Yadda cin zarafin mata masu buƙata ta musamman ya zama ruwa dare a Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
"Na sha wahala sosai a zuciyata, kuma shi ya sa na zo nan domin in ba da labarina ga mutane."
Waɗannan su ne kalmomin farko da Seo Mi-hyun ta faɗa wa 'yan sanda.
Sue, wadda ke da raunin fahimta tana fama da matsalar haɗa dogayen jimloli, kuma tana iya yin magana ne da gajerun kalmomi da kuma ishara kawai. Duk da haka, har yanzu tana tuna cin zarafin da aka yi mata sosai.
Tana ɗaya daga cikin mutum uku da ke zaune a wata cibiyar kula da masu buƙata ta musamman ta gwamnati a Koriya ta Kudu, waɗanda daraktan cibiyar ya ci zarafinsu ta hanyar lalata.
Lamarin ya girgiza Koriya ta Kudu, tare da haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da yadda ake tafiyar da cibiyoyin gwamnati da ke kula da masu bukata ta musammam.
A farkon wannan watan, wata kotu da ke Seoul ta yanke wa daraktan cibiyar, mai suna Kim, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Sai dai Kim ya ɗaukaka ƙara.
Kotun ta yanke hukuncin ne kusan shekara biyu bayan Sue, wadda ke cikin shekaru 40 da haihuwa, ta fara sanar da mahaifiyarta irin cin zarafin da aka yi mata.
Domin kare martaba da sirrin waɗanda abin ya shafa, an sauya sunayen Sue da wani daga cikin waɗanda aka ci zarafinsu a wannan rahoto.
"Abin da kawai na yi ne shi ne jurewa"
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 2016, Su ta fara zama a Saekdongwon, wata cibiyar kula da mutanen da ke da raunin fahimta.
Cibiyar, wadda take a birnin Incheon na Koriya ta Kudu, tana samun dukkan kuɗaɗenta ne daga gwamnati. Har yanzu tana da kusan mazauna 33, duk da cewa an nemi mahukuntanta su rufe ta bayan aukuwar wannan lamari.
A cewar Su, cin zarafin ya fara ne jim kaɗan bayan ta fara zama a cibiyar. Ta ce Kim kan zo mata da yammaci ko kuma da sassafe, inda kuma yake yi mata fyaɗe.
Ta hannun lauyarta, Ko Eun-young, Su ta ce babu wani babba a cibiyar da za ta iya kai wa kukanta game da abin da ke faruwa. Ta kuma ƙara da cewa tana ganin sauran ma'aikatan cibiyar ba za su taimaka mata ba. Mahukuntan cibiyar ba su mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge ba.
Rayuwarta ta ci gaba da kasancewa haka tsawon kusan shekara goma, har sai da lamarin ya fito fili a watan Fabrairun 2025 bayan da ta samu rauni a kanta.
Ta ce abin ya faru ne lokacin da Kim ya sake ƙoƙarin yin lalata a ita. Su ta ture shi da hannuwanta, sannan Kim ya mayar da martani ta hanyar jefa mata gilashi.
Lauyarta ta shaida wa kotu cewa ma'aikatan cibiyar sun kai ta asibiti ne kuma suka sanar da mahaifiyarta abin da ya faru bayan an yi mata ɗinki a raunin da ta samu a kai.
A cewar lauyar, mahaifiyarta ta nemi a nuna mata bidiyon CCTV domin ta gano yadda ɗiyarta ta ji rauni, amma mahukuntan cibiyar sun ƙi ba ta damar ganin bidiyon, suna masu cewa ba su da izinin su bayar da shi.
Daga nan sai mahaifiyarta ta dawo da ita gida tare da yanke shawarar cewa ba za ta koma cibiyar ba.
Sai bayan da aka faɗa wa Su cewa ba lallai ba ne ta koma Saekdongwon ne ta bayyana wa mahaifiyarta cewa an daɗe ana cin zarafinta ta hanyar lalata. Daga bisani mahaifiyarta ta kai ƙarar lamarin ga 'yan sanda.
