'Na san an samu kuskure': Iyalan da suka haihu da maniyyin da ba nasu ba

Hoton ɗan Laura, James.

Asalin hoton, Keith Bridle / BBC

Bayanan hoto, Laura da abokiyar zamanta sun ce an yi amfani dashen ɗantayin da ba nasu ba wajen haifar ɗansu James
    • Marubuci, Anna Collinson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, File on 4 Investigates
    • Marubuci, Jo Adnitt
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Investigations
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Jim kaɗan bayan haihuwar James ne na gano akwai matsala," a cewar Laura.

Ita da abokiyar zamanta, Berth suna da ƴaƴa biyu - James da Kate, wadda ita ce babba - dukansu an haife su ne ta hanyar dashen ɗantayi a wani asibiti da ke arewacin Cyprus.

Matan biyu sun yi amfani da ƙwayayen su kuma a hankali suka zaɓi mai ba da gudummawar maniyyi wanda yake da lafiya. Sun faɗa wa asibitin da ya sayi maniyyin cewa yana da kyau a yi amfani da manyiyyi ɗaya wajen duka yaran - saboda yaransu su yi alaƙa da juna.

Sai dai lokacin da aka haifi James, sun gano cewa "idanunsa masu kyau" daban suke da asalin mahaifiyarsa, Berth, da kuma wanda ya aka sayi maniyyin a wajensa. Lamarin ya saka shakku a cikin zukatan matan. "Shin asibitinmu ya yi kuskure ne?"

Bayan damuwa na kusan shekara goma, Beth da Laura sun yanke shawarar yi wa ƴayansu gwajin ƙwayar halitta na DNA. Sakamakon ya nuna cewa duka yaran ba sa alaƙa da maniyyin da mahaifansu suka saya. Abin da ya ƙara tabbatar da cewa yaran ba sa ma alaƙa da juna.

"Ba mu ji daɗi ba ko kaɗan kan lamarin, kuma me hakan zai yi ga makomar ƴaƴan?" in ji Beth.

James da Kate.

Asalin hoton, Family supplied

Bayanan hoto, Hoton James da Kate wanda aka ɗauka shekaru da dama da suka wuce - dukansu an haife su ta hanyar dashen ɗantayi

BBC ta tattauna da iyalai bakwai waɗanda suka yi imanin cewa an yi amfani da maniyyin da bai dace ba yayin dashen ɗantayin. Iyalai da dama sun yi gwajin kwayar halitta don gano asalin ƴaƴansu.

Duka lamuran suna alaƙa da asibitoci da ke arewacin Cyprus - wani yankin da dokokin Tarayyar Turai ba sa aiki, wanda Turkiyya kaɗai ta amince da shi.

Arewacin Cyprus ya zama wurin da ƴan Birtaniya ke zuwa don neman haihuwa, in ji masana. Ba a cika kula da asibitoci ba sannan suna yin aiki cikin rahusa kuma ana samun nasarar aiki yadda ya kamata.

Suna da masu ba da ƙwayaye da kuma maniyyi da yawa a faɗin duniya, abin da ya sa masu neman haihuwa ke yawan zuwa can, musamman ƴan ƙungiyar LGBT ko kuma waɗanda ba su yi aure ba, waɗanda kuma ba za su iya samun irin damar a ƙasashensu ba.

Akwai bidiyoyi da kuma hotuna da dama a kafafen sada zumunta na waɗanda suka samu nasara a can.

Arewacin Cyprus ɗin yana gudanar da harkoki waɗanda suke haramtattu a Birtaniya.

'Mun ɗauka mun sayi maniyyi daga Denmark'

Mun ɗauki tsawon watanni kafin iyalai su amince su yi magana a wannan bincike. Mun aiki kut da kut da Beth, Laura, Kate da kuma James don tabbatar da cewa sun shirya bayar da labarinsu.

Beth da Laura sun faɗa mana cewa sun yanke shawarar fara iyali a 2011.

Sun zaɓin cibiyar dashen ɗantayi a arewacin Cyprus. Mai kula da aikin a asibitin a lokacin, Julie Hodson ta faɗa musu cewa za su iya sayan maniyyin da ya daskare daga babbar cibiyar sayar da maniyyi mafi girma a duniya, Cyros International da ke Denmark.

Ma'auratan sun ji daɗin, in ji su, ba. yan ganin gwajin da aka yi wa masu ba da maniyyi

Ra'ayin su ya kama na wani mutum mai suna "Finn" - ɗan asalin Denmark wanda ya kwatanta kansa da mai lafiya wanda ba ya shan giya ko kuma sigari.

Beth da Laura
Bayanan hoto, Beth (hagu) da Laura (dama) sun yi fatan cewa maniyyin ɗan Denmark "Finn" zai kawo wa ƴaƴansu farin ciki

A wani rubutu da suka ga Finn ya yi, ya ce burinsa shi ne bayar da maniyyi don samar da "rayuwa da farin ciki ga wasu".

Beth da Laura sun yi fatan cewa hakan zai samarwa ƴaƴansu fari ciki da nutsuwa yayin girma. "Mun ji cewa yana da kyau a ce mun haifi ƴaƴanmu ta hanyar maniyyi iri ɗaya," in ji Beth.

Finn da ƴan uwansa a Denmark suna kama da irin ma'auratan ƴan Birtaniya.

"Mun tambayi Julie mai kula da aikin dashen ɗantayin, abin da muke so mu yi da maniyyin Finn," in ji Laura. "Sai ta ce: "Dr Firdevs za ta kawo muku shi.' Shi ke nan."

