BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Amurka ta ƙaryata cewa sojojinta na cikin yunwa a Gabas ta Tsakiya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 13/08/2026
Wane babban ɗan wasa Arsenal za ta saya bayan gaza ɗaukar Vinicius Jr?
Ƙungiyar Arsenal ta gaza cimma burinta na ɗauko ɗan wasan gefe na Real Madrid kuma ɗan ƙasar Brazil, Vinicius Junior, duk da ƙoƙarin da ta yi wanda ya ja hankalin duniya sosai.
Sarautu biyar waɗanda asalinsu na bayi ne a wasu masarautun ƙasar Hausa
Bayin Sarki sun samo asali ne tun a lokacin mulkin Haɓe ko Hausawa kuma tun asali ba su da wani matsayi baya ga bauta.
Yadda Najeriya da Afirka ta Kudu za su fafata wasan neman gurbin zuwa gasar kofin duniya
Najeriya ta rasa damar samun tikitin shiga gasar kai-tsaye bayan rashin nasara a wasan kwata-fainal, inda Kamaru ta doke ta ci 1 mai ban haushi.
Me ya kamata a yi idan mutum ya yanke jiki ya faɗi?
Chinedu Ozor, matashin ɗan wasan baya mai shekara 18 da Katsina United ta ɗauka a kwanakin baya, ya faɗi a fili yayin wasan da ƙungiyar ta kara da Niger Tornadoes a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Tsawon wane lokaci Iran za ta iya ɗauka tana yaƙi?
Wata bakwai bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Iran da Amurka, kuma duk da matsin tattalin arziƙi da na ababen more rayuwa kan ƙasar, alamu sun nuna cewa har yanzu mahukuntan ƙasar ba su matsu a kawo ƙarshen yaƙin ba.
Abu 3 da Kudu maso Yammacin Najeriya ke la'akari da su wajen zaɓen shugaban ƙasa
Kudu maso Yamma, yanki ne da ke da muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, musamman idan aka zo zaɓen shugaban ƙasa.
Sabuwar dokar noma da aka saka a arewacin Najeriya saboda ƴanbindiga
Matsalar tsaron ta tilasta ɗaukar matakai da dama kuma ɗaya daga cikin matakin shi ne haramta wa manoma shuka duk wani amfanin gona mai tsayi a hanyar Zaria zuwa Sokoto
A shirye muke mu ɗauki tsawon lokaci muna yaƙi - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 12 ga watan Agustan 2026.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 14 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 13 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 13 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 13 Agusta 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Messi ya buga wa Inter Miami wasa bayan mutuwar mahaifinsa
Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 10 - 16 Agusta 2026.
Galatasaray ta taya Martinelli, ina Zubimendi zai tafi?
Galatasaray ta taya ɗanwasan Arsenal Gabriel Martinelli, haka ma ɗanwasan tsakiya na Spain Martin Zubimendi zai iya barin Gunners zuwa Chelsea, yayin da Newcastle ta nace wa ɗanwasan baya na Benfica Amar Dedic.
Yadda aka yi bikin Ronaldo da amaryarsa Georgina a Portugal
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo ya auri abokiyar zamansa ta shekaru da dama, Georgina Rodríguez, wadda ta yi suna a matsayin abin koyi da kuma mai tasiri a shafukan sada zumunta, a wani bikin auren kotu da aka gudanar a Portugal.
Man Utd na son Endrick, Napoli na harin Gabriel Jesus
Coventry City na son karɓo aron ɗanwasan gaba na Chelsea Mykhaylo Mudryk, Barcelona za ta ci gaba da farautar ɗanwasan tsakiya na Manchester City Rodri yayin da Manchester United ke son ɗauko ɗanwasan gaba na Real Madrid Endrick.
