Shawarwari 4 da IMF ya bai wa Najeriya don sauƙaƙa wa ƴanƙasar raɗaɗin cire tallafi

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da muhawara kan batun cire tallafin man fetur ke ci gaba da ɗaukar hankalin al'umma a Najeriya, wani babban jami'in Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya gabatar da wasu shawarwari guda uku da ya ce za su iya taimaka wa gwamnati wajen rage raɗaɗin da ƴan ƙasa ke fuskanta sakamakon wannan manufa.
Batun tallafin man fetur ya sake ɗaukar hankali a Najeriya bayan da ɗantakarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin mayar da tallafin idan aka zaɓe shi a 2027.
A watan Mayun 2023 ne Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na rantsuwar kama aiki.
Shugaba Tinubu ya kafa hujjar cewa cire tallafin wani yaƙi ne da cin hanci da buƙatar bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Sai dai tun daga lokacin ƴanƙasar ke kokawa da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki sakamakon matakin.
Fargabar IMF da shawarwarinta ga Najeriya
A ƴan kwanakin nan ne dai gwamnatin ƙasar ta sanar da rangwamen man fetur a gidajen man NNPPCL mallakin gwamnatin ƙasar na wata ɗaya.
Wani abu da wasu ke ganin kamar mayar da tallafin man ne a fakaice.
To sai dai a jawabin da ya yi a taron IMF da Bankin Duniya da ke gudana a Thailand, daraktan sashen kuɗi na IMF, Rodrigo Valdés, ya shawarci Najeriya kada ta mayar da tallafin man.
Mista Rodrigo ya ce mayar da tallafin zai sake jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin mawuyacin hali.
A maimakon haka ya shawearci ƙasar ta ɗauki wasu matakai huɗu da ya ce za su taimaka wajen rage raɗaɗin cire tallafin da ƴanƙasar ke ji.
Ga jerin shawarwarin da IMF ya bayar:
1. Tallafa wa marasa ƙarfi
Rodrigo Valdés ya ce yana da kyau gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan tallafa wa marasa ƙarfi da kuɗaɗe.
Tun bayan cire tallafin man fetur ɗin dai gwamnatin Najeriyar ta ɓullo da wasu shirye-shiryen tallafa wa ƴanƙasar da kuɗaɗe domin abin da ta kira rage raɗaɗi.
To amma wasu ƴan ƙasar sun riƙa sukar shirye-shiryen da cewa ba sa kai wa hannun mutanen da suka kamata.
2. Tallafa wa manoma
Shugaban sashen kuɗin na IMF ya kuma wani tallafin da ya kamata gwamnatin Najeriyar ta mayar da hankali a kansa shi ne tallafa wa manoma.
A baya gwamnati ta sanar da tallafa wa manoma da takin zamani domin bunƙasa harkokin noma.
Sai dai manoman sun riƙa kokawa da cewa matakin gwmanati na buɗe boda ta janyo musu koma-baya a harkokinsu na noma.
3. Rage hauhawar farashi
Asusun na IMF ya kuma buƙaci gwamnatin Najeriyar ta ɗauki matakan rage hauhawar farashi domin sama wa talakawa ƙansar sauki.
IMF ya buƙaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya tabbatar an dawo da hauhawar farashin kayayyaki (inflation) zuwa matakin da manufofin kuɗi na ƙasar suka tsara.
"Hauhawar farashin kayayyaki na da yawa, amma a lokaci guda tasirin waɗannan sauye-sauyen tattalin arziƙi na rage ko takaita ayyukan tattalin arziƙi''.
IMF ya ce a irin wannan yanayi ne babban banki ke buƙatar daidaita tsakanin waɗannan ƙalubalen guda biyu.
''Dole ne ya tabbatar da cewa an dawo da hauhawar farashin kayayyaki zuwa matakin da aka sa a gaba cikin wa'adin manufofin kuɗi, wanda a mafi yawan lokuta muke ɗauka a matsayin shekaru biyu zuwa uku."
4. Ciyar da ɗalibai a makarantu
Babban jami'in na IMF ya kuma yi kira ga gwamnatin ƙasar ta ci gaba da shirinta na ciyar da ɗalibai makarantu, wanda ya ce zai taimaka wajen rage raɗaɗin.
A baya gwamnati ta riƙa ciyar da dalibai abinci a makarantun furamare a matsayin tallafi.
To sai dai masu suka na ganin wasu na fakewa da wannan salo wajen laƙume kuɗaɗen gwamnati.
Farfesa Muttaqa Muhammad Usman, Malami a sashen nazarin tattalin arziki na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce IMF na goyon bayan cire tallafin mai ne saboda bashin da yake bai wa gwamnatin ƙasar.
''Shugabannin ƙasashen sun yi imani da waɗannan kafofi, wajen karɓar bashi, wanda kuma su suke ƙara kuɗin ruwa mai yawa, kuma ba shi ne da yake zurarewa'', in ji shi.
Masanin tattalin arzikin ya ce har yanzu ƙasar ba ta samu ci gaba da take hanƙoro bayan cire tallafin man.
Ya ce a duk lokacin da man fetur ya ƙara kuɗi a duniya to hakan zai ya shafi tsadar kayayyaki saboda ƙaruwar kuɗin sufuri.
Me ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi?
Farfesa Muttaqa ya ce abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi shi ne ta zauna da masana tattalin arziki domin ɓullo da matakan da suka dace domin magance matsin tattalin arziki da take ciki.
''Ya kamata a duba masalahar ƴanƙasa, ba abin da turawa suke so ba'', in ji shi.
Masanin tattalin arzikin ya ce yana da kyau gwamnati ta inganta masana'antu da matatun man fetur, domin samun man cikin sauki ta yadda ƴankasar za su samu sauƙi.
''Bai kamata gwamnati ta riƙa biye wa wasu da ke wajen ƙasar, wajen ɗaukar matakan da ba sa yi wa ƴan ƙasar daɗi'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.
Malamin jami'ar ya ƙara da cewa fiye da shekara 40 da suka gabata, gwamnatocin Najeriya-daban sun riƙa yin alƙawarun gyara tattalain arziki da kuma inganta shi, amma har yanzu hakan bai samu ba.