"Lokacin da suka gaya mini cewa ba sai na koma Saekdongwon ba, sai na ji zan iya yin magana ba tare da tsoro ba," in ji Su a wata tattaunawa da BBC ta hannun lauyarta.
Da aka tambaye ta yadda ta iya jurewa irin wannan hali ita kaɗai tsawon waɗannan shekaru, sai ta amsa da cewa:
"Na yi haƙuri ne kawai."
Cibiyar na cikin birnin Incheon da ke Koriya ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images
Daga baya, 'yan sanda sun faɗaɗa bincikensu daga bayanan da Su ta bayar zuwa ga sauran mutanen da ke zaune a cibiyar.
Jami'an sun gano akalla wasu mutum biyu da ake zargin sun fuskanci irin wannan cin zarafi. Ɗaya daga cikinsu ita ce Lee Mina, wadda ta ce Kim ya yi mata fyade yayin da take banɗaki.
A farkon wannan wata, alkalin da ke sauraron shari'ar ya yanke hukuncin cewa shaidun dukkan mutanen uku da suka kai ƙara abin gaskiya ne kuma sahihi.
Kotun ta yanke wa Kim hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari saboda laifukan fyaden da ya yi wa Lee da Su. An sassauta hukuncin zuwa shekaru biyar idan aka kwatanta da hukuncin da masu gabatar da ƙara suka nema. Sai dai Kim ya musanta dukkan zarge-zargen kuma ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Game da mutum na uku kuwa, kotun ta same shi da laifin aikata wani nau'in cin zarafin lalata da bai kai matsayin fyade ba. Alkalin ya ce an yi watsi da zargin fyaden ne saboda kotun ba ta samu cikakkiyar hujjar da ke tabbatar da cewa an yi amfani da ƙarfi ko barazana ta yadda wanda abin ya shafa ba zai iya yin turjiya ba.
Wani haɗaɗɗen kwamitin ƙungiyoyin kare haƙƙin masu bukata ta musamman da sauran ƙungiyoyin farar hula ya soki hukuncin, yana mai cewa ikon da waɗanda abin ya shafa suke da shi na yin turjiya bai kamata ya zama abin da za a yi la'akari da shi wajen ƙayyade hukunci ba.
Kwamitin ya kuma soki yadda aka gudanar da binciken, yana mai cewa hukumomi sun gaza gano wasu mutane da ka iya kasancewa sun fuskanci irin wannan cin zarafi.
A watan Nuwamban 2025, bayan fara bayyana zarge-zargen cin zarafin, hukumomin yankin Ganghwa sun ba wata ƙungiya daga Jami'ar Woosuk aikin gudanar da cikakken bincike kan halin da mazauna cibiyar Saekdongwon ke ciki.
Rahoton ƙungiyar, wanda aka gabatar wa kotu a matsayin hujja, ya nuna cewa adadi mai yawa na mazauna cibiyar, akalla mutum 10, na iya kasancewa sun fuskanci cin zarafin lalata daga Kim.
Sai dai kotun ba ta yi tsokaci a kan waɗannan bayanai ba yayin shari'ar.
A cewar kafafen yaɗa labarai na cikin gida, 'yan sanda sun fuskanci ƙalubale wajen yi wa mazauna cibiyar tambayoyi domin gano cikakkun bayanai game da zarge-zargen, domin yawancinsu suna da nakasa mai tsanani kuma suna da matsalar sadarwa.
An kuma ruwaito cewa wasu daga cikinsu kan bayar da amsoshin da ba su da alaƙa da tambayoyin da aka yi musu, yayin da wasu ba su ba da wata amsa ba.
Bayan wannan lamari, an nemi a rufe cibiyar Saekdongwon.

Asalin hoton, SADD TV
Kim bai ce komai kan zarge-zargen cewa ya ci zarafin mutane da dama a cibiyar ba.
Jun Ji-soo, babban malami kuma jagoran tawagar bincike daga Jami'ar Woosuk, ya shaida wa BBC cewa masu binciken sun "karɓi bayanai ne kawai daga mutanen da za su iya bayyana abin da ya faru da su."
