Lokuta bakwai da manyan ƙungiyoyin Premier suka yi 'dakon teburi'

A graphic depicting Steven Gerrard, Mikel Arteta and Kevin Keegan

Asalin hoton, BBC Sport

    • Marubuci, Alex Bysouth
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Senior Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Masu dakon tebur!"

Wannan ne kalaman da wasu ƙungiyoyin ke amfani da su wajen tsokanar magoya bayan ƙungiyar da ta daɗe a kan teburi amma ta kasa lashe kofi.

A taƙaice yanayi ne da ƙungiyar da ta nuna kamar za ta lashe kofin amma ya kuɓuce mata.

Yanzu haka Arsenal na ƙoƙarin yakice wannan tambari da aka yi mata bayan shaharar da ta yi wajen "dakon tabur" a cikin kusan shekaru 20 a baya-bayan nan.

To amma ba Arsenal ce kawai ta taɓa shiga irin wannan hali, hasali ma akwai wasu ƙungiyoyin da nasu "dakon teburin" ya fi na Arsenal ciwo.

BBC ta duba wasu lokuta da ƙungiyoyin Premier suka yi dakon teburi amma daga ƙarshe suka sha takaici bayan abokan hamayyarsu sun musu shigar sauri daga ƙarshe.

7. Liverpool: 2018-19

A ƙoƙarinta na lashe kofin Premier karon farko, Liverpool ta kama hanya tiryan-tiryan wajen tabbatar da hakan a kakar 2018-2019, inda ta tattara maki 97, wanda a lokacin ita ce ƙungiya da ta tara maki mafi yawa a tarihin gasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matsala ɗaya ce ta samu, wato Manchester City ta fi ta da maki ɗaya.

Liverpool a lokacin, ƙarƙashin Jurgen Klopp ta samu nasara a wasa 30 kuma ta kasance a kan teburin Premier na tsawon kwana 141 - yayin da a cikin watan Disamba na kakar Manchester City tana ƙasanta da maki 10.

Amma wasan da Liverpool ta sha kashi da ya fi shahara a lokacin shi ne wanda ta ziyarci City - inda ɗan wasan baya na City, John Stones ya hana ƙwallo shiga raga a kan layi - kuma wannan wasa shi ne ya yanke hukunci kan ƙungiyar da za ta lashe kofin.

Duk wani yunƙuri da Liverpool ta yi na ganin ta riƙe wuta, abin ya ci tura, har ya kai ga City ta lashe kofin.

6. Arsenal: 2002-03

Arsene Wenger ya yi fatan shafe kakar wasan ba tare da an doke shi ba, bayan lashe kofuna biyu a shekarar 2002, inda a lokacin ake tunanin Arsenal za ta zama 'giwar Ingila' bayan ƙwace kofi daga hannun Manchseter United.

A wannan lokaci Arsenal ƙarƙashin Wenger, wanda ake wa laƙabi da 'Farfesa', ta kwashe kusan wata biyar a kan teburi.

Sai dai ba da daɗewa ba United ta yi nasara a kan Liverpool ta kuma sake yin nasara a kan Newcastle United, yayin da Arsenal ta yi canjaras da Aston Villa a filin wasa na Highbury a tsakiyar Afrilu.

Aka yi wasa tsakanin ƙungiyoyin biyu, inda Theirry Henry ya zura ƙwallo biyu bayan Ruud van Nistelrooy ya ci da farko, sai dai Ryan Giggs ya ƙara jefa ɗaya, aka tashi 2-2.

Tun daga lokacin United ta ci gaba da ƙoƙari a wasanninta, yayin da ita kuma Arsenal ta yi tuntuɓe a wasanninta da Bolton da kuma Leeds.

Ruud van Nistelrooy, in all-blue Manchester United kit, scores as Arsenal's Martin Keown, in red and white, watches on with a pained expression

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Arsenal and United played out a classic at Higbury in 2003, but a draw was not enough for the Gunners

5. Arsenal: 2007-08

A shekarar 2008, bayan komawa wasa a filin Emirates, Arsenal wadda ta nuna kamar za ta taka rawa, ya zuwa watan Maris ta yi rashin nasara ne sau ɗaya kacal, kuma ta shafe kwana 156 a kan teburi, amma ya zuwa watan Maris Arsenal ta koma ta uku, a ƙasan Manchester United da Chelsea.

Daga nan ne Arsenal ta shiga cikin halin ha'ula'i a Premier bayan ɗan wasa Eduardo ya karya ƙafarsa a karawa da Birmingham, inda Arsenal ta yi wasa 5 ba tare da yin nasara ba.

