An sace mutane 1,100 cikin watanni uku a Najeriya - Amnesty

Yanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan ƙaruwar sace-sacen mutane a sassan Najeriya, inda ta ce an sace mutane aƙalla 1,100 a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun 2026, kuma mafi yawa a jihohin Arewa.

Amnesty International ta ce dole ne gwamnain shugaba Bola Tinubu ta gaggauta ɗaukar matakan magance wannan matsala da ke ƙara muni, musamman a tsakanin al'ummar karkara da mazauna sansanonin ƴan gudun hijira.

Malam Isa Sanusi, daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ya shaida wa BBC cewa bayan wani bincike da jami'anta suka gudanar ne ya gano yawan mutanen da aka sace, kuma sun fahinci cewa waɗanda aka yi garkuwa da su suna fuskantar nau'ikan cin zarafi sosai, ciki harda azabtarwa da horo da yunwa da fyaɗe da kuma tilasta masu aikata kisa.

Ya ce ''Mutane mafi yawa da aka sace a lokaci guda su ne a jihar Borno, a wani gari da ake cewa Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza, inda ƴan Boko Haram suka sace mutane fiye da 300. Sannan kuma akwai mutane kusan 200 da aka sace a Woro a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.''

Malam Isa Sanusi ya ƙara da cewa ''Akwai wanda kuma a jihar Zamfara aka sace mutum 150 a ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda aka ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa mata ne da yara.''

Daraktan ƙungiyar Amnesty a Najeriya ya ce wannan alƙalumman da aka tantance ne kuma aka tabbatar da su, amma ''akwai inda ake sace mutanen da ba a jin labari saboda suna faruwa ne a wurare masu nisa, da suke nesa da kafofin yaɗa labarai,''

Ya yi bayanin cewa Amnesty tana tsoron yadda abin ya ɗauki sabon salo ta yadda idan aka samu labarin sace mutanen ba a ganin abin a matsayin wata matsala saboda yadda yake neman zama ruwan dare.

''Ya kamata mutane su sani cewa duk wuraren nan da muke cewa ana sace mutane, kafin a sace mutanen sai an kashe mutane kuma, a ƙona shaguna, a ƙona runbin abinci, a sace wa mutane dukiya, a sace masu ƴaƴansu mata aje ana masu fyaɗe ana lalata su,'' in ji Isa Sanusi.

Amnesty International ta ce dole ne gwamnati ta tashi tsaye wajen zaƙulo sabbin dabarun yaƙi da ƙalubalen tsaro a Najeriya domin idan ba haka ba, tun tana cin ƙananan ƙauyuka da ƙananan garuruwa, ''to za ta iya shigowa cikin birni, kuma ta hana kowa sakewa.''

Yadda Boko Haram ta yi wa mutane 20 yankan rago a Borno

Boko Haram

Asalin hoton, Others

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dama ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta ce an yi wa mutane 20 yankan rago tare da sace wasu akalla 30 a yankin Mafa na jihar Borno.

Ƙungiyar ta ce waɗanda aka kashen a ranar Talata 31 ga watan Maris din 2026 ƴan gudun hijira ne maza da mata da ke zaune a cikin daji, kuma an kashe su ne a yayin da suka fita domin neman itacen girki.

Akwai kuma wasu aƙalla 30 da aka yi garkuwa da su, in ji Amnesty International.

Ta ce daga cikin mutanen da aka kashen akwai waɗanda aka yi wa yankan rago da kuma wasu da aka kashe da harbin bindiga.

Mutanen sun fuskanci barazanar Boko Haram a lokuta da dma, lamarin da ya sa suka yi gudun hijira.

Isa Sanusi shi ne shugaban kungiyar amnesty a Najeriya kuma ya ce dole ne hukumomi a Najeriya su zage dantse wajen kare fararen hula daga munanan hare-haren ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

Ya shaidawa BBC cewa ''Irin waɗannan abubuwan suna yawan faruwa, b a ma jin labarin su, kuma yawancin waɗanda abin nan ya ke shafa, ba a ma maganar su domin a cikin su harda yra ƙanana,''

''Wannan yana nuna yadda wannan matsala ta Boko Haram ta ke cigaba da zama matsala ga rayuwar mutane kuma da gazawar gwamnati wajen kare rayuwar al'umma.'' In ji Isa Sanusi.