KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. NATO ta ce ba za ta shiga shirin rufe mashigar Hormuz ba

    Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar tsaro ta NATO sun sanar cewa ba za su shiga shirin Donald Trump na rufe mashigar Hormuz ba. Maimakon haka, sun ce za su iya shiga tsakani ne kawai bayan rikicin ya ƙare.

    Wannan mataki na iya jawo rashin jin daɗin shugaba Amurka, Donald Trump.

    Faransa ta riga ta bayyana shirin kafa rundunar haɗin gwiwa mai “manufar zaman lafiya” tare da Birtaniya, domin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin ‘yanci a mashigin Hormuz.

    A cewar sanarwar sojojin Amurka, an fara toshe zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran a hukumance ‘yan mintuna da suka wuce.

    An ce wannan aiki yana gudana ne bisa umarnin Donald Trump, kuma manufarsa ita ce hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin jiragen Iran a yankin Tekun Fasha da Tekun Oman.

  2. Ana ci gaba da nemo hanyoyin warware rikicin Gabas ta Tsakiya - Shehbaz Sharif

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya ce yunƙurin warware rikicin Amurka da Iran na ci gaba.

    Wannan na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin ƙasashen guda biyu da aka gudanar a babban birnin Pakistan, Islamad a ƙarshen mako, ba ta cimma komai ba.

    "Tsagaita wutar na ci gaba a daida lokacin da nake maganar nan, ana kuma yunƙurin samar da mafiya dangane da sauran batutuwan da ake taƙaddama a kansu, kamar yadda Sheriff ya shaida wa majalisarsa.

  3. An ƙone gawar mawaƙiyar India, Asha Bhos-le

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Asha Bhos-le ta yi waƙoƙi fiye da 12,000 a rayuwarta.

    Fitattun mutane daga masana’antar shirya fina-finai da kiɗe-kiɗe da wasanni na ƙasar India sun hallara a birnin Mumbai domin yi wa fitacciyar mawaƙiya Asha Bhos-le bankwana, wadda ta rasu tana da shekaru 92.

    Taurari da suka haɗa da tsohon kyaftin ɗin wasan kwallon cricket, Sa-chin Ten-dul-kar sun taru a gidanta kafin a kai ga Kone gawarta, cikin wani salo na girmamawa a filin wasa na Shivaji Park inda za'a yi mata jana'izar ban girma.

    Dubban mutane ne suka fito kan tituna yayin da ake wucewa da gawar. Asha Bhos-le ta shafe shekaru tana jan zaren ta wajen rera waƙoƙin da ‘yan Bollywood ke amfani da su.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dandazon masu alhini yayin da suke sanya gawar mamaciyar a mota domin kai ta wurin da aka ƙonata.
  4. Rundunar sojin Amurka ta ce nan ba da jimawa ba za ta rufe Hormuz

    Rundunar sojin Amurka ta aika da sanarwa ga masu harkokin jiragen ruwa, inda ta ce za ta fara ƙaddamar da takunkumi kan hana jiragen da ke ta'ammali da Iran a ruwa a tekun Oman da na gabashin yankin Larabawa a mashigar Hormuz.

    Rundunar ta ce hare-haren zai shafi dukkanin jiragen ruwa ba tare da la’akari da tutar ƙasar da suke ɗauke da ita ba.

    Rundunar sojin ta Amurka ta ce duk wani jirgin ruwa da ya shiga ko ya fita daga yankin da aka ƙaƙaba wa takunkumi ba tare da izini ba, zai fuskanci tarewa ko karkatarwa ko kuma a kama shi.

    Sanarwar ta kuma ce takunkumin zai shafi dukkan gaɓar tekun Iran, ciki har da tashoshin jiragen ruwa da wuraren fitar da mai, ba tare da iyakancewa ga wasu wurare kaɗai ba.

    Iran ta yi barazanar ɗaukar matakin ramuwar gayya kan shirin takunkumin, wanda ake sa ran zai fara aiki nan ba da jimawa ba.