Sai dai masu fafutukar kare haƙƙin masu buƙata sun ce dogaro da shaidun kaɗai ya sa 'yan sanda suka kasa gano wasu waɗanda abin ya shafa, musamman mazauna cibiyar da ke da matsalar sadarwa.
"Idan waɗanda aka ci zarafinsu suna bayyana abin da ya same su ta hanyar da ta bambanta da yadda muke tsammani, bai kamata gwamnati ta ƙara ƙoƙari domin tabbatar da cewa an saurari muryoyinsu ba?" in ji Baek In-seong na Cibiyar Ba da Shawara ta Han Sahoe ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima'i masu nakasa.
A martaninsu, 'yan sanda sun ce:
"Ko da yake ana iya samun kura-kurai a wasu lokuta, bai kamata a ɗora su a kan dukkan tsarin binciken baki ɗaya ba."
Ƙungiyoyin kare haƙƙin masu buƙata ta musamman sun kuma soki masu neman a sassauta wa Kim hukunci.
Public reaction and protests

Asalin hoton, Getty Images
"Muna so mu mu yi rayuwa cikin zaman lafiya"
Tun bayan da aka gano wannan lamari, Firaministan Koriya ta Kudu ya ba da umarnin kafa wata tawagar gaggawa da ta ƙunshi hukumomin gwamnati daban-daban domin mayar da martani, yana mai bayyana lamarin a matsayin:
"Wani mummunan lamari da ke jefa tambaya kan ainihin manufar wanzuwar gwamnati."
A watan Afrilun 2026, gwamnati ta sanar da cewa ta gudanar da bincike a cibiyoyin kula da masu buƙata ta musamman 1,507 a fadin ƙasar, inda ta gano zarge-zargen cin zarafi guda 33. Zuwa yanzu, an fara bincike a kan guda takwas daga cikin waɗannan lokuta.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za ta ƙarfafa bincike na musamman bisa la'akari da matakin haɗari, tare da gudanar da binciken haɗin gwiwa wanda zai haɗa da hukumomin yankuna, 'yan sanda da kungiyoyin kare haƙƙin masu buƙata ta musamman.
Hukumomin yankin Ganghwa sun ba da umarnin rufe cibiyar Saekdongwon, yayin da gwamnatin yankin ta soke lasisin cibiyar da ke tafiyar da ita.
Sai dai har yanzu ba a rufe cibiyar gaba ɗaya ba, saboda ana jiran a mayar da mutanen da har yanzu suke zaune a wurin zuwa wasu wurare da suka dace tare da kammala shirye-shiryen gudanar da rayuwarsu ta cin gashin kai.
Mahukuntan yankin sun sanar da cewa za su samar da wani shiri na musamman ga kowane mutum cikin mutum 33 da ke zaune a Saekdongwon domin taimaka musu tafiyar da rayuwarsu. Har yanzu ana ci gaba da wannan tsari.
Saekdongwon ta shigar da ƙara a gaban hukumomin gudanarwa domin dakatar da matakin soke lasisinta.
A halin yanzu, cibiyar ba ta fitar da wata sanarwa game da hukuncin da aka yanke wa Kim ba.
Da aka tambayi Su abin da ya fi canzawa a rayuwarta tun bayan da ta bar Saekdongwon, sai ta ce:
"Ina jin natsuwa. Ina farin ciki kowace rana."
Ta kuma ce abin da ta fi so a sabuwar rayuwarta shi ne cewa tana iya cin abinci da yin barci a duk lokacin da take so.
Ta bayyana cewa babban burinta yanzu shi ne:
"In yanke duk wata alaƙa da daraktan cibiyar gaba ɗaya, kuma kada in sake samun wata hulɗa da shi har abada."
Sai dai ta ƙara da cewa har yanzu mutane masu buƙata ta musamman suna buƙatar wuraren da za su ji suna cikin aminci.
"Ina fatan a samu cibiyoyin da ba a samun matsalar cin zarafi ta hanyar lalata, kuma ta masu buƙata ta musamman su sami damar rayuwa cikin zaman lafiya."





























