Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 26/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. An sake gano gawar mace a Afirka ta Kudu

    ’Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce sun sake gano gawar wata mace a gundumar Ekurhuleni, lamarin da ya kai adadin gawarwakin matan da aka gano a yankin cikin watanni biyu da suka gabata zuwa 10.

    An gano gawar a garin Tembisa, amma ba a bayar da ƙarin bayani game da lamarin ba.

    A farkon wannan mako, daruruwan mutane sun halarci jana’izar Elizabeth Mose-lakgoomo, ɗaya daga cikin mata tara da ake binciken mutuwarsu a gundumar.

    Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen duniya da ke fama da matsalar cin zarafin mata sosai.

  2. Mutane 11 sun mutu a harin bam a Pakistan

    ...

    Ƴansanda a Pakistan sun ce aƙalla mutane 11, ciki har da jami’an tsaro, sun mutu sannan wasu 30 suka jikkata a wani harin bam a gundumar Dera Ismail Khan, da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Sun ce wata mota da aka loda da abubuwan fashewa ta kutsa shingen binciken jami’an tsaro, inda ta yi sanadin mutuwar mutane 11, ciki har da mata biyu da yaro guda.

    Kawo yanzu, babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

    A baya dai, mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Taliban sun sha kai irin waɗannan hare-haren bam kan jami’an tsaron Pakistan.

  3. Iran ta sake yi wa Amurka gargaɗi

    Mojtaba Khamenei

    Babban Kwamandan Sojin Iran, Khatam al-Anbiya, ya yi gargaɗin cewa idan Amurka ta ɗauki matakin da ya kira na kuskure kan Iran, za ta kai hari kan dukkan sansanonin sojin Amurka, dakarunta da ke yankin.

    Kamfanin Dillancin Labaran Mehr na Iran ya ruwaito cewa gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da Tehran ke jiran martanin Washington kan sabon yunƙurin sake buɗe Mashigin Hormuz.

    Iran ta ce ba ita ce za ta fara yaƙi ba, amma a shirye take ta kare tsaronta da kuma ikon mallakarta idan maƙiyanta suka kawo mata hari.

  4. ’A shirye Rasha take ta taimaka a kawo ƙarshen rikicin Mashigin Hormuz’

    Putin

    Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce ƙasarsa a shirye take ta taimaka wajen kawo daidaito a Mashigin Hormuz da yankin Tekun Farisa.

    Lavrov ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga shugabannin ƙasashen duniya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Asabar.

    Ya ce ana buƙatar samun amincewar juna tsakanin ƙasashen yankin Tekun Farisa, ƙasashen Larabawa da Iran, tare da samar da ingantaccen tsarin tsaro na yankin.

    Ministan ya ce Rasha, tare da sauran ƙasashen da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya, a shirye take ta bayar da gudunmawa wajen samar da kwanciyar hankali a yankin da ke da matuƙar muhimmanci ga harkokin duniya.

  5. An kwaso wasu ƴan Najeriya 105 daga Afirka ta Kudu

    An kwaso wasu ƴan Najeriya 105 daga Afirka ta Kudu

    An sake kwaso wasu ƴan Najeriya 105 daga Afirka ta Kudu, sakamakon hare-haren ƙyamar baki da ake kai wa ƴan kasashen Afirka.

    Daga cikin akwai mutum 82 da yara 23, kuma sun koma Najeriya ne a ranar Alhamis, inda jami’an gwamnati suka tarbe su.

    A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta wallafa a shafin X ranar Asabar, ta ce Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ce ta dauki nauyin dawo da 100 daga cikin mutanen.

    Ta ce cocin ta bayar da sama da dala 265,854 domin sayen tikitin jirgi, domin kwashe ’yan Najeriya 500 da ke cikin mawuyacin hali daga Afirka ta Kudu.

    Ma’aikatar ta ce sai kuma wani ɗan Najeriya ne ya dauki nauyin dawo da sauran mutane biyar.

