Lokuta huɗu da siyasa ta raba Kannywood

Kannywod

Asalin hoton, Social Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A tsawon shekaru, masana'antar Kannywood ta kasance tana nuna ƙwanji da tasiri a a tsakanin al'umma, musamman Hausawa wajen taka rawar gani a tsarin rayuwa da zamantakewa.

Wannan ya sa ƴan fim da mawaƙa da sauran masu harkokin na fim suke amfani da damar wajen shiga harkokin siyasa ana damawa da su, inda suke waƙoƙin kamfe, har suke samun muƙami.

A lokaci da dama, ƴan masana'antar sukan bayyana cewa sun shiga siyasa ne domin samun damar tallafawa masana'antar, tare da nemo mata hanyoyin inganta harkokinta.

Sai dai duk da cewa siyasa ta bai wa wasu ƴan Kannywood damar kusantar masu riƙe da madafun iko, a ɗaya ɓangaren ta kuma kasance sanadin rabuwar kai a tsakani ƴan masana'antar.

A lokuta daban-daban, ƴan masana'antar sukan kasu gida-gida bisa jam'iyya ko ɗan takarar da suke goyon baya, lamarin da ya kai ga samun cacar-baki da habaice-habaice da ma zarge-zarge.

Wannan ya sa BBC ta yi nazarin lokuta huɗu da siyasa ta shiga tsakani tare da dara masana'antar.

'Lema ta yage'

Zaben 2015 shi ne ya fara bayyana ɓaraka a tsakanin ƴaƴan masana'antar ta Kanywood bayan sun taka rawar gani a yaƙin neman zaɓen Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC har ya samu nasara.

Daga cikin fitattun masu goyon bayan Buhari a lokacin akwai Dauda Kahutu Rarara da Adam A. Zango da Bello Muhammad Bello da Fati Nijar da Abdul Amart da Halima Atete da Jamila Nagudu da Aminu Ladan Abubakar da Rukayya Dawayya da wasu da dama.

Wannan tafiya ta ƙara ƙarfi bayan kafa ƙungiyar APC Northern Musicians Forum (ANMFO), wadda ta zama ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka haɗa mawaƙan Arewa masu goyon bayan Buhari.

Daga cikin waƙoƙin siyasa da suka yi tashe a kakar zaɓen lokacin, akwai 'Lema ta yage' wadda Abdul Amart ya shirya, wadda ta zo da sabon salon tara mawaƙa da dama.

Sai dai daga an samu saɓani mai zafi a tsakani, inda har wasu mawaƙa suka yi barazanar shigar da ƙara kotu saboda zargin akwai kuɗin da aka ba su wani mawaƙi guda ɗaya ya yi sama da faɗi da su.

Atiku da Buhari sun raba kan Kannywood a 2019

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da zaɓen 2019 ya ƙarato, sai wani ɓangare na ƴan Kannywood ya ci gaba da goyon bayan Buhari da APC, yayin da wani sabon ɓangare ya fito fili ya bayyana goyon bayan Atiku Abubakar na PDP.

Masu goyon bayan Buhari sun ci gaba da amfani da APC Northern Musicians Forum, yayin da waɗanda ke bayan Atiku suka kafa Kannywood Initiative Door-2-Door for Atiku 2019.

Mika'il Bin Hassan, wanda ya kasance ɗaya daga cikin jagororin tafiyar Atiku, ya bayyana cewa sun kafa ƙungiyar ne domin su sanar da jama'a abin da suke ganin Atiku zai iya yi wa Najeriya. Ya kuma zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen tallafawa 'yan fim duk da irin rawar da Kannywood ta taka wajen taimaka masa a 2015.

A ɗaya ɓangaren kuwa, magoya bayan Buhari, sai suka ce lokacin da Buhari ya hau mulki Najeriya na cikin matsalar tattalin arziki da tsaro, amma gwamnatin ta samu nasarar shawo kan wasu daga cikin matsalolin.

Haka aka yi a kakar zaɓen aa tafka muhawara da musayar yawu har zaɓen ya wuce. Sai dai jim kaɗan bayan zaɓen aka fara samun ɓaraka na cikin gida a cikin ƙungiyoyin.

