Me ya sa Ingila ba ta cika samun nasara a kan manyan ƙasashe ba?

.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A yayin da Ingila za ta kara da Spain a filin wasa na Wembley a wasan farko na Nations League, magoya bayan Three Lions za su ƙara damuwa da tuna wani irin kayi da suka sha sau da dama.

Wannan wasa na zuwa ne watanni uku bayan Ingila ta rasa damar buga wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya cikin raɗaɗi, bayan Argentina ta fitar da ita daga gasar a wasan kusa da na ƙarshe.

Da Ingila ta doke Argentina, da ta buga wasan ƙarshe na Kofin Duniya da Spain, wanda da ya kasance maimaita wasan Euro 2024 inda Ingila ta doke Spain.

Matsalar Ingila ita ce idan ana maganar wasanni da ƙasashen da ke cikin goma na farko a jadawalin FIFA, tarihinsu bai da kyau.

A wasanni 15 na baya-bayan nan da suka buga da ƙasashen da ke cikin goma na farko a duniya, Ingila ta yi nasara shida kacal.

Uku daga cikin waɗannan nasarori shida sun zo ne a manyan gasa.

Sun doke Denmark a wasan kusa da na ƙarshe na Euro 2021, Netherlands a irin wannan mataki na Euro 2024, sannan suka doke Faransa a wasan neman matsayi na uku a Kofin Duniya na wannan bazarar.

Nasarar da suka yi kan Faransa a wasan neman matsayi na uku ita ce nasara ta farko da Thomas Tuchel ya samu kan ƙasa da ke cikin goma na farko a duniya tun bayan da ya zama kocin Ingila.

Har ila yau, nasararta ta farko kan ƙasa da ke cikin ashirin na farko ta zo ne a wasan farko na rukuni a Kofin Duniya, lokacin da Ingila ta doke Croatia.

Me alkaluma ke cewa?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Nasarori shida kacal daga wasanni 15 da aka buga da ƙasashen da ke cikin goma na farko ba tarihi ba ne mai kyau ga ƙungiyar da ke son lashe manyan gasa.

Biyu daga cikin waɗannan nasarorin sun kai Ingila wasan ƙarshe na Euro 2020 da Euro 2024.

Wata nasarar kuma ta zo ne a wasan neman matsayi na uku a Kofin Duniya, yayin da biyu suka zo a wasannin neman gurbin Euro da Italiya, wadda ita ma tana cikin wani yanayi na rashin ƙarfi.

Sauran nasarar ta zo ne kan Belgium a Nations League shekaru shida da suka gabata.

Idan aka kalli wasanni da manyan ƙasashe musamman, alkaluma sun nuna cewa Ingila na fama da wahalar doke ƙungiyoyi masu irin wannan ƙarfi, musamman a Kofin Duniya.

Tun daga 1998, an fitar da Ingila daga dukkan wasannin Kofin Duniya guda bakwai da ta buga da ƙasashen da ke cikin goma na farko a jadawalin FIFA.

A wasanni 10 na baya-bayan nan da Ingila ta buga a Kofin Duniya da ƙasashen da ke cikin goma na farko, ta yi nasara sau ɗaya kacal.

Hakan ya faru ne a matakin rukuni na Kofin Duniya na 2002 lokacin da ta doke Argentina.

Haka kuma, duk lokacin da Ingila ta fuskanci zakarun da ke riƙe da kofi a Kofin Duniya, ta sha kashi a dukkan wasanni huɗu:

• 1954: Uruguay 4-2 Ingila

• 1962: Brazil 3-1 Ingila

• 2022: Ingila 1-2 Faransa

• 2026: Ingila 1-2 Argentina

A gasannin Turai kuwa, Ingila na da tarihi mafi kyau idan aka kwatanta da ƙasashen da ke sama da ita a matsayi.

Ta doke Denmark da Netherlands a wasannin kusa da na ƙarshe na Euro 2021 da Euro 2024, wanda ya taimaka mata zuwa wasan ƙarshe a lokutan biyu.

Sai dai duka wasannin ƙarshe sun ƙare da shan kashi.

Italiya ce ta lashe Euro 2020, yayin da Spain ta lashe Euro 2024.

Wani abu da alkaluman suka nuna shi ne batun mallakar ƙwallo.

A wasanni 15 na baya-bayan nan da Ingila ta buga da ƙasashen da ke cikin goma na farko, mafi ƙarancin mallakar ƙwallon da ta yi shi ne kashi 35.8 cikin 100 a wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Duniya da Argentina.

Haka nan Ingila ta mallaki ƙwallo da kashi 34.9 cikin 100 a wasan ƙarshe na Euro 2024 da Spain, yayin da ta mallaki kashi 42.1 cikin 100 a wasan ƙarshe na Euro 2020 da Italiya.

"Muna bukatar mu yarda da juna"

Harry Kane, wanda shi ne kan gaba wajen zura ƙwallaye a tarihin Ingila da ƙwallaye 85, an tambaye shi dalilin da ya sa yake ganin Ingila ba ta yawan yin nasara a manyan wasanni da kuma abin da za ta iya yi don shawo kan ƙalubalen.

"Ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne a kasance da kwarin gwiwa a manyan lokuta," Kane ya shaida wa BBC Radio 5 Live.

"Yana da matuƙar wuya a karɓi sakamakon wasan Argentina, saboda muna da burin lashe gasar, tare da yin nasara ta salonmu da hanyar wasanmu.

Da mun yi hakan muka sha kashi, da mun amince da hakan."

"Amma wasan Argentina shi ne wataƙila karo na farko a cikin lokaci mai tsawo da muka shafe mintuna 30 na ƙarshe muna ƙoƙarin guje wa shan kashi, kuma a ƙarshe ma har yanzu mun sha kashin."

Kane, wanda ya zura ƙwallaye 152 a wasanni 154 da ya buga wa Bayern Munich kuma ya lashe kambunan Bundesliga biyu, ya yi amfani da gogewarsa a ƙungiyar Jamus da yake bugawa a yanzu.

"Na koyi haka daga Bayern Munich, misali. A nan ba mu jin tsoron kowace ƙungiya," in ji ɗan wasan Ingila mai shekara 33.

"Mun kusan kai wa ga nasara sosai, kuma sau da yawa mun kusanci hakan. Amma a ƙarshe, babu wanda ya kamata mu ji tsoro."

"Abin da kawai muke bukata shi ne mu kasance yadda muke a manyan lokuta, kuma muna fatan a ƙarshe za mu shawo kan wannan cikas."