  5. Hezbollah ta kai hare-hare kan Isra'ila

    Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta kai hare-hare kan sojojin Isra'ila a Shlomi da ke Isra'ila ta hanyar yin amfani da jirage marasa matuƙa.

    To sai dai kuma dakarun Isra'ila sun bayar da bayanai inda suke cewa dakarun na ci gaba da faɗaɗa farmakinsu a kudancin Lebanon

    IDF ta ce wani farmaki a yankin Bint Jbeili ya kashe ƴan ƙungiyar Hezbollah 100 sannan sun samu ɗaruruwan makamai.

  6. Ba ni da niyyar yin sa-in-sa da Donald Trump - Fafaroma Leo

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Fafaroma Leo ya ce ba shi da niyyar yin faɗa-in-faɗa da Donald Trump bayan da shugaban na Amurka ya caccake dangane da kalamansa a kan yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

    "Ni ba ɗan siyasa ba ne," in ji Fafaroma Leo, a lokacin da yake kare kalaman nasa da ya yi "saƙon irin ɗaya ne: samar da zaman lafiya."

    Fafaroma dai ya nemi ƙasashen duniya da su kawo ƙarshen abin da ya kira "mahaukacin yaƙi". Ya kuma yi watsi da amfani da sunan addinin Kiristanci wajen halasta yaƙi."

    A martanin da ya yi, Donald Trump ya bayyana Fafaroma da "wanda bai san komai ba kan laifuka da kuma tsare-tsaren ƙasashen duniya".

  7. Dan ƙwallon Ghana, Dominick Frimpong ya rasu

    Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Berekum Chelsea, Dominick Frimpong ya rasu sakamakon harin ƴan fashi a kan motar bas da ke ɗauke da su bayan kammala wani wasan gasar Premier a Ghana da ƙungiyar FC Samartex

    Ɗan wasan mai shekara 20 ya samu rauni daga harbin bindiga sakamakon buɗe wa tawagar tasu wuta.

    Frimpong dai ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aduana FC da yake taka leda a kungiyar Berekum Chelsea a matsayin aro.

    Ya buga wasanni 13 a gasar League sannan ya ci ƙwallaye biyu a wannan kakar.

  8. Netanyahu ya ce Isra'ila na goyon bayan Amurka kan Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiminista Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila tana goyon bayan Asojojin ruwan Amurka na yunƙurin rufe mashigar Hormuz.

    A wani bidiyo da yake jawabi ga majalisar ministocinsa, Netanyahu ya ce " shugaba Trump ya yanke kuɗirin toshe mashigar Hormuz, mu ma muna goyon bayan wannan matsaya."

    Ya kuma ƙara da cewa ya yi magana da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ranar Lahadi bayan tattaunawa da Iran inda ya ba shi cikakken bayani na abin da ya faru a Pakistan.

    Firaiministan na Isra'ila ya ƙara da cewa duk wani abu da ke nuna rashin jituwa tsakanin Amurka da Isra'ila "to ba gaskiya ba ne."

  9. Faransa da Birtaniya za su yi taro kan mashigar Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce Faransa da Birtaniya za su shirya wani taro "da manufar dawo da ƴancin shigi da fici a mashigar Hormuz" a ƴan kwanaki masu zuwa.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya, Macron ya ce za a shirya taron ne inda za a gayyaci ƙasashen da suke a shirye su bayar da gudunmawarsu wajen "samar da wani shiri na haɗin gwiwa domin wanzar da zaman lafiya da dawo da ƴancin zirga-zirga a mashigar Hormuz."

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta gaza cimma matsaya a ƙasar Pakistan, inda kuma Donald Trump ya yi barazanar kai wa jiragen ruwa da suka biya ko za su biya Iran kuɗin wucewa ta mashigar ta Hormuz.

  10. Donald Trump ya caccaki Fafaroma Leo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki shugaban ɗariƙar katolita na duniya Fafaroma Leo, inda ya zarge shi da rauni wajen yaƙi da laifuka da kuma rashin ƙwarewa a harkokin ƙasashen waje.