YBN da 13×13 a 2023

Bayan zaɓen 2019, da yawa sun yi tsammanin rikici ya ƙare, amma a yayin da zaɓen 2023 ya gabatowa, sai aka gane ashe akwai sauran rina a kaba.

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ne ya jagoranci ƙungiyar13×13, wadda ta haɗa mawaƙa da ƴan fim da dama, kamar su Adam A. Zango da Aminu Ala da Nura M. Inuwa da Umar M. Shareef da Yakubu Mohammed da Fati Nijar da Aishatu Humaira matar Rarara a yanzu.

A lokacin dai su ƙungiyar ta ce ba ta siyasa ba ce, illa dai ƙungiya ce ta taimakon juna da tallafa wa mabukata, saboda a farkonta a cikin mambobinta akwai mutane masu ra'ayoyin siyasa daban-daban.

YBN kuwa an samu sunanta ne daga Yahaya Bello Network, kuma ta kasance a ƙarƙashin jagorancin furodusa Abdul Amart Maikwashewa. Ƙungiyar ta yi wa Yahaya Bello waƙoƙi ne tare da tallata shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Sai dai a daidai lokacin da jagororin ƙungiyoyin biyu suka fara raba taimako, sai ya zama ɓangarorin biyu suka rubuce-rubuce da habaici tsakanin su, kowane ɓangare na nuna jagoransa a matsayi zakara.

A lokacin ne marigayi darakta Aminu S. Bono ya ba da shawarar a shirya wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci tsakanin YBN da 13×13 domin ƙarfafa zumunci da ɗinke kan masana'antar duk da a lokacin yana tare da Rarara ne.

Triple R da yaƙin zaɓen Tinubu

Yanzu kuma siyasa ta sake dawowa da wani sabon salo. Dauda Kahutu Rarara da tafiyarsa ta Triple R suna kara bayyana karfin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, yayin da wasu daga cikin 'yan Kannywood ke da ra'ayoyi daban-daban kan wannan tafiya.

Wannan sabon yanayin ya sake tayar da tsohuwar tambaya: shin Kannywood za ta sake shiga irin rarrabuwar da aka gani a 2015, 2019 da 2023?

Rarara ya dade yana daga cikin mawakan da suka fi shahara wajen amfani da waka wajen tallata 'yan siyasa. Saboda haka, shiga wata sabuwar tafiya ta siyasa ba sabon abu ba ne a gare shi. Amma idan aka yi la'akari da tarihin Kannywood, duk lokacin da wani bangare ya yi tsayin daka wajen tallata dan takara, wasu kan fito su nuna adawa ko su zabi wata tafiya.

A nan ne matsalar take. Ba laifi ba ne dan Kannywood ya goyi bayan dan takara. Ba kuma laifi ba ne wani ya ki goyon bayan wanda abokinsa yake tallatawa. Matsalar ita ce idan bambancin siyasa ya koma cin mutunci, habaici, kiyayya ko kuma amfani da siyasa wajen hana wani damar yin sana'a.

Tun daga Buhari da Atiku a 2015 da 2019, zuwa YBN da 13×13 a 2023, har zuwa Triple R da yakin Tinubu a yanzu, tarihi ya nuna cewa siyasa na iya hada Kannywood a lokaci guda, amma kuma tana iya raba ta gida biyu.

Zabe yana zuwa ya wuce, 'yan takara suna canzawa, jam'iyyu suna sauya matsayi, amma Kannywood za ta ci gaba da kasancewa. Don haka babban abin da ke gabanta shi ne ko za ta iya koyon darasi daga abubuwan da suka faru a baya: a bar kowa ya yi siyasa da ra'ayinsa, amma a kare zumunci, sana'a da makomar masana'antar.

Ƴan Kannywood da ke riƙe da muƙamin gwamnati

  • Ali Nuhu - Shugaban Hukumar Finafinai ta Najeriya
  • Rahama Sadau - Kwamitin iDICE
  • Bashir Datti - Kwamishina a jihar Filato
  • Abba El-Mustapha - Hukumar Tace Fina-finai ta Kano
  • Maryam Jankunne - Mai ba gwamnan Kano shawara kan matan karkara
  • Rabiatu Sulaiman Kurfi - Mai taimaka wa gwamnan Katsina kan kafofin sadarwa na zamani