    ’Yan Najeriyar 105 sun iso filin jirgin saman Legas ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a jirgin South African Airways.

  6. Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara ganin amfanin gyare-gyaren da Tinubu ke yi

    Mohammed Idris

    Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya ce Najeriya ta fara ganin amfanin wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar.

    Ya bayyana haka ne a Abuja yayin wani taron da aka shirya domin cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya.

    Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta karɓi ragamar mulki ne a cikin yanayi mai cike da ƙalubalen tattalin arziki da kuɗaɗe, amma ta ɗauki matakin tunkarar matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar.

    "A yanzu Najeriya tana matsawa daga matakin gyare-gyare da daidaita tattalin arziki zuwa ci gaba, samar da kayayyaki da faɗaɗa tattalin arziki," in ji shi.

    Mohammed Idris ya ce mataki na gaba shi ne tabbatar da cewa waɗannan sauye-sauyen sun haifar da ƙarin ayyukan yi, kuɗin shiga, tare da rage tsadar rayuwa.

    Ya ce gwamnati na mayar da hankali kan fannoni kamar ababen more rayuwa, noma, ilimi, makamashi da bunƙasa sana'o'i.

    Ministan ya ce manufar gwamnatin ita ce Najeriya ta ƙara samar da abubuwan da take amfani da su a cikin gida, ta sarrafa albarkatun da take haƙowa, tare da amfani da yawan jama'a da albarkatun ƙasar wajen samar da damarmaki.

  7. Trump ya yi watsi da shirin Iran na buɗe Mashigin Hormuz cikin gaggawa

    Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi watsi da shawarar da Iran ta gabatar na buɗe mashigin Hormuz cikin gaggawa.

    A hirarsa da manema labarai, ya ce Iran na fuskantar matsananciyar matsala, kuma hakan ne ya sa take son cimma yarjejeniya domin buɗe mashigin Hormuz nan take.

    “Na yi watsi da shawararsu,” in ji Trump.

    Trump ya sake nanata cewa Amurka ce ke da cikakken iko a kan mashigin Hormuz, yana mai cewa ƙasarsa na samun gagarumar nasara.

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa shi ma, kamar jami’an Iran, yana son a cimma yarjejeniya. Sai dai ya jaddada cewa ba zai amince da shawarwarin Iran ba.

  8. Isra'ila ta kai hare-haren bama-bamai a Lebanon

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar Lebanon sun ce sojojin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu yankuna da ke kudancin ƙasar, ciki har da yankunan Mansouri da Majdal Zoun da ke gundumar Tyre.

    Rahotanni sun ce an kuma harba makamai masu linzami zuwa Wadi Hassan, wani kwari da ke bayan garin Majdal Zoun, yayin da wasu hare-haren suka sauka a yankunan Barashit da Hadata da ke gundumar Bint Jbeil a jihar Nabatieh da tsakar dare.

    Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da aka ga jiragen yaƙin Isra'ila suna shawagi a ƙananan tsayi a sararin samaniyar birnin Tyre da ƙauyukan da ke kewaye da shi.

  9. Fafaroma ya jagoranci ibada ta musamman a Faransa

    Pope

    Fafaroma Leo ya gudanar da ibada ta musamma a dandalin Place de la Concorde, inda ya jagoranci dubban ɗaruruwan mutane wajen yin addu’a a wani gagarumin taron ibada da aka gudanar a fili. Fadar Vatican ta ce kimanin mutum 700,000 ne suka halarci taron.

    Fafaroman ya gaishe da masu ibadar, tare da yin tsokaci na musamman kan matasa, inda ya yaba da ƙwazonsu da kuma yadda suke bayar da gudummawa ga al’ummar Kiristoci.

    An fara ibadar ne bayan Fafaroma Leo ya bi titin Champs-Elysées a cikin mota buɗaɗɗiya ta sama, yana gaishe da jama’a.