    Da yake magana da manema labarai bayan wallafa saƙon a shafukan sada zumunta, Trump ya ce shi ba “babban mai goyon bayan” Fafaroma ba ne, wanda ya yi ta bayyana ra’ayoyinsa kan yaƙin Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.

    A nasa ɓangaren, Fafaroma Leo ya bayyana barazanar da shugaban ya yi ta rusa al'umma da tarihin Iraniyawa a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba”.

    Trump ya ƙara da cewa ba ya son Fafaroma da ke sukar shugaban Amurka, yana mai ikirarin cewa bai zama lallai Fafaroma ya hau kujerar da yake kai ba da ba shi ne a Fadar White House ba.

    A lokacin hutun Easter kuwa, Fafaroma Leo ya roƙi shugabanni a bainar jama’a da su kawo ƙarshen tashin hankali tare da daina bautar da jama'a da kuma ƙuntata masu.

  11. Hare-haren Rasha sun ci gaba a Ukraine bayan tsagaita wuta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An sake samun hare-haren Rasha a Ukraine bayan ƙarewar wa’adin tsagaita wuta da aka ayyana domin bikin Easter na Orthodox a ƙarshen ranar Lahadi.

    Rahotanni sun ce an ji ƙarar fashe-fashe a yankunan Sumy da Dnipro-petrovesk da kuma Kirovoh-rad.

    Haka kuma an ji ƙarar garkuwar tsaron sararin samaniya a birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Tsagaita wutar dai ba ta cika lokacin da aka kwashe ba, sai da ɓangarorin biyu suka zargi juna da ƙarya yarjejeniyar sau da dama.

  12. Peter Magyar ya zama firaiministan Hungary bayan doke Viktor Orban a zaɓen

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan ƴan adawa a Hungary sun shafe dare suna bukukuwa bayan gagarumar nasarar da Peter Magyar da jam’iyyarsa ta Tisza ta samu a zaɓen ƙasar.

    Jam’iyyar Tisza mai goyon bayan muradun ƙungiyar tarayyar Turai ta samu kashi biyu bisa uku na kujerun majalisar dokokin ƙasar, lamarin zai ba ta damar canza kundin mulkin ƙasar.

    Mr Magyar ya yi jawabi ga ɗinbin magoya bayansa a Budapest, inda ya ce sun ƙwato ƴancin Hungary ta hanyar kawar da gwamnatin firaminista Viktor Orban.

    Mr Magyar ya shaida wa magoya bayan nasa cewa da wannan nasara, Hungary za ta koma yadda take a baya, a matsayin babbar ƙawa ga ƙungiyar tarayyar Turai da kuma ƙngiyar tsaro ta NATO.

    Tuni dai Viktor Orban ya kira Peter Magyar ta waya, tare da taya shi murnar nasara a zaɓen, sannan kuma ya yi jawabin karɓar ƙaddara ga ƴan jam’iyyarsa da ta sha kayi.

    A gefe guda kuma ƴan adawa ne suka shiga shagulgulan murnar wannan nasara, inda suka shafe dare suna kaɗe-kaɗe da raye-raye,

    Wannan dai gagarumar nasara ce ga jam’iyya mai ra’ayin mazan jiya da aka kafa shekau biyu da suka gabata, kuma ta janyo murna da farin ciki a ƙasar da ma ƙasashen Turai.

    Mr Orban wanda abokin ɗasawar Donald Trump da kuma Vladimir Putin ne ya bayyana Rashin nasarar tasa a matsayin abin baƙin ciki.

    Ya dai shafe shekau 16 yana jan ragamar gwamnatin Hungary.

  13. Gwamna Zulum ya ce sun rufe kasuwar Jilli

    ..

    Asalin hoton, Zulum Twitter

    Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatin jihar Bornon ta rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka gabata kasancewarta matattarar ƴan ta'adda.

