Kotu ta ɗaure wata mata shekaru biyu bisa laifin safarar yarinya ƴar shekara 16

Asalin hoton, Getty Images
Babbar kotu a jihar Borno da ke Maiduguri ta yanke wa Fatima Sanda, mai shekaru 37, hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari bisa laifin safarar wata yarinya ’yar shekara 16 da tursasa mata shiga harkar karuwanci.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Aisha M. Ndume, ta same ta da laifin kai yarinyar ga wasu mutane domin cin zarafinta ta hanyar lalata da ita.
Hukumar yaƙi da safarar mutane ta Najeriya (NAPTIP) ce ta sanar da hukuncin a shafinta na sada zumunta.
Ta ce hukuncin ya yi daidai da sashe na 16(1) na dokar hana safarar mutane da gudanar da ayyukan yaƙi da ita ta shekarar 2015, wadda aka yi wa kwaskwarima.
Baya ga hukuncin ɗaurin, kotun ta umarci Fatima Sanda da ta biya yarinyar diyyar naira 500,000.




