    Ƴansiyasa da dama sun halarci taron, ciki har da shugabannin masu ra’ayin dama na jam’iyyar National Rally, Marine Le Pen da Jordan Bardella, da kuma tsohon shugaban ƙasar Faransa, Nicolas Sarkozy.

    Tun da farko, yayin da yake jawabi a wata cibiya da ke tallafa wa Ƴan ci-rani, Fafaroman ya ce akwai yiwuwar mutane su “zauna tare cikin mutunci da zaman lafiya”.

    Ya kuma yaba da rawar da mata ke takawa wajen gina abin da ya kira “son juna”, a madadin al’adar da ke raba al’umma.

  10. Fashewar bam ta yi ajalin aƙalla mutum 11 a Pakistan

    Ƴansanda a arewa maso yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 ne suka mutu, yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a yankin Dera Ismail Khan.

    Ƴansandan sun ce wata mota ɗauke da abubuwan fashewa ta yi karo da wata mashigar binciken jami’an tsaro.

    Daga cikin jami’an tsaron da aka kashe har da mata biyu da wani yaro. Ya zuwa yanzu, babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

    Mayaƙan Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) sun taɓa kai irin waɗannan hare-haren bam kan jami’an tsaro a baya.

    Lamarin ya faru ne kwana biyu bayan da Pakistan ta sanar da cewa ta kai hare-haren sama kan wasu mayaka da take zargi da ke Afghanistan, waɗanda ke kai hari kan dakarunta a yankunan da ke kan iyaka.

  11. 'Trump ya ƙi amincewa da tsarin tsagaita wuta na Iran'

    Trump

    Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi amincewa da tayin tsarin tsagaita wuta da Iran ta yi, kuma ana sa ran za a sake komawa kai hare-haren sama bayan zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na Amurka.

    Rahoton ya zo ne a yayin da jami’an Iran suka sanar da wani shirin kwana bakwai da suka gabatar wa Amurka, wanda ya ƙunshi sake buɗe mashigar Hormuz da kuma rage tashin hankali.

    A gefe guda kuma, wani jami’in Amurka ya ce tattaunawar da ake yi da Tehran ta hannun masu shiga tsakani tana tafiya cikin “kyakkyawan yanayi kuma da ma’ana.”

    A farkon wannan makon, a cikin jawabin da ya yi a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, Trump ya ce yana ganin za a iya cimma yarjejeniya da Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin mulkin Amurka. Sai dai a lokaci guda, ya kuma yi nuni da yiwuwar sake komawa matakin soji kan Iran.

  12. Pezeshkian ya ce ya gana da Mojtaba Khamenei sau biyu

    Iran

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya shaida wa gidan talabijin na CBS na Amurka cewa ya gana da Mojtaba Khamenei sau biyu cikin watanni bakwai tun bayan da ya hau kujerar shugaban ƙasa.

    Mista Pezeshkian ya ce: “A cikin sa’o’i bakwai da na yi tare da jagoran-juyin-juya-halin, bai nuna alamar wata illa ba. Mun zauna a ƙasa muna tattaunawa. Ba mu saba zama haka ba, amma shi ya zauna a wurinsa tsawon lokacin kuma jikinsa yana cikin ƙoshin lafiya har ya iya jure wannan yanayin.”

    An wallafa cikakken bayanin hirar a shafin yanar gizon fadar shugaban ƙasar Iran.

    Shugaban Iran ya ce Mojtaba Khamenei yana cikin “cikakkiyar ƙoshin lafiya ta fuskar lafiya”, sannan ya ƙara da cewa: “Ni likita ne, kuma daga bakina kuke jin wannan, ku yarda da shi; ba shi da wata matsala.”

    Tun bayan maye gurbin mahaifinsa, wanda aka ce an kashe shi a wani harin haɗin gwiwa da Isra’ila da Amurka suka kai a ranar 29 ga Maris, Mojtaba Khamenei bai sake fitowa bainar jama’a ba, kuma bai fitar da wani bidiyo ko sautin murya ba tun bayan zaɓensa a matsayin jagoran ƙasar.