Man City ta kusa mallakar Bouaddi, Madrid na son Zubimendi
Manchester City na dab da ɗaukar Ayyoub Bouaddi, Real Madrid na son Martin Zubimendi, yayin da Barcelona da Tottenham ke bibiyar Harry Kane.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Dabbobi 10 mafiya muni a duniya
Kallon dabbobi musamman ma na daji abu ne mai samar da nishaɗi da ban-sha'awa, wanda hakan ya sa masu hali kan shiga dazuka domin kallon su da irin ɗabi'unsu, sai dai ba kowace dabba ce take da daɗin kallo ba.
Muhimman abubuwa 5 kan zaɓen gwamnan jihar Osun
Wannan shi ne karo na bakwai da za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
Dabaru 3 na samun aiki mai maiƙo ba tare da alfarma ba
Tun bayan da labaran wasu ƴan biyu kuma ƴan gida ɗaya da suka samu aiki a kamfanin mai na Najeriya, NNPC ba tare da sani kowa ba ko kuma wani ya yi musu alfarma ba, ƴan Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu tare da bayyana mamakinsu kan faruwar hakan.
Matakan soji uku da Amurka ta ɗauka waɗanda suka girgiza duniya
A tsawon shekaru Amurka ta jagoranci wasu matakan soji da suka kai ga kamawa da kisan jagororin wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da kuma shugabannin ƙasashen da ake zargi da aikata miyagun laifuka.
Manyan dazukan Najeriya 6 da suka zama mafakar ƴanbindiga
Yayin da gwamnati da hukumomin tsaro ke ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu aikata laifuka daga irin waɗannan wurare, har yanzu akwai wasu dazuka da ke ci gaba da zama sanannun mafaka ga ƙungiyoyin ƴanbindiga da sauran masu ɗauke da makamai.
Dalilan da suka sa na nace kan takarar Muslim-Muslim - Sheikh Jingir
Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi ƙarin haske kan matsayinsa da kalaman da ya yi game da tikitin takarar Musulmi da Musulmi.
G-100: Sabuwar haɗakar da ke da nufin kawar da Tinubu daga mulki
A baya-bayan nan yunƙurin da ƴan hamayya suka yi na haɗewa a jam'iyya ɗaya domin tunkarar babban zaɓen 2027 ya ci tura, inda ba tare da daɗewa ba suka sake tarwatsewa zuwa cikin wasu jam'iyyun daban-daban.
Hanyoyi uku da Amurka za ta iya tsoma baki a zaɓen Najeriya
A wasu lokuta, jami'an Amurka kan bayyana matsayarsu kan zaɓen wata ƙasa, su yi kira ga gwamnati da ƴan siyasa su mutunta dimokuraɗiyya, ko kuma su yi amfani da takunkumi kan waɗanda ake zargi da take haƙƙin ɗan'Adam ko lalata tsarin zaɓe.
Yadda aka ɓoye Trump a akwatin abincin jirgin sama saboda tsoron Iran
Kafafen yada labaran Amurka sun ce an dauke shugaban Amurka daga tsohon Air Force One zuwa jirgin soja yayin da yake barin taron kungiyar tsaro ta NATO a Turkiyya a watan da ya gabata.
An yanke wa tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad hukuncin kisa
Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa Assad, wanda ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa bayan an hamɓarar da gwamnatinsa a watan Disamban 2024.
Auren gata a Kano: Ƙalubalen da ake fuskanta wajen tantance masoyan gaskiya da na bogi
Tsawon kwanaki, titunan birnin sun cika da hayaniyar shagulgula, inda amare da danginsu ke shirya kayayyakin aure tare da halartar wasu tarurruka da shirye-shirye da aka tanada musu.
Ko Najeriya na da damar zuwa Gasar Kofin Duniya ta mata bayan shan kashi?
Shan kashi da Najeriya ta yi a hannun tawagar mata ta Kamaru ya ɗasa shakku kan damar da Najeriyar ke da ita ta zuwa Gasar Kofin Duniya ta Mata da za a yi a 2027 a ƙasar Brazil.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































