Mene ne amfanin shan hantsi ga lafiyarmu?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Claudia Posada
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Wasu mutane suna buƙatar mintuna kaɗan ne kawai na hasken rana a kowace rana a lokacin bazara, yayin da wasu kuma ke buƙatar shan hantsi na lokacin da ya wuce haka?
Hotunan Coco Chanel bayan ta yi balaguro cikin jirgin ruwa a Tekun Bahar Rum a shekarar 1923, inda fatarta ta jeme, sun taimaka wajen yaɗa al'adar shan hantsi domin neman fata ta sauya launi. Wannan launin fata da ta samu ya zama alamar nasara a zamantakewa, kuma ya canza yadda al'ummomin Yammacin duniya ke kallon hasken rana.
Daga farko zuwa tsakiyar ƙarni na ashirin, an riƙa amfani da hasken rana a matsayin magani a cibiyoyin jinya domin kula da matsalolin ƙashi saboda ƙarancin sinadarin Vitamin D) da tarin fuka. A wancan lokaci kuma, an kasance ana ƙarfafa ra'ayin cewa jemewa ga farar fata ko rinewar fata ga baƙaƙen fata sakamakon shan hantsi alama ce ta ƙoshin lafiya.
Bayan ƙarni guda, dangantakarmu da hasken rana ta zama mai matuƙar sarkakiya. A cikin shekaru hamsin da suka gabata, ƙaruwar masu kamuwa da cutar sankarar fata ta sa aka sake nazarin wasu hanyoyin magani, yayin da ayyukan wayar da kan jama'a suka mayar da hankali kan kariya da kuma ƙarfafa amfani da man kariya daga illar hasken rana (sunscreen). Har yanzu akwai tabbatacciyar alaƙa tsakanin yawan shan hantsi da kuma ƙarin haɗarin kamuwa da sankarar fata.
Sai dai a cikin 'yan shekarun nan, bincike ya nuna cewa abin da ake kira "shan hantsi na matsakaicin lokaci" na da amfani ga lafiyar ƙwaƙwalwa, samar da yawan sinadarin Vitamin D a jiki da kuma ƙarfafa garkuwar jiki.
Bincike ya kuma nuna cewa hakan na iya rage haɗarin kamuwa da wasu nau'ikan cutar daji, inganta lafiyar zuciya da jijiyoyin jini, da kuma taimakawa wajen kyautata aikin ƙwaƙwalwa da samun ingantaccen barci.
To amma ta yaya za a iya cin wannan moriyar ba tare da faɗawa cikin haɗarin da hasken rana kan haifar ba? Kuma a zahiri, ya yawan hasken ranar da muke buƙata?
Me ya sa muke buƙatar hasken rana?
Samun hasken rana na matsakaicin lokaci na taimaka wa jiki wajen samar da Vitamin D, wanda yake da muhimmanci ga lafiyar ƙasusuwa da kuma aikin tsokoki. Wani bincike ya nuna cewa yawan Vitamin D a jiki na da alaƙa da raguwar kamuwa da wasu cututtukan daji da mace-mace masu alaƙa da su, tare da rage yiwuwar kamuwa da cutar sikari nau'i na biyu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hasken rana kuma na taimakawa wajen rage hawan jini. Lokacin da sinadarin radiation na hasken rana wato UVA ya kai ga fata, yana sa jiki ya fitar da wani sinadari mai suna nitric oxide, wanda ke faɗaɗa jijiyoyin jini. Hakan na rage haɗarin bugun zuciya da kuma shanyewar jiki.
Wani babban bincike da aka gudanar kan mata 29,518 a Sweden tsawon fiye da shekara 20 ya gano cewa amfani da gadajen kwanciya a rana yana da alaƙa da ƙaruwa a yawan mace-mace gaba ɗaya da kuma mace-macen da cutar daji ke haifarwa.
Rebecca Mason, farfesa a fannin ilimin yadda jiki ke aiki a Jami'ar Sydney da ke Australia, ta ce samun isasshen Vitamin D yana taimakawa wajen "rage kumburi a jiki, taimakawa wajen yaƙi da ƙwayoyin cuta masu mamaya, da kuma daidaita aikin garkuwar jiki ta yadda ba za ta rika kai hari ga ƙwayoyin jikin mutum ba."
An kuma nuna cewa hasken rana na taimakawa wajen inganta barci da kuma ƙarfafa aikin kwakwalwa. Hasken safiya yana ɗauke da wasu nau'ikan haske masu shuɗi (blue light) da ke sa kwakwalwa ta fahimci cewa lokaci ne na yini, abin da ke ƙara samar da sinadarin cortisol tare da rage samar da sinadarin barci na melatonin. Saboda haka mutum kan ji ya fi kasancewa cikin faɗakarwa da kuzari.
Ƙarin kasancewa a hasken rana na iya inganta tunani da lafiyar ƙwaƙwalwa. Wani bincike da ya ƙunshi mahalarta fiye da 360,000 ya nuna akwai alaƙa tsakanin shan hantsi (kimanin awa ɗaya da rabi) da raguwar haɗarin kamuwa da cutar mantuwa.
Hasken rana kuma na ƙara yawan sinadarin serotonin a kwakwalwa, wanda ke taimakawa wajen kwantar da hankali. An gano cewa marasa lafiya da ake kula da su saboda matsananciyar damuwa a ɗakuna masu hasken rana suna warkewa da sauri. A gefe guda kuma, rashin samun isasshen hasken rana na iya ƙara haɗarin bayyanar alamomin damuwa, rashin walwala da kuma rashin barci.

Asalin hoton, Getty Images
Sau nawa ya kamata mu sha hantsi?
