Me ya sa ake caccakar shugaban INEC, Joash Amupitan?

Amupitan yana shan rantsuwa bayan amincewa da naɗinsa a matsayin sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya INEC

Asalin hoton, Presidency X

Bayanan hoto, Amupitan yana shan rantsuwa bayan amincewa da naɗinsa a matsayin sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya INEC
Lokacin karatu: Minti 6

Za a iya cewa wannan ne kusan karon farko da wani shugaban hukumar zaɓen Najeriya ke fuskantar ƙalubale daga shugabannin jam'iyyun da na addinai da kuma sauran al'umma.

Wannan suka da ake yi masatana ƙara dasa shakku a zukatan 'yan Najeriya dangane da irin adalci da hukumar za ta yi a babban zaɓen 2027.

Masana dai na cewa da zarar an samu irin wannan yanayi inda aka naɗa shugaban wata hukuma amma jim-kaɗan bayan naɗin sai aka samu 'yan ƙasa na sukar mutumin da aka naɗa bisa wasu dalilai da suke ganin za su iya kawo naƙasu a cancantarsa ko kuma gudanar da adalci ga aikin da aka ba shi, to ya kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki domin cirewa al'umma shakku.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfewa Joash Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC a watan Oktobar 2025, bayan ƙarewar wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya shugabanci hukumar na tsawon shekara 10.

BBC ta yi nazari dangane da ƙorafe-ƙorafen jam'iyyu da ƙungiyoyi a kan shugaba hukumar ta INEC da kuma shawarwarin masana kan yadda ya kamata a warware taƙaddamar.

Ƙorafin ADC kan Amupitan

Shugaban Jam'iyyar ADC David Mark da Mataimakinsa Rauf Aregbesola
Bayanan hoto, David Mark yayin taron da suka nemi shugaban INEC ya yi murabus daga muƙaminsa

Tun bayan da hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana cewar Sanata David Mark ba shi ne shugaban jam'iyyar ADC ba, ta kuma cire sunansa daga shafinta da sauran jagorarin da suke ƙarkashinsa bisa dogaro da hukuncin kotu, 'yan jam'iyyar ta ADC ɓangaren Sanata David Mark suke ta caccakar shugaban hukumar.

A wani taron da suka gudanar a ranar 2 ga watan Afrilu, 'yan jam'iyyar ta ADC ɓangaren Sanata David Mark sun yi kira ga shugaban hukumar INEC ya yi gaggawar sauka daga muƙaminsa ko kuma gwamnati ta cire shi.

Taron wanda David Mark da sauran jagorrin jam'iyyar suka jagoranta ya ce yana fargabar ADC da sauran jam'iyyun adawar ƙasar ba za su samu adalci ba a zaɓen da za a yi a 2027 matuƙar Farfesa Amupitan ne ke shugabantar INEC.

"Ba mu yarda da shi ba, ba zai yi mana adalci ba, tamkar ɗan aiken gwamnati muke kallonsa, muna kiran da ya gaggauta murabus, ko kuma gwamnati ta sauke shi da kanta," in ji Sanata David Mark.

Kiran PDP ga Amupitan

Tattaunawar da aka yi tsakanin ADC da PDP ɓangaren Tanimu Turaki

Asalin hoton, Nuruddeen Jos

Bayanan hoto, Atiku Abubakar da Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da kuma Davida Mark

Ita ma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba a bar ta a baya ba wajen nuna rashin amincewa da jagorancin Amupitan.

Jam'iyyar ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki wanda ya yi wani taron haɗin gwiwa da jam'iyyar ADC, ya nuna rashin shakkunsa bisa abin da ya kira rashin tabbas da kasancewa "dan amshin shata" ga jam'iyyar APC mai mulki da suka gani a tattare da Farfesa Amupitan.

Kabiru Turaki ya ce "muna tare da jam'iyyar ADC" a wannan gwagwarmaya ta neman adalci daga gwamnati ta hanyar "sauke Farfesa Amupitan daga shugabanci hukumar INEC" wadda ita ce za ta gudanar da zaɓe a 2027, saboda "imanin da muka yi cewa ɗan amshin shata ne".

Dole a cire Amupitan - MURIC

Amupitan

Asalin hoton, X

Bayanan hoto, Shugaban Hukumar zaɓen Najeriya INEC Farfesa Joash Amupitan

Cikin wata sanar da MURIC ta fitar a makon jiya ta nuna takaicinta ga matsayar Gwamnatin Tarayya na ƙin sauraren ƙungiyoyin musulmai na neman a sauke Farfesa Amupitan daga muƙaminsa.

MURIC ta ce yana daga cikin mutanen da suka "rubuta wasika ga Amurka" wadda ta kai ga ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da "ake kashe Kiristoci".

"Ya sayar da Najeriya a baya. Kuma zai sake sayar da ita a nan gaba. Duk wanda ya je yake gayyato 'yan mulkin mallaka zuwa lamarin da ya shafi cikin gidansa akwai buƙuatar a yi masa wani kallo na musamman. Muna kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna ga Shugaban INEC. Gwamnatin Tarayya sai su maya shi da wani Kiristan da zai iya haƙurin zama da abokan rayuwasa Musulmai da sauran mabiya addinai".

Kuma sun bayyana ko yunƙurinsa na sabunta katin zaɓe wani ƙokari ne "na hana Musulmai da dama samun damar kaɗa ƙuri'a" a zaɓen 2027.

