Wasanni 4 da za su yi zafi a gasar Champions League ranar Laraba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muhammad Abdu
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Za a ci gaba da wasanni na bibiyu a cikin rukuni a gasar Champions League da za a yi karawa tara a filaye da dama a fadin nahiyar Turai ranar Laraba.
Daga cikin karawar da akwai wadanda za su ja hankalin masu ruwa da tsaki, daga ciki akwai karawar da Roma za ta karbi bakuncin Real Madrid a Italiya.
A wasan farko a cikin rukuni Roma ta je ta tashi 1-1 a gidan Fenerbahce, yayin da Real Madrid ta doke Inter Milan 2-1 a Sifaniya.
Haka kuma akwai babbar karawar da Paris St Germain za ta ziyarci Manchester City a Etihad, City zuwa ta yi Portugal ta doke Porto 2-0 a wasan farko, yayin da PSG ta dura 6-1 a ragar Bratislava a Faransa.
Wasannin da za a buga ranar Laraba:
- Feyenoord vs Como
- LASK vs Liverpool
- Roma vs Real Madrid
- Aston Villa vs Fenerbahçe
- Shakhtar Donetsk vs AEK Athens
- Bodø/Glimt vs Borussia Dortmund
- Manchester City vs Paris Saint-Germain
- Real Betis vs Porto
- Slovan Bratislava vs Stuttgart
Ga jerin wasannin da za su ja hankalin masu ruwa da tsaki a tamaula
1. Man City da PSG

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ce ke kan gaba a nasara a tarihin haduwar kungiyoyin biyu, inda ta ci wasa hudu, yayin da Paris St Germain ta samu nasara biyu, sannan aka yi kunnen doki sau biyu.
Sai dai PSG ta yi nasara a haduwarsu ta baya-bayan nan da ci 4-2 a gida a gasar Champions League ta kakar 2024/25.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Erling Haaland ya ci kwallaye 59 a wasanni 59 da ya buga a gasar Champions League. Idan ya ci kwallo a wannan karawar, zai karya tarihin mafi yawan cin kwallaye a wasa na 60 a Champions League, tarihin da Ruud van Nistelrooy ke rike da shi mai kwallaye 48.
Haka kuma, Haaland a halin yanzu yana kan-kan-kan da Sergio Agüero a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallaye a Champions League a tarihin City, inda dukkansu ke da 36 a raga.
Mai tsaron gida na masu masaukin baki, Gianluigi Donnarumma, ya buga wasa 161 a Paris tsakanin 2021 zuwa 2025, inda ya lashe kofunan Faransa hudu da kuma gasar Champions League a 2025.
City ta yi rashin nasara sau daya kacal a cikin wasa 25 na baya-bayan nan da ta karbi bakunci a matakin rukuni, wadda ta lashe karawa 21 da yin canjaras uku aka doke ta uku daga ciki.
Sabon dan wasan da PSG ta dauka a lokacin bazara, Ferran Torres, ya ci kwallo 16 a wasa 43 da ya buga wa City tsakanin 2020 zuwa 2022, inda ya lashe Premier League da kuma League Cup.
Ousmane Dembélé ya zura kwallo a wasa biyar a jere da ya buga a Champions League, inda ya ci jimillar takwas a cikin wadannan wasannin.
PSG ba ta yi rashin nasara ba a wasa 11 na baya-bayan nan da ta buga a gasar UEFA da kungiyoyin Ingila, inda ta ci takwas da yin canjaras uku.
Wasa tsakanin Manchester City da Paris St Germain
2024/2025
Champions League Laraba 22 Janairu 2025
PSG 4 - 2 Man City
2021/2022
Champions League Laraba 24 Nuwamba 2021
Man City 2 - 1 PSG
Champions League Talata 28 Satumba 2021
PSG 2 - 0 Man City
2020/2021
Champions League Talata 04 Mayu 2021
Man City 2 - 0 PSG
Champions League Laraba 28 ga watan Afirilu 2021
PSG 1 - 2 Man City
2015/2016
Champions League Talata 12 ga watan Afirilu 2016
Man City 1 - 0 PSG
Champions League Laraba 06 Afirilu 2016
PSG 2 - 2 Man City
2008/2009
UEFA Cup Laraba 03 Disamba 2008
Man City 0 - 0 PSG
2. LASK za ta karbi baƙuncin Liverpool
Wannan shi ne wasa na uku da za a fafata tsakanin kungiyoyon a gasar zakarun Turai, kuma kungiyar Anfield ce ta yi nasara a dukkan karawar biyu.
LASK ba ta taba samun nasara ba a wasa shida da ta buga da kungiyoyin Ingila daga ciki wasa daya canjaras aka doke ta karawa biyar.
LASK ba ta samu nasara ba a wasanninta tara na baya-bayan nan a matakin rukuni a gasar Turai, inda tasha kashi karo shida da canjaras uku.
Dan wasan tsakiyar Liverpool, Dominik Szoboszlai, ya fuskanci LASK sau biyar lokacin yana tare da tsohuwar kungiyarsa Salzburg, inda aka ci wasa hudu da shi a cikin fili da rashin nasara daya. A wasanni ukun farko daga ciki ya ci kwallo biyu ya bayar da hudu aka zura a raga.
Cody Gakpo ya ci kwallo biyu lokacin da Liverpool ta doke LASK da ci 4-0 a matakin rukuni a UEFA Europa League na kakar 2023/24.
