Jihohi 10 da suka fi fama da talauci a Najeriya

Asalin hoton, Multiple/FB
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Kimanin mutane miliyan 123 ne ke barazanar faɗawa cikin matsanancin talauci a Najeriya, kamar yadda wani rahoto na Bankin Duniya ya nuna a 2026.
Rahotanni na baya-bayan nan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar (NBS) ta fitar sun nuna cewa jihar Sokoto ce ta fi fama da talauci a Najeriya, inda aka ƙiyasta kusan kashi 90.5% na al'ummarta suna rayuwa cikin matsanancin talauci.
Sai dai wani rahoton hukumar raya ƙasashe na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ya wallafa, ya nuna cewa yawan mutanen da ke fama da talauci a yankuna daban-daban na Najeriya ya bambanta sosai kuma ba jihar Sokoto ke kan gaba ba.
Rahoton ya bayyana wasu daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da talauci, ciki har da rashin ilimi, ƙarancin damar samun aikin yi, da kuma matsalolin tsaro. Haka kuma, ya nuna cewa yawancin jihohin da suka fi fama da talaucin suna yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
A cewar rahoton na UNDP, ga jerin jihohi 10 da suka fi fama da talauci a Najeriya a shekarar 2026:
1. Kebbi
Jihar Kebbi ce ke kan gaba a jerin jihohin Najeriya da rahoton UNDP ya ce ta fi fam da talauci a ƙasar. Rahoton ya nuna cewa talaucin a jihar ya shafi fannoni daban-daban na rayuwa, ciki har da ilimi, yanayin gidaje, tsaftar muhalli da samun muhimman ayyuka.
Bayanan UNICEF na shekarar 2019 sun nuna cewa kashi 39 cikin 100 na al'ummar jihar ne kawai ke samun ruwan sha mai tsafta, yayin da kashi ɗaya cikin 100 kacal ke samun ruwan sha mai inganci.
Waɗannan alkaluma sun nuna wasu matsalolin da suka daɗe suna addabar jihar, musamman ƙarancin muhimman ababen more rayuwa.
2. Yobe
Rahoton da UNDP ta fitar ya nuna cewa Jihar Yobe ce ta biyu a jerin jihohin da suka fi fama da talauci a Najeriya bisa ƙididdigar mutanen ke cikin ƙangin talauci (Multidimensional Poverty Index, MPI).
Rahoton ya nuna cewa talaucin jihar ya samo asali ne daga matsaloli masu yawa da suka haɗa da ƙarancin ilimi, rashin zuwa makaranta, matsalolin abinci mai gina jiki da kuma ƙarancin kayan more rayuwa.
Haka kuma jihar na fuskantar ƙalubale a bangaren gidaje, tsaftar muhalli, samun ruwan sha da makamashin girki. A cewar rahoton, yawan waɗannan matsaloli a lokaci guda na nuna cewa iyalai da dama ba sa samun muhimman abubuwan rayuwa yadda ya kamata.
3. Sokoto
Duk da cewa rahotannin baya-bayan nan na Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) sun taɓa nuna Sokoto a matsayin jihar da ta fi fama da talauci, rahoton UNDP ya sanya ta a matsayi na uku a ma'aunin MPI.
Rahoton ya nuna cewa matsalolin da suka fi addabar jihar sun haɗa da ilimi, musamman shekarun karatu da halartar makaranta, da kuma rashin wadataccen ruwan sha mai tsafta da kuma tsaro.
Haka kuma, akwai ƙalubale a bangaren gidaje, wutar lantarki da tsaftar muhalli.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin tsaro a yankin arewacin Najeriya kuma matsalar ta raba dubban mutane da muhallansu.
4. Jigawa
A matsayi na huɗu kuwa rahoton ya ce Jihar Jigawa ce tana cikin wuraren da talauci ya yi kamari a Najeriya.
Bayanan rahoton sun nuna cewa ƙarancin ilimi, abinci mai gina jiki da kuma rashin wadatattun ayyukan ruwa da tsaftar muhalli na daga cikin manyan abubuwan da ke jefa al'umma cikin talauci.
An kafa jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991.