Amoputan dan APC ne - Kperogi

Farfesa Farooq Kperogi ya yi ta bin diddigin tsofaffin sakonnin da Amupitan ya riƙa wallafawa domin bankaɗo gaskiya alaƙarsa da APC da kuma shugaba Tinubu

Asalin hoton, Kperogi Facebook

Bayanan hoto, Farfesa Farooq Kperogi ya yi ta bin diddigin tsofaffin sakonnin da Amupitan ya riƙa wallafawa domin bankaɗo gaskiya alaƙarsa da APC da kuma shugaba Tinubu

A ranar JUma'a 11 ga watan Afrilu fitaccen marubucin nan mai tarin mabiya a kafafen sada zumunta mai yawan janyo ce-ce-ku-ce Farfesa Farooq Kperogi ya wallafa wani abu da 'yan Najeriya suka kalla a matsain tonan asiri ga shugaban na INEC Farfesa Amupitan.

A shafinsa na X Farfesa Kperogi ya wallafa cewa bayan bin diddigi na shakara da shekaru na wallafe-wallafen da Amupitan ya yi a shafinsa na X ya gano cewa mutumin da aka nada ya jagoranci INEC "dan jam'iyyar APC ne" kuma mai goyon bayan shugaba Tinubu.

Kperogi ya yi ta bin ƙwaƙƙwafin bayanan da shugaban na INEC ya riƙa wallafawa masu alaƙa da shugaban Najeriya Tinubu.

BBC ba ya iya tabbatar da ingancin bayanin ba, amma masu shafukan sada zumunta na ta wallafa shi a matsayin wanda Amupitan ya wallafa a baya.

Asalin hoton, X

Bayanan hoto, BBC ba ta iya tabbatar da ingancin bayanin ba, amma masu shafukan sada zumunta na ta wallafa shi a matsayin wanda Amupitan ya wallafa a baya.

BBC ba ya iya tabbatar da ingancin bayanin ba, amma masu shafukan sada zumunta na ta wallafa shi a matsayin wanda Amupitan ya wallafa a baya.

"Saƙonni da dama na baya da shugaban INEC Farfesa Joash Ojo Amupitan ya wallafa da muka tabbatar lokacin yana matsayinsa na Farfesa a jami'ar Jos ba tare da wani kuskure ba ya bayyana goyon bayansa da muradinsa ga APC kuma musamman ga shugaba Tinubu. In yana jin yana da wani girma da ya shafi jami'a to ya riƙe abinsa, amma ya kamata ya san girman nauyin ofishin da yake riƙe da shi ya ajiye muƙaminsa. Zan dawo kan wannan batu." in ji Kperogi.

An riƙa yaɗa wasu bayanai da ke nuna matsayar Farfesa Amupitan game da zaɓen Tinubu da APC a 2023, sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin hotunan ba.

Shugaban INEC ba shi da shafi a X

INEC ta yi kira ga 'yan Najeriya su yi watsi da ƙagaggun labaran ƙarya da ake yaɗawa game da shugaban hukumar Farfesa Amupitan.

Hukumar ta ce zargin baki ɗayansa "ƙarya ne" tsararren abu ne. "Domin kawar da shakku a zukatan mutane, shuganam INEC ba shi da wani shafi a X.

"Babu wani lokacin da ya taɓa fitowa ya yi sharhi kan siyasar jam'iyyun," in ji Sanarwar.

Baya ga nan INEC ta ce tana sani da laifin intanet da mutane suke aikatawa, suna amfani da hoton Amupitan suna samar da wani shafi domin ɓata masa suna, INEC ta ce tuni ta miƙa wannan ƙorafi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki.

Mece ce mafita

Farfesa Kari

Asalin hoton, Kari Linkdin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana irim su Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja, ya ce an riga an yi tabo ga hukumar zaɓe da kuma shugabanta, "shi alƙali ne wanda ake da kwarin gwiwar da ake sa ran adalci daga gare shi" dan haka wannan lamari ne mai sarƙaƙiya.

Yadda ya zama mai sarƙaƙiya in ji Farfesan saboda da shigowar ɓangaren malaman addini, amma da shiyasa ce kawai da babu wani abun sarƙaƙiya domin an saba da haka a siyasa.

Gwamnati na da zaɓi da dama kan wannan batu, "ko gwamnati ta sallame shi ta yada kwallon mangwaro ta huta da ƙuda, ko kuma shi ya ajiye aikin ya huta da zarge-zarge," in ji Kari.

Yace abubuwan da suke ƙara rura wutar wannan rikici shi ne "shirun da Amupitan ya yi kan zarge-zargen da ake masa.

"MURIC sun zarge shi da rubuta maƙalar da Amurka ke amfani da ita kan Najeriya. Tsohon Ministan wasannin Salamon Dalong ya zarge shi da rashin adalci lokacin da suka yi aiki tare. Sai zargi na ƙarshe da aka masa na goyon bayan Shugaban ƙasar da jam'iyyarsa mai mulki, babu wanda ya fito ya musanta, musantawar da za ta gamsar da kowa," in ji Farfesa Kari.

Shawarar da Farfesan ya ba da ga shugaba Tinubu ita ce matuƙar yana son a yarda da zaɓen da za a gudanar to ya ɗauki mataki tun yanzu saboda "in ba a bi a hankali ba kan ta tafasa za ta ƙone, kan a yi zaɓe 'yan adawa za su yi fatali da sakamakon zaɓen".