Abin da tarin gajiya ke yi wa fata – kuma me za ka yi a kai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ellen Tsang
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
A tsawon lokaci, an bayyana cewa gajiya na shafar fata.
Sa dai a gomman shekarun baya-bayan nan, an gudanar da cikakke bincike don gano yadda hakan ke faruwa, tare da yin ƙarin haske kan abubuwa da ke shafar fata baki ɗaya.
Gajiya kan yi tasiri daban-daban, kama daga fitowar kuraje a fuska da kuma bushewar fata - hakan kuma na ƙara barazanar kamuwa da cutuka kamar su kyasfi da sauransu.
"Gajiya na shafar fata matuka," a cewar Dakta Alia Ahmed, wata ƙwararriyar likita a ɓangaren fata da ke birnin Landan.
Ta ce tana fara duba yanayin lafiyar marasa lafiya da take gani da kuma alamu da suke nunawa, har da tambayar yaya suke ji, suna cikin tsoro ko kuma fargaba, yaya yanayin barcinsu, abincin da suke ci da kuma motsa jiki.
"Likitocin kula da fata suna kasancewa kamar jami'an sirri," in ji ta, inda ta ce yanayin fata - zai iya nuna yadda lafiyar mutu take baki ɗaya.
Ta yaya gajiya ke shafar fata?
Ƙwakwalwa da kuma fata sun fito ne daga ƙwayoyi iri ɗaya a cikin mahaifa kuma suna da alaƙa.
Idan muka ji gajiya, ƙwaƙwalwa na yin martani don fitar da wasu sinadarai zuwa cikin jini.
Wannan zai saka mu san abin da ke faruwa da kuma taimaka mana wajen yin abubuwa.
Sai dai, sinadaran da ke fita na ƙarfafa wani ɓangare na jiki, amma yana rikita fata.
Suna kuma yi wa abin da ke bai wa fata kariya lahani - wato abin da ke kare fatar waje. Wannan na bai wa wasu ƙwayoyi masu lahani su shiga, abin da zai janyo bushewar fata,'' in ji Dakta Ahmed.
A lokaci guda, gajiya na saka wasu ƙananan ƙwayoyi da ke kashe cutuka a cikin fata su ragu - abin da ke janyo yiwuwar kamuwa da cutuka.
Akwai kuma hujjoji da ke cewa zai ƙara janyo fitar kuraje.
Dakta Ahmed ta yi nuni da cewa tarin gajiya kan shafi yanayin barci, wanda ta ce zai janyo tsaiko wajen gyara fata.
Gajiya na janyo kaikayi

Asalin hoton, Getty Images
Gajiya tana kuma janyo ƙwayoyin halitta da ke fata su fitar da wasu sinadarai da za su kaikayi.
"Idan ka ji kaikayi, za ka kaikayi jikinka, abin da ke ƙara janyo lahani ga fata," in ji Dr Ahmed. "Sannan ba za ka gane wa jikinka ba. Me ya sa ba zan daina kaikayi ba? Kana kara wa jikinka gajiya. Kuma wannan shi zai riƙa ƙara maka ƙaikayin.
Idan mutum ya kasance yana da matsalar fata hakan zai yi wani tasiri na daban, in ji ta, inda ta ba da misali da kaikayi irin na masu fama da kyasfa: "Kana kaikayi. Abin yana shafa ingancin rayuwarka. Ba ka jin daɗin abin saboda mutane na magana a kai sannan hakan na ƙara maka gajiya. Kuma wannan ne zai saka ka shiga wani hali.
Shin rage gajiya yana taimako?
"Gajiya za ta kasance mai lahani idan muka fara jin ba za mu iya magance ta ba," kamar yadda Rajita Sinha, wata farfesa a jami'ar Yale da ke Amurka.
A wannan lokaci, za mu riƙa jin alamu kamar ciwon kai ko kuma ciwon ciki, ko kuma fara manta abubuwa da kuma wahala wajen yin barci.
Ta bayar da shawarar cewa a nemi taimako da kuma yawaita motsa jiki.
Akwai hujjoji da suka bayyana cewa yawan motsa jiki na rage gajiya matuka yadda ya kamata.
Farfesa Sinha ta kuma ba da shawarar a riƙa fitarwa da shigar da numfashi saboda hakan na inganta lafiya ƙwakwalwa.

Asalin hoton, Getty Images
Shin ina fama da gajiya?
Dakta Ahmed ta shawarci mara lafiya cewa su yi abubuwa da dama don magance gajiya, domin gano abin da ya fi musu aiki.
Wannan ya kunshi motsa jiki wanda ake yi a kan gado kafin barci, shiga da fitar da numfashi yayin tattaki da sauransu ga waɗanda ke son tattara hankalinsu wuri guda.
Sai dai, ta ce samun hutu yana da wahala ba faɗa a baki kawai ba.
"Ina ganin mutane masu aiki tukuru a asibitin da nake aiki," in ji ta, ciki har da waɗanda aiki ya yi musu yawa a wuraren aiki - ko kuma gida, kamar kula da yara ko kuma iyaye tsofaffi.
Yayin da wasu suka ce suna zuwa motsa jiki ko kuma tattaki a kullu yaumin, ta ce da ta tambaye su ta gano cewa suna yin haka ne tare da tunanin abubuwan da suke son yi. "Ya kamata zuciyarka ma ta samu lokacin hutu a waɗannan lokuta," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Abin da fata yake bukata
Ba ya ga rage gajiya, fata na son kula yadda ya kamata - ciki har da mayunka da suka dace da kuma magungunan da ake buƙata, abinci mai kyau, barci da kuma ingantaccen salon rayuwa, a cewar Dakta Ahmed.
Ta ce akwai buƙatar a yawaita yin hakan na tsawon lokaci domin ganin ingantaccen fata - abin da zai sa mutum ya gane dalilin da ya sa fatarsa ke samun lahani.