An ƙirƙiro jihar ne daga tsohuwar jihar Kano a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB)
5. Zamfara
Jihar Zamfara ta biyo baya a matsayi na biyar cikin jihohin da suka fi fama da talauci a Najeriya.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da ke da mafi yawan yara da ba sa zuwa makaranta. Rufe makarantu saboda hare-haren ƴan bindiga da rashin guraben aiki ga matasa sun ƙara jefa mutane cikin talauci.
A cewar rahoton UNDP, matsalolin ilimi da na abinci mai gina jiki sun fi ƙamari a jihar. Haka kuma akwai ƙarancin abubuwan more rayuwa kamar gidaje masu kyau, ruwa mai tsafta da makamashin girki.
6. Gombe
Rahoton ya ce Gombe ta shida cikin jihohin da suka fi fama da talauci a ƙasar.
Jihar Gombe, wadda ake yi wa laƙabi da "Jewel in the Savannah" (Lu'u-lu'un Cikin Hamada), tana ɗaya daga cikin jihohin da ke yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya. Ita ce jiha ta farko a yankin da ke kan gaba a waɗannan alƙaluma.
Ko da yake matakin talaucin jihar bai kai na wasu jihohin da ke saman jadawalin ba, rahoton ya nuna cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale da suka shafi ilimi, makamashin girki da tsaftar muhalli.
Jihar tana ƙunshi ƙabilu da dama da suka haɗa da Fulani, Tangale, Waja, Tera, Hausa, Bolewa, Kanuri, da sauransu.
7. Borno
Jihar Borno ce ke biye da Gombe a wannan jadawali. Tana mataki na bakwai a jadawalin UNDP.
Jihar Borno, wadda ke yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, tana ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar ƙalubalen matsanancir talauci.
Ko a 2025, rahoton NBS kan talauci ya nuna cewa kimanin kashi 64% zuwa 72.5% na al'ummar jihar suna rayuwa cikin talauci.
Rahoton ya nuna cewa talaucin jihar ya fi shafar al'umma ta fuskar ilimi, abinci mai gina jiki da kuma rashin wadatattun kayan more rayuwa. Haka kuma matsalolin gidaje, ruwa da tsaftar muhalli suna cikin abubuwan da suke ƙara talauci a jihar.
8. Bauchi
A matsayi na takwas kuwa akwai Jihar Bauchi.
Rahoton UNDP ya nuna cewa talaucin da ake samu a jihar ya fi alaƙa da matsalolin ilimi, rashin tsaftar muhalli da samun ruwan sha.
Bauchi tana fama da matsaloli da dama da suka shafi tattalin arziki, zamantakewa, da tsaro, waɗanda suka dabaibaye jihar da talauci.
Alƙaluman NBS sun nuna cewa kimanin kashi 73.9% na al'ummar Jihar Bauchi suna rayuwa cikin talauci.
Gwamnatin jihar ta sha bayyana damuwa kan yadda ƴan bindiga suka mamaye wasu yankuna da dazuzzuka, musamman a ƙaramar hukumar Alkaleri da sauran iyakokin jihar.
9. Neja
Jihar Neja ce ta tara a jerin jihohin da rahoton ya nuna sun fi fama da talauci.
Jihar Neja tana fuskantar ƙalubalen talauci na fuskoki daban-daban, ko da yake babban birninta Minna yana samun ci gaba, amma yankunan ƙauyuka da ke da mafi yawan jama'a suna fama da matsananciyar yunwa da fatara.
Ko a rahotannin Hukumar NBS sun nuna cewa fiye da kashi 60% na al'ummar jihar suna rayuwa cikin talauci. Wannan matsala ta ta'allaka ne ga rashin ingantattun asibitoci, rashin tsaftataccen ruwan sha, da rashin kyawawan hanyoyin karkara don kwashe amfanin gona.
10. Katsina
Katsina ce ta cike jerin jihohi goma da suka fi fama da talauci a rahoton.
A cewar UNDP, ilimi, abinci mai gina jiki da rashin wadatattun ayyukan ruwa da tsaftar muhalli suna daga cikin manyan matsalolin tsaro da ke addabar jihar.
Yankunan ƙauyuka da ƙananan hukumomi da dama suna fuskantar hare-hare akai-akai.
Ƴan bindiga suna sace mutane don neman kuɗin fansa da satar shanu, lamarin da ya tilasta wa dubban mazauna ƙauyuka barin gidajensu.




























