An gaza ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran

JD Vance

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Amurka da Iran sun bayar da dalilai masu cin karo da juna, a matsayin abin da ya sa aka gaza cimma matsaya a zaman tataunawar zaman lafiya da ƙasashen biyu suka yi a Pakistan.

Kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran ta ruwaito cewa an gaza cimma yarjejeniyar zaman lafiya a taron na birnin Islamabad ne saboda wasu "buƙatu marasa amfani" da Amurka ta gabatar.

"Duk da ƙoƙarin da wakilan Iran suka yi domin ganin komai ya tafi yadda ya dace, wasu ''buƙatu marasa amfani'' daga ɓangaren Amurka sun sa an gaza ƙulla yarjejeniya. Da haka zaman tattaunawar ya tashi,'' in ji kafar yaɗa labarai ta IRIB a wni saƙo da ta wallafa a Telegram.

Amma Amurka ta ce buƙatun nata "sauƙi" ne kuma "waɗanda suka dace".

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya ce shugaba Trump ya tura shi wakilci Pakistan tare da ba shi umarnin ''dagewa domin ganin an cimma matsayar zaman lafiya.''

Ya ce ''Mun yi duk abin a ya dace, amma mun gaza cimma wata matsaya saboda wata buƙata mai sauƙi da muka gabatar. Wadda ita ce muke ganin ta fi dacewa da kowa''

Babu dai tabbacin ko za a ƙara wani yunƙuri a cikin makonni biyun tsagaita wuta da aka ƙula, ko kuma akwai shirin gudanar da wani zaman na daban.

A jawabin da ya gabatar bayan kammala zaman, Mr Vance ya ce Amurka ta fayyace sharuɗɗanta, kuma ta sanar ƙarara cewa babu gudu ba ja da baya a kan su, ''amma Iran ba ta amince da buƙatun namu ba''.

Ya ce ''mun shafe sa'oi muna tattaunawa, amma ina baƙin cikin sanar da ku cewa ba mu cimma matsaya ba''.

Tuni dai tawagar Amurkan da ta hada da mataimakin shugaban ƙasar JD Vance da mai bai wa fadar White House shawara, Jared Kushner da kuma manzo na musamman ga shugaba Trump a gabas ta tsakiya, Steve Witkoff, da sauran jami'ai suka bar Pakistan domin komawa Amurka.