Maharan sun kashe mutane biyar a wajen haƙar ma'adinai a Filato

Asalin hoton, Facebook
An kashe masu aikin haƙar ma'adinai biyar tare da jikkata wasu biyu a ranar 26 ga Satumba, bayan da wasu mahara suka kai hari wani wurin haƙar ma'adinai a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Marit da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi, inda tattalin arzikin al'ummar yankin ya dogara sosai kan aikin haƙar tin.
Harin ya ƙara jawo damuwa kan tsaron mazauna yankin da masu aikin haƙar ma'adinan da ke gudanar da ayyukansu a yankin.
Harin ya faru ne kwana uku bayan da aka kashe wasu masu aikin haƙar ma'adinai uku a yankin Gangare da ke Barkin Ladi.
Mai magana da yawun ƙungiyar Berom Youth Moulders Association ta yankin, Rwang Tengwong, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kare al'ummomi tare da hana sake aukuwar hare-haren bayan sabon harin na baya-bayan nan.
Wani mazaunin yankin, Simon Mundat, ya kuma yi kira ga hukumomi da su "ƙarfafa tsaro a yankin domin jama'armu su iya gudanar da ayyukansu na halal ba tare da tsoro ba."
A ranar 21 ga Satumba, Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanya dokar hana fita da dare ba tare da ƙayyade ranar kawo ƙarshenta ba a ƙananan hukumomi uku, ciki har da Barkin Ladi, domin "kula da zaman lafiyar jama'a da dakile barazanar tsaro da ke kunno kai", bayan wasu hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane.
















