Ƙasashen duniya da tattalin arziƙinsu zai fi haɓaka a 2026

Asalin hoton, Getty Images
Bayan rashin tabbas da tattalin arziƙin duniya ya fuskanta a shekarar da ta gabata, tattalin arziƙin ya sake gamuwa da cikas sanadiyyar rikicin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya.
Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta ce ko da rikicin bai yi tsawo ko kuma ya ƙazance fiye da ƙima ba, duk da haka hasashen da aka yi na ci gaban tattalin arzikin duniya a 2026 zai gamu da cikas, inda zai yi rauni zuwa 3.1.
Amma hukumar ta yi gargadin cewa idan yain na Gabas ta Tsakiya ya tsananta, har ya kai ga cewa farashin makamashi ya jijjiga duniya, hasashen ci gaban tattalin arziin duniya zai iya faowa zuwa kashi 2% kacal a shekarar ta 2026.
Haka nan tashin farashin kaya zai iya haura kashi 6% a shekarar 2027.
Farashin man fetur da gas ya yi tashin da ba a gani ba a baya-bayan nan tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran.
Iran ta toshe mashigar Hormuz, wata hanyar ruwan teku mai muhimmanci ga sufurin ɗanyen man fetur a duniya, lamarin da ya zama babban abin taƙaddama tsakanin Iran din da Amurka.
Ga jerin ƙasashen da hasashen na hukumar IMF ya ce za su fi samun bunƙasar tattalin arziƙi duk da halin da duniya ke ciki:
Indiya
Indiya ta riƙe matsayinta ta ƙasar da tattalin arziƙinta ke haɓaka fiye da kowace ƙasa a duniya.
Hasashen IMF ya nuna cewa Indiya za ta samu haɓakar tattalin arziƙi da kashi 6.5% duk da halin da tatta;lin arziƙin duniya ya shiga sanadiyyar yaƙin Iran.
IMF ta alaƙanta haɓakar tattalin arziƙin Indiya da shirin da ta faro tun a shekara ta 2025, wanda ya sa ta iya shanye matsin ƙare-ƙaren haraji da buƙatun cikin gida.
China
Haɓakar tattalin arziƙin China na tafiyar hawainiya sanadiyyar rikicin kasuwanci a duniya, musamman tsakaninta da Amurka da kuma wasu ƙalubale a harkar gine-gine.
A haka, IMF ta rage hasashenta na ci gaban tattalin arziƙin China a 2026 daga 4.5% zuwa 4.4.
Sai dai hasashen da hukumar ta yi kan bunƙasar tattalin arziƙin China da kashi 4% a shekarar 2027 bai canza ba.
Ana tunanin cewa China za ta shiga cikin matsi sanadiyyar matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na hana jiragen ruwa daga Iran wucewa ta mashigar Hormuz, kasancewar China ita ce ƙasar da ta fi kowa sayen man fetur daga Iran.
Najeriya
Hasashen haɓakar tattalin arziƙi da kashi 4.1% labari mai daɗi ne ga Najeriya - ƙasa mafi girman tattalin arziƙi a Afirka, duk da cewa hukumar lamunin ta duniya ta rage hasashen ci gaban tattalin arziƙin ƙasar na 2026 da kashi 0.3% daga abin da ta bayyana a farkon shekara sanadiyyar abin da ke faruwa a duniya.
Najeriya ce ƙasar da ta fi fitar da man fetur a nahiyar Afirka, sai dai rikicin Iran wanda ya janyo toshe mashigar Hormuz ya haifar da tashin farashin man fetur da na kayan masarufi a ƙasar.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasar (NBS) ta ce hauhawar farashi ya ƙaru daga 15.06% a watan Fabrairu zuwa 15.38% a watan Maris.
Hauhawar farashin kayan abinci kuma ya ƙaru daga kashi 12.12% zuwa 14.31%
Saudiyya
A matsayinta ta ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke fitar da man fetur a duniya, Saudiyya za ta fuskanci abubuwa da dama.
Yayin da tashin farashin man fetur a duniya zai samar wa ƙasar ƙarin kuɗaɗen shiga, rikicin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya ya jefa ƙasar cikin yanayi na rashin tabbas.
Hukumar lamuni ta duniya ta ce dukkanin ƙasashe masu fitar da man fetur za su samu tagomashi saboda tashin farashin makamashi, duk da cewa rikicin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya ya yi matuƙar illa ga tattalin arziƙin yankin.











