso za yu iya zama wuri ɗaya?

Asalin hoton, X/Multiple
Doka Kabiru Sa'id Sufi, masanin siyasa ne, kuma mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya ya ce akwai abubuwa biyu muhimmai a suke tsaiko wajen zaman ƴansiyasar guda biyu a inuwa ɗaya.
"Na farko dai duk da kasancewar idan aka duba tarihi ƴan gidan siyasar gida ɗaya ne wato gidan fadama kuma ƴan taɓo ne, amma da aka shiga mulkin Obasanjo, sai su Kwankwaso da wasu ministoci irin su Nasir El-Rufai suka zama na hannun daman Obasanjo a lokacin a Atiku da Obaanjo suna takun-saƙa."
Masanin siyasar ya ƙara da cewa abu na biyu mai muhimmanci shi ne dukkan ƴan siyasar biyu yanzu burinsu ɗaya ne.
"Tun bayan da Atiku ya yi zango biyu na mataimakin shugaban ƙasa, shi kuma Kwankwaso ya yi gwamna biyu, sai ya zama dukansu buƙatarsu kusan ɗaya ce.
''Yanzu dukansu burinsu zama shugaban ƙasa ne, shi ya sa yake da wahala su haɗu a waje ɗaya, har gara Kwankwaso ma zai iya zama mataimakin shugaban ƙasa."
Dokta Sufi ya ƙara da cewa magoya baya na tasiri sosai a siyasar jagororinsu.
"Saboda kowannensu magoya bayansu ba sa fahimtar juna, har sukan jefi juna da maganganu. Su kan su jagororin sukan yi gugar zana a tsakaninsu," in ji Kabiru Sufi.
