    Da CBS ta tambaye shi ko lokacin da ya gana da Mojtaba Khamenei ya tambaye shi ko yana da izinin zuwa Amurka, Pezeshkian ya ce: “Kasancewarmu a Amurka ba lallai sai da izini ba. Mun sanar da shi cewa za mu zo, amma tafiye-tafiyenmu suna ƙarƙashin ikon gwamnati.”

  13. Za mu faɗaɗa kwamitin yaƙin zaɓenmu - ADC

    ADC

    Jam'iyyar ADC ta ce za ta ci gaba da yin ƙarin naɗe-naɗe da kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓe yayin da take shirye-shiryen zaɓen 2027.

    Ta ce jerin sunayen da aka fitar zuwa yanzu mataki ne na farko, kuma za a sanar da wasu manyan muƙamai da kwamitoci gudanarwa nan gaba.

    A wata sanarwa da Phrank Shuaibu ya fitar, ya ce za a kafa kwamitoci da tsari daga matakin shiyya da jiha har zuwa unguwanni da rumfunan zaɓe a faɗin Najeriya.

    Jam’iyyar ta ce za ta haɗa magoya bayanta, ƙwararru, shugabanni da matasa wajen gudanar da ayyukan siyasa da tsara manufofi.

    Manufofin da ake shiryawa sun haɗa da tsadar rayuwa, abinci, noma, tsaro, ayyukan yi, masana’antu, ilimi, lafiya da tattalin arziki, tare da ƙoƙarin samar da hanyoyin magance matsalolin ’yan Najeriya.

  14. Zamfara za ta sake buɗe makarantu bayan samun sauƙin cutar diphtheria

    Dauda Lawal

    Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce a ranar 25 ga Satumba cewa za a sake buɗe makarantu a ranar 28 ga Satumba, bayan samun sauƙi a halin da ake ciki game da cutar diphtheria, kamar yadda shafin yanar gizon Channels mai zaman kansa ya ruwaito.

    Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa dukkan makarantu da ke faɗin jihar za su koma ci gaba da karatun boko daga ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026, sakamakon samun sauƙi a yaɗuwar cutar diphtheria.

    Rahoton ya ce: “Umarnin ya shafi dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu, ciki har da cibiyoyin makarantun Islamiyya da Alƙur’ani da ke faɗin jihar.”

    A cewar shafin, ma’aikatar lafiya ta ba da shawarar sake buɗe makarantu tare da buƙatar al’umma su ci gaba da bin matakan kariya daga cutar.

    An kuma umarci makarantu da su hana duk mutumin da ke nuna alamun cutar diphtheria shiga makaranta.

    Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce ta samu rahoton sama da mutane 10,400 da suka kamu da cutar diphtheria, yayin da mutane 406 suka mutu tsakanin watan Janairu zuwa 9 ga Agusta 2026.

    Jaridar Cable mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 15 ga Satumba cewa aƙalla kashi 98 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi takwas, inda Kano ta kasance jihar da cutar ta fi kamari.

  15. Sojojin Mali sun ce sun kashe mayaƙa sama da 300

    Mali

    Sojojin Mali sun ce a ranar 25 ga Satumba sun kashe ɗaruruwan mayaƙa a wasu samame da suka gudanar a yankunan kudu maso yammaci da arewacin ƙasar, wato Dioila da Kidal.

    A wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na Facebook, sojojin sun ce:

    “Ranar 24 ga Satumba, mun samu sahihan bayanan sirri cewa mayaƙa tsakanin 200 zuwa 300 sun taru a arewacin Dandougou a yankin Dioila, inda suka kuma jibge manyan makamai da kayan yaƙi.”

    Sojojin sun ce bayan sun tabbatar da sahihancin bayanan, jiragen yaƙinsu sun kai hare-hare ta sama kan wuraren da mayaƙan suke, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da lalata kayan yaƙinsu.

    Sun ƙara da cewa an gudanar da wani samame a ranar 21 ga Satumba, gabashin birnin Kidal, inda aka kai hari kan wasu ƙungiyoyi biyu na mayaka ɗauke da manyan makamai.