    Gwamnan wanda ya faɗi hakan a wata sanarwa da yake mayar da martani ga harin ’kuskure" da sojojin saman Najeriya suka musanta wanda bayanai suka nuna mutum fiye da 50 sun mutu, ranar Asabar.

    “An sanar da ni kan abin da ya aru dangane da harin sama da rundunar sojin sama ta kai a kasuwar Jilli da ke kan iyakar Borno da Yobe. Ina son sanar da cewa gwamnatin Borno ta rufe kasuwar Jilli da Gazabure shekaru biyar da suka wuce.”

  14. Farashin ɗanyen mai ya tashi sakamakon rikicin Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin mai ya tashi bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, da kuma sanarwar da Washington ta yi cewa za ta rufe mashigar tekun Iran baki ɗaya.

    Farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi da fiye da kashi bakwai cikin ɗari, inda ya kai dala 103 kowacce ganga.

    Iran dai ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin ruwan soji da ya doshi mashigar Hormuz.

    Sa'o'i bayan alwashin Shugaba Trump na hana zirga-zirgar jiragen ruwan, rundunar sojin Amurka ta yi ƙarin haske kan batun, inda ta ce matakin zai shafi jiragen ruwa ne da kodai suka tashi daga gaɓar tekun Iran ko kuma suke kan hanyar zuwa can.

    Ta ce sojojin Amurka ba za su hana jiragen ruwa daga wasu tashoshin wucewa ta mashigar Hormuz ba.

    Birtaniya dai ta ce ba za ta shiga yunƙurin aiwatar da matakin na Amurka ba.

    Duk da yawan dakarun sojin Amurka a Gabas ta tsakiya, Iran ta yi nasarar jigilar miliyoyin gangar manta zuwa sassan duniya a lokacin da ake ci gaba da yaƙin, wani abu da fadar White House ta sha alwashin daƙilewa.

    A nata ɓangaren, rundunar sojin Iran ta yi gargaɗin cewa duk wani jirgi da ke ƙoƙarin kutsa kai ta mashigar Hormuz zai ɗanɗana kuɗarsa.

    Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa ko kaɗan bai damu ba da matakin da Iran za ta ɗauka, kodai ta koma a ci gaba da tattaunawa ko kuma ta yi biris, yana mai cewa zabi ya rage mata.

  15. Iran ta sha alwashin kai hari ga jiragen ruwan Amurka da ke son toshe Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Press TV

    Rundunar juyin-juya halin Iran ta IRGC, ta yi barazanar kai hari kan duk wani jirgin ruwan sojin Amurka da ya doshi mashigar Hormuz da Trump ya ce zai kai wa jiragen dakon mai hari,.

    Wannan dai na zuwa ne bayan da rundunar sojin Amurka dai ta ce umarnin da shugaba Trump ya bayar na toshe mashigar Hormuz ga jiragen da ke fita ko zuwa mashigar zai fara aiki da yammacin Litinin, agogon Iran.

    Shugaba Trump ya sanar da matakin ne bayan tattaunawa da Iran ta gaza cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen rikicin da kuma buɗe wannan muhimmiyar hanyar kasuwanci gaba ɗaya.

    Jim kaɗan da sanarwar Trump ɗin farashin ɗanyen mai na Brent ya yi tsallen baɗake inda ya haura dala 102.

    Mista Trump ya ce matakin zai ƙara zama matsin lamba ga Iran, don sake buɗe mashigar ta Hormuz.

    Shugaban majalisar wakilan Iran Muhammad Bagher Ghalibaf, ya ce barazanar ba ta ɗaga musu hankali ba kuma suna jira.

  16. Buɗewa

    Masu bibiar shafin BBC Hausa na kai tsaye barkan ku da safiyar ranar Litinin wadda hausawa ke yi wa taken ko nasara na tsoran ki.

    Kamar kullum yau ma muna tafe da labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a yaƙin da AMurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran da ma sauran al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu a shafin da ma sauran shafukan BBC Hausa na Facebook da Instagram da X da Yotube.