Ko da yake shawarwarin masana kan yawan hasken rana da ake buƙata na bambanta bisa shekaru, wurin zama da kuma nau'in fata, yawancin masana suna ba da shawarar samun hasken rana na ɗan gajeren lokaci amma a kai a kai.
A cewar Rebecca Mason, mafi dacewar lokacin shan hantsi domin samar da Vitamin D shi ne da tsakar rana, inda hasken UVB ya fi ƙarfi. Ta ce ya fi kyau a kasance a rana na ɗan lokaci kaɗan amma sau da yawa.
Ga masu farar fata, Mason ta ba da shawarar a riƙa shan hantsi na ƴan mintuna a yawancin ranakun mako. A wuraren da hasken UV ya fi ƙarfi kuwa, ya fi kyau a yi hakan da sassafe ko kuma da yammaci kaɗan kafin rana ta take.
Mutanen da ke da fata mai duhu na iya buƙatar ƙarin lokaci a rana saboda yawan sinadarin melanin da ke fatarsu yana jinkirta samar da Vitamin D. Wani bincike ya nuna cewa a lokacin bazara a Birtaniya, masu duhu suna buƙatar kusan mintuna 25 na hasken rana domin samar da isasshen Vitamin D.
Mason ta ce mutanen da ke da fata mai matuƙar haske, ko waɗanda suka taɓa kamuwa da cutar melanoma ko kuma suna da tarihin cutar a iyalinsu, da kuma masu ɗimbin kurajen fata suna cikin haɗarin kamuwa da sankarar fata. Haka kuma masu amfani da magungunan rage ƙarfin garkuwar jiki suna buƙatar ƙarin kulawa.
Bincike ya nuna cewa masu duhun fata suna da kariya daga lalacewar ƙwayoyin halitta (DNA) da hasken UV ke haifarwa, yayin da masu hasken fata ke iya fuskantar irin wannan illa da zarar sun shiga rana. Wannan na nuna muhimmancin ba da shawarwari da suka dace da nau'in fatar kowane mutum.
Masu fata mai duhu suna da yawan sinadarin melanin, wanda ke aiki a matsayin kariyar halitta daga hasken UV mai illa.

Asalin hoton, Getty Images
Ko da yake irin kariyar da ake buƙata daga hasken rana na bambanta gwargwadon nau'in fata da ƙarfin hasken UV, Mason ta ce masu fata mai duhu, ya kamata su rika sanya tabarau na kariya idan suna cikin rana.
A shekarar 2024, ƙasashen Australiya da New Zealand sun kasance cikin na farko da suka ɗauki sabuwar hanya da ta yi la'akari da bambance-bambancen mutane. Sun Sun rarraba al'ummarsu zuwa rukuni uku bisa ga nau'in fata da kuma haɗarin kamuwa da sankarar fata da mutum ke fuskanta.
Mene ne illolin yawan zama a rana?
Yawan shiga rana na iya ƙara haɗarin ƙonewar fata da kuma saurin tsufar da fata. Haka kuma, shi ne babban abin da ke haddasa sankarar fata.
A Birtaniya, yawan sabbin masu kamuwa da cutar melanoma (wacce ita ce mafi hatsarin nau'in sankarar fata) da ake gano wa a kowace shekara ya kai mafi girman matsayi a tarihi, inda adadin ya zarce mutum 20,000 a karon farko. Ƙungiyar bincike kan cutar daji ta Cancer Research UK ta ce yawan shiga rana na taimakawa wajen samun ƙaruwar masu fama da cutar.
Sankarar fata ita ce nau'in cutar daji da ta fi yawaita a Amurka, inda ake sa ran gano sama da mutum 112,000 sabbin masu fama da melanoma mai kutsawa cikin jiki a wannan shekara.
Taƙaita shan hantsi ga yara da matasa ke samu yana da muhimmanci ƙwarai, domin bincike ya nuna cewa yawan hasken rana da mutum ya samu a = shekaru 20 na farkon rayuwarsa na taka muhimmiyar rawa wajen tantance yiwuwar kamuwarsa da sankarar fata a gaba.
Yawan zama a rana na iya haifar da yanar ido. Ko da yake sau da yawa ana iya magance wannan matsala ta hanyar tiyata, tana iya kaiwa ga makanta idan ba a yi magani ba.
Likitoci suna ba da shawarar sanya tabarau mai kariyar UV 400 domin kare idanu daga illolin hasken rana mai cutarwa.
Mene ne illolin ƙarancin hasken rana ga jiki?
Idan kana zaune a yankin da ke da ƙarancin hasken rana, akwai yiwuwar ka fuskanci ƙarancin Vitamin D, musamman a lokacin hunturu, a cewar Rhodes. Baƙar fata, waɗanda ba sa samun hasken rana, ko kuma waɗanda suke rufe yawancin jikinsu, su ne suka fi fuskantar wannan haɗari. Ƙarancin Vitamin D na iya shafar ƙasusuwa.
Sai dai ana iya gyara matsalar ƙarancin sinadarin Vitamin D ta hanyar shan magungunan da za su taimaka wajen samar da sinadarin. Sai dai amfani da magungunan ya danganta ga shekaru da kuma ƙa'idojin da ƙasashe suka gindaya.
Yana da muhimmanci a guji shan maganin Vitamin D fiye da ƙa'ida, kamar yadda masana suka bayyana.
A kula: An tanadi wannan bayani ne domin ilimantarwa kuma ba zai maye gurbin shawarar likita ko wani ƙwararren ma'aikacin lafiya ba.





