Ba a Premier kawai ba, Arsenal ta sha kashi ta ko ina, inda Tottenham ta lallasa ta a matakin kusa da ƙarshe na gasar League Cup, United ta taka mata burki a kofin FA sannan Liverpool ta yi waje da ita a gasar zakarun Turai.

Tun daga wannan lokaci Arsene Wenger bai ƙara lashe Premier ba, inda ƙungiyar ta kwashe kakar wasa 9 ba tare da cin kofi ba, lamarin da ya sanya Mourinho ya bayyana Wenger a matsayin "ƙwararre kan rashin nasara".

Arsenal ba ta sake cin komai ba har sai wuraren ƙarshe-ƙarshen jagorancin Wenger inda ta lashe kofin FA.

4. Arsenal: 2022-23

Idan muka matso nan kusa-kusa a kakar 2022-23 Arsenal na kafa tarihi. Abin takaici ƙungiyar ta zamo wadda ta fi shafe kwanaki a kan teburi ba tare da lashe kofin ba, kwana 248.

A cikin mako 30, Arsenal ta sauka daga saman teburi ne na kwana 3 kacal, bayan da Manchester City ta yi nasara a wani kwantan wasanta a watan Fabarairu.

Daga baya Arsenal ta sake komawa saman teburi kuma ta ci gaba da zama a sama har zuwa lokacin da ta je baƙunci a gidan Manchester City a ranar 26 ga watan Afrilu, inda ƴan wasan na Guardiola suka lallasa Arsenal da ci 4-1.

Southampton celebrate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fatan Arsenal na lashe kofin Premier a 2023 ya zo ƙarshe ne wasan da ta yi canjaras 3-3 a gida da ƙungiyar Southampton

3. Manchester United: 1997-98

A shekarar 1998, Arsenal ce ke sheƙe-aya. Inda Wenger ke sauya yadda abubuwa a ƙungiyar.

Arsenal ta samu nasarar cike giɓin maki mai yawa har ta zo ta lashe kofin Premier sannan kuma ta lashe FA.

Da farko Manchester United ce a gaba, har ma wasu suna da tabbacin tamkar ta riga ta lashe kofin. Blackburn ce ke biye wa United ya zuwa lokacin da aka kai rabin kakar, Arsenal tana a matsayi na 6.

A wani lokaci a kakar, Arsenal na ƙasan United da maki 13.

Daga United ta shiga mummunan hali, inda ta samu maki ɗaya tal a karawarta da Southampton da Bolton da kuma Leicester, sannan ta yi rashin nasara a hannun Sheffield Wednesday, ta yi canjaras da West Ham kafin ta yi wata muhimmiyar karawa da Arsenal a watan Maris.

Marc Overmars ya ci ƙwallo gab da tashi wasa yayin da Arsenal ta yi nasara a wasa 10 a jere.

Daga nan United ta koma matsayi na biyu a kan tebur bayan yin canjaras da Liverpool da Newcastle a watan Afrilu, inda suka ƙare kakar a mataki na biyu, bayan gazawa da maki ɗaya.

Steven Gerrard a wasan Liverpool da Chelsea ranar 27 ga watan Afrilun 2014

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Steven Gerrard a wasan Liverpool da Chelsea ranar 27 ga watan Afrilun 2014

2. Liverpool: 2013-14

Zamewar da za a daɗe ba a manta da ita ba - lokacin da ɗan wasan tsakiya na Liverpool, Steven Gerrard ya zame, kuma na take ɗan wasa Demba Ba ya ɗauke ƙwallon sannan ya jefa ta a raga, lamarin da ya bai wa Chelsea nasara da ci 2-0 a filin wasa na Anfield.

Damar da Liverpool ta samu ta kuɓuce.

A karawar kusa da ta ƙarshen kaka a Premier, Liverpool ta zura ƙwallo uku da farko, amma daga baya Crystal Palace ta farke, inda a ƙarshe aka tashi canjaras.

A kakar da ta biyo ne Gerrard ya bar Anfield ba tare da lashe Premier ba, duk da dai daga baya Liverpool ta lashe kofin a 2020.

1. Manchester United: 2011-12

Ɗaya daga cikin hotunan gasar Premier mafi shahara shi ne na ɗan wasan City, Sergio Aguero na wulwula rigarsa bayan zura ƙwallo a minti na 94, ƙwallon da ta ƙwace kofin Premier daga hannun abokan hamayyarsu Manchseter United.

United ta yi nata ƙoƙarin a wannan rana cikin watan Mayun 2012, inda ta yi nasara kan Sunderland.

To amma matsalar ita ce ta ɓarar da damarta ne tun kafin wannan lokacin bayan da ƙungiyar ƙarsƙashin Alex Ferguson ta zubar da maki takwas yayin da ya rage saura wasa shida a kammala kakar.