Liverpool ta yi nasara a wasa takwas daga cikin goma da ta buga da kungiyoyin Austria da yin rashin nasara daya, kuma ba ta taba shan kashi ba a wasannin waje, inda ta ci hudu da canjaras daya.
Liverpool ta yi nasara a wasa 19 daga cikin 22 na baya-bayan nan da ta buga a matakin rukuni a gasar Champions League aka doke ta uku daga ciki.
Wasan da aka buga tsakanin LASK da Liverpool:
2023/2024
Europa League Alhamis 30 ga watan Nuwamba 2023
Liverpool 4 - 0 LASK Linz
Europa League Alhamis 21Sep 2023
LASK Linz 1 - 3 Liverpool
3. Real Madrid za ta ziyarci Roma a Italiya

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin biyu sun hadu sau 12, inda Madrid ke kan gaba a tarihin wasannin da nasara takwas, yayin da Roma ta ci wasa uku, sannan aka yi canjaras daya.
Kungiyar ta Spain ta lashe haduwarsu hudu na baya-bayan nan ba tare da an zura mata kwallo ba a raga, sannan ta kuma yi nasara a karawa biyar daga cikin shida da suka buga a birnin Rum aka doke ta wasa daya.
Paulo Dybala da Donyell Malen sun taba yin rashin nasara a wasan karshe a Champions League a hannun Madrid. A lokacin Dybala yana taka leda a Juventus a 2017, yayin da Malen yake tare da Borussia Dortmund a 2024.
Roma ta yi nasara a wasa takwas daga cikin tara na baya-bayan nan da ta karbi bakuncinta a gasar Champions League aka doke ta daya daga ciki.
Kylian Mbappe mai shekara 27 da kwana 298, ya ci kwallo 99 a gasar ta zakarun Turai, zai iya zama dan wasa mafi karancin shekaru da zai ci 100 a Champions League, inda zai karya tarihin Lionel Messi, wanda ya kai wannan matsayi yana da shekara 28 da kwanaki 84.
Kocin Madrid, José Mourinho, shi ne ya horar da Roma daga 2021 zuwa 2024, inda ya jagorance ta zuwa lashe kofin UEFA Conference League a kakar 2021/22, sannan ya kai ta wasan karshe na Europa League a kakar da ta biyo baya.
Mai tsaron bayan Madrid, Dean Huijsen, ya buga wasa 14 a Roma lokacin da aka karbo shi aro daga Juventus a 2024, yayin da Antonio Rüdiger ya buga wasa 72 a kungiyar Giallorossi tsakanin 2015 da 2017.
Kungiyar Sifaniya ta yi nasara a wasa 20 daga cikin 22 na baya-bayan nan da ta buga da kungiyoyin Italiya aka doke biyu daga ciki.
Ga jerin wasannin da aka buga tsakanin Roma da Real Madrid:
2018/2019
Champions League Talata 27 Nuwamba 2018
Roma 0 - 2 Real Madrid
Champions League Laraba 19 Satumba 2018
Real Madrid 3 - 0 Roma
2015/2016
Champions League Talata 08 Maris 2016
Real Madrid 2 - 0 Roma
Champions League Laraba 17 Fabrairu 2016
Roma 0 - 2 Real Madrid
2007/2008
Champions League Laraba 05 Maris 2008
Real Madrid 1 - 2 Roma
Champions League Talata 19 Fabrairu 2008
Roma 2 - 1 Real Madrid
2004/2005
Champions League Laraba 08 Disamba 2004
Roma 0 - 3 Real Madrid
Champions League Tatata 28 Satumba 2004
Real Madrid 4 - 2 Roma
2002/2003
Champions League Laraba 30 Oktoba 2002
Real Madrid 0 - 1 Roma
Champions League Talata 17 Satumba 2002
Roma 0 - 3 Real Madrid
2001/2002
Champions League Laraba 24 Oktoba 2001
Real Madrid 1 - 1 Roma
Champions League Talata 11 Satumba 2001
Roma 1 - 2 Real Madrid
4. Fafatawa tsakanin Real Betis da Porto
Wasanni 48 na baya-bayan nan da Real Betis ta buga a gasar UEFA, guda ɗaya kacal ne ya ƙare babu ci (0-0), yayin da babu ko wasa ɗaya cikin 31 na baya-bayan nan da Porto ta buga a Turai da ya ƙare 0-0.
Tarihin a kan wasan Betis tsakanin kungiyoyin Portugal shi ne: ta yi nasara uku aka doke ta da canjaras biyu.
Masu masaukin baki sun yi rashin nasara sau ɗaya kacal a wasa 11 na baya-bayan nan da ta buga a matakin rukuni a gasar UEFA, wadda ta yi nasara takwas da canjaras biyu).
Betis ta ci ƙwallaye biyu ko fiye a kowanne daga cikin wasanninta tara na baya-bayan nan a gida a gasar Turai.
Porto ta yi rashin nasara a wasa huɗu daga cikin biyar na baya-bayan nan da ta buga da kungiyoyin Sifaniya da cin karawa daya.
Porto ta shiga zagaye na biyu wato sauran minti 45 a gasar zakarun ana zura mata kwallo ko kwallaye sau uku kacal a cikin wasa 15 na baya-bayan nan a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
