Ma'auratan sun ce Dakta Firdevs Uguz Tip ce ta jagoranci aikin - sun kwatanta ta da tawagarta a matsayin mutanen kirki.

Watanni tara bayan nan, Laura ta haifi ƴarsu ta fari, Kate.

An email exchange about selecting a sperm donor. Key details: Sender: Dogus IVF Centre (Julie Hodson, International Patients Coordinator)
Date: Thursday, 28 April 2011
Recipients: Beth (and partner Laura)
Main points: Beth and Laura reviewed Cryos sperm donors and chose a donor named “Finn.”
They asked if there was anything else they needed to do.
The clinic replied that no further action was needed, apart from following the medication protocol.
Dr. Firdevs would arrange for the sperm to be couriered to the hospital before their arrival in Cyprus.
Quoted highlights from the email: “We have chosen ‘FINN’ if that’s ok?”
“Dr. Firdevs will arrange for the sperm to be couriered to the hospital.”
Bayanan hoto, To request:Complete the translations here: https://tinyurl.com/yc2wt4thFill-in the commissioning form https://bit.ly/ws_design_form with this title in English: Cyprus IVF clinic - ragouts - 2026033104
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lokacin da suka yi niyyar samun yaro na biyu, sun koma ga tawagar da ta yi musu dashen ɗantayin na farko inda suka tambaya cewa ko za su iya sake amfani da maniyyin Finn. Hodson ta tabbatar da cewa Firdevs za ta sayi maniyyin ta kawo.

A lokacin ne Beth ta haifi James.

Aikin da aka yi wa ma'auratan a arewacin Cyprus, ciki har da kuɗin magunguna, otel da kuma na jirgi, sun kai aƙalla fam 16,000 - inda maniyyin Finn ya kai fam 2,000.

Beth da Laura sun ce tun suna ƙanana sun faɗa ƴaƴansu mutumin da aka yi amfani da maniyyinsa. "Dukansu suna kwatanta cewa rabinsu su ƴan Denmark ne," in ji Laura.

Sai dai idon James da suka kasance duhu-duhu, bakin gashi da kuma fata mai tsansi, sun janyo zargi a zukatan iyayensa cewa wannan ba maniyyin Finn bane - bayan tsawon shekaru na shakku, Beth da Laura sun yanke shawarar gwajin kwayar halitta ta DNA.

Sakamakon gwajin ya nuna babu wanda suka haifa da maniyyin Finn a cikin yaransu. An haife su da maniyyi daban-daban, kuma ba su alaƙa da juna.

Sakamakon gwajin ya sare gwiwar ma'auratan kuma suna cike da tarin tambayoyi. Su wanene suka ba da maniyyin, shin an yi gwaje-gwajen lafiyarsu?

"Mun tashi daga jin daɗin cewa maniyyin Finn aka yi amfani da shi wajen haihuwar ƴayanmu zuwa rashin tabbas," a cewar Beth.

Beth da Laura sun yi kokarin tuntuɓar Firdevs da Hodson, sai dai babu wani martani da suka samu.

Kate na kallon James lokacin da aka haife shi.
Bayanan hoto, Gwajin kwayar halitta ya nuna cewa an yi amfani da maniyyi daban-daban wajen haihuwar Kate da James

BBC ta shafe tsawon watanni tana kokarin bincike kan batun Beth da Laura.

Lokacin bincikenmu, mun gano wasu iyalai ƴan Birtaniya biyu da Dakta Firdevs ta yi wa aiki, su ma suna zargin an yi amfani da maniyyin da ba nasu ba yayin aiki.

Su ma sun yi gwajin kwayoyin halitta inda zargin da suke yi ya tabbata.

Beth da Laura sun yi zargin cewa da wuya ma in asibitin ya sayi maniyyi daga wajen Finn.

Lokacin da muka tuntuɓi Dakta Firdevs ta ce ba ita ce ke da alhakin sayan maniyyi ba a asibitin, kuma wani bayani kan maniyyin Finn da aka kawo mata.

Ta kuma nuna shakku kan gwajin kwayoyin halitta na Beth da Laura. Ba za a iya cewa an yi amfani da maniyyin da bai dace ba, in ji ta.

Firdevs ta faɗa wa BBC cewa "ba ta yi aikin dashen ɗantayi ba" daga 2011 zuwa 2014, lokacin da Beth da Laura suka je, duk da cewa bayanai a shafin inatanet na asibitin Dorgu ya nuna cewa akwai taimako da ta bayar lokacin aikin.

Asibitin Dorgu wanda Firdevs ta ce shi ke da alhakin kula da aikin Beth da Laura, bai ce uffan ba lokacin da muka nemi ji daga gare sa.

A 2015, Firdevs da Hodson suka bar asibitin Dorgu inda suka koma aiki a wani asibiti a arewacin Cyprus.

Hodson, wadda ta daina aiki a yankin, ba ta mayar da martani ga buƙatar ji daga gare ta da BBC ta yi.

Beth, da Laura da kuma ƴaƴansu sun kara yin gwaje-gwaje a yanzu, waɗanda za a yi amfani da su a kotunan Birtaniya. Gwajin ya nuna cewa Kate da James ba su da alaƙa ta jini kuma ba a haife su da maniyyi iri ɗaya ba.

Wasu ma'aikata.
Bayanan hoto, Firdevs (hagu) da Julie Hodson (dama) sun ci gaba da aiki tare bayan barin asibitin Dogus