    Sojojin sun ce ayyukan tsaro da sa ido na ci gaba da gudana a waɗannan yankuna, domin zaƙulo sauran mayaƙan da suka tsira da kuma kawar da barazanar da suke yi.

    A ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, hukumomi na ƙara fitar da bayanan da ke nuna nasara sosai a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

    Sai dai sau da yawa bayanan na saɓawa rahotannin majiyoyi masu zaman kansu da kuma labaran ƴan gudun hijira, waɗanda ke nuna cewa hare-hare da tashe-tashen hankula na ci gaba kuma babu alamar za su kawo ƙarshe nan kusa.

  16. Aƙalla mutum 14 sun rasu a hatsarin jirgin sama a Congo

    Jami'ai a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun bayyana cewa, wani ƙaramin jirgin sama da ke ɗauke da tawagar sojoji ya yi hatsari tare da kamawa da wuta a kusa da Kenge, babban birnin lardin Kwango da ke kudu maso gabashin kasar.

    Aƙalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu, ciki har da babban mai shigar da ƙara na rundunar sojin kasar.

    Har yanzu ba a san takamaiman abin da ya haddasa hatsarin ba, ko kuma ko idan akwai wadanda suka tsira da ransu.

  17. An yi kutsen intanet tare da sace bayanan jami'an FBI

    FBI

    Jami'an hukumar tsaro ta FBI na da na yanzu sun bayyana matuƙar damuwa game da tsaron lafiyarsu, bayan wani kutsen intanet da aka kai a ranar Litinin, inda aka sace bayanan sirrin dukkan ma'aikatan hukumar.

    Ƙungiyar masu kutse mai suna ShinyHunters, wadda ta shahara wajen aikata irin wannan ta'asa, ta yi barazanar wallafa bayanan da ta sace idan ba a biya mata bukatunta ba.

    Wakilin BBC ya ce zuwa yanzu hukumar FBI ba ta yi wani cikakken bayani kan wannan kutsen mai haɗari ba inda ta ƙi amsa tambayoyin ƴan jarida kan lamarin.

  18. Ƙawancen sojojin Saudiyya sun kakkaɓo jiraga marasa matuƙa na ƴan Houthi a Yemen

    Houthi

    Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya bayyana cewa, sojojinsa sun kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa guda biyu da ƴan tawayen Houthi suka harba zuwa birnin Riyadh, tare da wasu makamai masu linzami guda biyu da aka harba zuwa kudancin ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi magana kan yadda lamrin jin ƙai ke ƙara taɓarɓrewa, yayin da fararen hula ke ci gaba da fuskantar mummunan tasirin wannan rikici.

    A wani yanayi na nuna hadin kai da ba kasafai ake gani ba, a ranar Juma'a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da ƙaruwar hare-haren da ƴan tawayen Houthi ke kai wa ƙasar ta Saudiyya.

  19. Ba za mu lamunci cin mutunci da zare ido ba - Iran

    Iran

    Iran ta gabatar da wani sabon shiri na sake buɗe mashigar Hormuz cikin kwana bakwai, amma rahotanni na cewa Shugaba Trump zai yi watsi da shirin.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya shaida wa manema labarai a birnin New York cewa, za a sake buɗe mashigar ruwan muddin aka dakatar da dukkan faɗan da ake yi a yankin, ciki har da na ƙasar Lebanon.

    Ya ce yanzu zaɓi ya rage ga Amurka, Iran ba za ta amince da duk wani matsin lamba, cin mutunci ko neman a zare ma ta ido ba.

    Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa Donald Trump ya yi watsi da wannan ƙudirin na Iran, kuma yana shirin ci gaba da kai hare-hare bayan zaɓen tsakiyar wa'adi na Amurka.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo maku a kullum, barka da hantsi.

    Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya. Kamar kodayaushe, za mu ci gaba da wallafa labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Sai ku kasance tare da mu.