Abu 5 da za ku riƙa yi domin ku burge mutane

.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Idan kana son ka zama mai jan hankali kamar Tom Cruise ko Taylor Swift, maimakon ka ɓata lokaci da kuɗi sosai wajen canza kamanninka, ya fi kyau ka mai da hankali kan halayenka.

Masoyansu da waɗanda suka taɓa yin hira da su sau da yawa suna bayyana su a matsayin mutane masu halaye na musamman.

Cruise da Swift mutane ne masu yawan magana, fara'a da murmushi, kuma sun iya mu'amala da mutane. Suna nuna cikakkiyar sha'awa ga mutumin da suke magana da shi, kuma suna fahimtar yanayin zamantakewar da suke ciki.

Wannan ya yi daidai da binciken ilimin halayyar ɗan Adam. Hakika, daga farkon haɗuwa da mutum kamanninsa na iya jan hankali, amma yayin da kuke ƙara mu'amala da juna kuma kuka san juna sosai, abu mai muhimmanci tsakaninku shi ne halayen mutum da yadda kuke fahimtar juna.

Ita zuciya na son mai ƙyautata ma ta, dan haka ga hanyoyi guda biyar da masana ilimin halayyar ɗan Adam suka zayyana da za su taimaka maka ka ƙara jan hankali da kwarjini a idanun mutane.

1. Hulɗa da jama'a

..

Bincike ya nuna, mutanen da suke haba-haba da faran-faran da jama'a, na jan hankali sosai da ƙyautata mu'amala a karon farko da aka haɗu da su.

Wannan na da nasaba da yadda suke nuna kyawawan ɗabi'u da fara'a da raha da sanya wasu dariya, idan su na magana kuwa kalaman da ke fitowa daga bakinsu tausasa ne cike da ƙwarin gwiwa.

Hakan na faruwa idan dama can waɗannan mutanen su na shiga da yin mu'amala mai ƙyau da wasu.

...

Ko da ba ka saba yin hulɗa da mutane da yawa ba, ka yi ƙoƙarin nuna wasu daga cikin halayen.

Idan kai natsuttse ne kuma ka fi son kasancewa kai kaɗai, to wani bincike ya nuna cewa; mutane masu irin wannan hali suna jin daɗin su na ƙoƙarin yin mu'amala da jama'a da shiga harkokin zamantakewa fiye da yadda suke tsammani tun da farko.

Wato, ko da kana ganin fita da mutane ko yin hira da baƙi zai yi maka wahala ko ba zai kayatar da kai ba, sau da yawa idan ka yi ƙoƙarin yin hakan, za ka ji daɗi kuma ka amfana fiye da yadda ka yi zato.

Wannan na nuna cewa ɗan ƙoƙarin fita daga inda ka fi jin daɗi (comfort zone) na iya taimaka maka wajen ƙara jan hankali da kuma kyautata dangantakarka da mutane.

2. Ka saurari mutane da nuna kana sha'awar abin da suke faɗa

....

Masu sha'awar Tom Cruise suna cewa yana da wata baiwa ta musamman ta sa mutum ya ji kamar magana da shi ne abin da yake mayar da hankali a kai a lokacin.

Haka nan, ɗan wasan barƙwanci kuma tsohon mai gabatar da shirin talabijin na dare, Stephen Colbert, ya taba yabawa Taylor Swift saboda yadda ta saurari ƴarsa mai shekara 14 da yadda ta nustu a lokacin da suke magana a karon farko da suka haɗu.

Wannan ya yi daidai da binciken ilimin halayyar ɗan Adam da ke nuna cewa mutane suna ganin mutum ya fi daɗin mu'amala idan yana nuna sha'awa a lokacin da ake tattaunawa, kuma yana yin tambayoyi kan abin da aka tattauna.

Saboda haka, wata hanya mai sauƙi ta ƙara jan hankalin jama'a, ita ce ka nuna sha'awa a zahiri wajen sanin mutane, sannan ka yi tambayoyi da ke nuna kana neman ƙarin bayani kan abun.

3. Ka zama mutum mai karamci

Sakamakon bincike daban-daban ya nuna cewa mutanen da suke aikata alheri kuma suna taimakon wasu ba tare da tsammanin wani sakamako a madadinsa ba, ana kallonsu a matsayin masu jan hankali.

Misali, bincike kan halayen da mutane ke nema a wajen abokin soyayya ya nuna cewa kirki da tausayi suna cikin halayen da aka fi so, kuma a wasu bincike an gano cewa su ne mafi muhimmancin halaye.

Har ila yau, wasu bincike sun nuna cewa mutane kan ga fuskar wani ta fi kyau idan an danganta mutumin da halin kirki da taimakon wasu.

Waɗannan sakamakon suna nuna cewa kasancewa mai kirki, taimakon wasu, da kuma la'akari da bukatunsu na iya ƙara maka karɓuwa da jan hankali a idanun mutane.

4. Kada ka zama mutum mai tsauri

....

Ba bakon abu ba ne a ji mutane suna cewa suna neman mutumin da ya iya soyayya, mai iya barkwanci da raha. Hatta tallace-tallacen neman masoyi sau da yawa suna nunawa ko koyar da mutane yadda za su dinga raha da masoyasansu,

Bincike ya goyi bayan wannan ra'ayi. A gwaje-gwajen soyayya cikin gaggawa da makamantansu, mutane masu barƙwanci da tausasan kalamai masu kayatarwa ana ganinsu a matsayin masu jan hankali.

Sai dai kuma, ƙoƙarin yin barkwanci fiye da ƙima na iya haifar da sakamako akasin abin da ake so.

Saboda haka, babban darasin da za a koya daga waɗannan bincike shi ne ka koyi ɗaukar abubuwa da sauƙi, ka ga abin dariya a cikin yanayi daban-daban, kuma kada ka riƙa ɗaukar kanka da muhimmanci fiye da kowa.

5. Ka kasance mai basira

...

Bincike ya nuna cewa mutane masu ƙirƙira da sabbin tunani sukan kasance masu jan hankali a idanun wasu. Ƙirƙira na iya bayyana ta hanyoyi da dama, kamar fasaha, rubutu, kiɗa, warware matsaloli ta sabuwar hanya, ko kuma kawo sabbin dabaru da tunani.

Mutane masu ƙirƙira galibi ana kallonsu a matsayin masu basira, masu sha'awa, kuma masu iya kawo sababbin abubuwa cikin rayuwa. Wannan na sa mutane su fi son mu'amala da su.

Ba sai ka zama fitaccen mai zane ko mawaki ba. Nuna ra'ayinka, koyon sabbin dabaru, ko neman hanyoyi na daban wajen magance matsaloli na iya nuna cewa kai mutum ne mai ƙirƙira.

...

Wata hujja da ka iya zama mafi gamsarwa ta fito daga wani bincike da ya nuna cewa surori iri ɗaya na rubutu sun fi jan hankali da kayatarwa idan an gabatar da su cikin salon labari mai ƙirƙira, musamman idan an bayyana cewa wani da ke da alaƙa da abin da ake magana a kai ne ya rubuta su.

Bisa ga waɗannan sakamakon, nuna ƙwarewarka ta ƙirƙira da fasaha wata hanya ce da za ta iya ƙara maka karɓuwa da jan hankali a idanun mutane. Misali, za ka iya:

Raba wa mutane waƙoƙi ko rubuce-rubucen da ka ƙirƙira.