Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 25/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Abdullahi Diginza da Rabiatu Kabir Runka

  1. Fafaroma Leo ya yi gargaɗi kan illar ƙirƙirarriyar basira ta AI

    HOTON FAFAROMA LEO

    Fafaroma Leo ya yi gargadi kan haɗurran da ke tattare da Fasahar kirkirarriyar Basirar (AI) yayin wata ziyara ta kwanaki huɗu a Faransa.

    Ya yi kira da a yi amfani da tantancewar ɗabi'a domin hana bil'adama ɓacewa a cikin wani abu da injuna ke mulki.

    An kiyasta cewa mutane dubu dari uku ne suka yi jerin gwano a kan titunan Paris domin ganin wucewar Fafaroman a cikin motar shi mai farin gilashi kan hanyarsa ta zuwa gabatar da huɗuba a babbar cocin Notre Dame.

    Da yake jawabi a hedikwatar hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, Paparoman ya kuma ce duniya na "lalacewa a hannun wasu tsirarun azzalumai".

    Ana sa ran babban limamin mabiya darikar Katolika na duniya zai gana da da matasa dubu tamanin a Stade de France.

  2. Rasha ta kai hari kan cibiyar adana bayanai ta Ukraine

    ukraine

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce Rasha ta faɗaɗa hare-harenta inda yanzu ta fara kai hari kan cibiyoyin adana bayanai da kamfanonin samar da intanet a Ukraine, domin saka ƴan ƙasar cikin mawuyaci hali.

    Ya ce hakan zai shafi yadda mutane ke amfani da hanyoyin sadarwa da kuma damar karatu da aiki.

    A ranar Juma'a, wani jirgi mara matuƙi na Rasha ya kai hari kan wata cibiyar kasuwanci a Kyiv, babban birnin Ukraine, inda ya kashe mutum huɗu tare da lalata wata cibiyar adana bayanai.

    Rasha ta tabbatar da kai harin kan wurin da ke ɗauke da cibiyar adana bayanai, tana mai cewa hukumar leƙen asirin sojin Ukraine ce ke amfani da shi.

    Kimanin gidaje 100,000 a Kyiv da yankin da ke kewaye da birnin sun fuskanci katsewar intanet a ranar Laraba sakamakon hare-haren.

    Wasu kamfanoni ma sun riga sun fara mayar da bayanansu daga na’urorin ajiyar bayanan da suka lalace zuwa ƙasashen waje.

    A birnin Lutsk da ke arewa maso yammacin ƙasar, jami’ai sun ce allunan bayanan lantarki da ke wuraren tsayawar motocin sufurin jama'a ba sa aiki tun ranar Juma'a.

    Majalisar birnin ta ce hakan ya faru ne "sakamakon ɓarnar da harin Rasha kan cibiyoyin adana bayanai a Kyiv ya haifar".

    A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Juma'a, Zelensky ya ce Rasha na ci gaba da faɗaɗa hare-harenta kan kamfanonin Amurka da na wasu ƙasashe, cibiyoyin adana bayanai, da masu samar da intanet.

  3. Ba mu amince da duk wani tallafi da China za ta ba Iran ba-Amurka

    Jakadan Amurka a China, David Perdue, ya shaida wa CNBC cewa Donald Trump ya bayyana wa Xi Jinping wata tattaunawa da suka yi da shugaban na China a Fadar White House, cewa ba su amince da taimakon da China ke bai wa Iran ba.

    A daren jiya, Mista Trump ya yi wata gagarumar liyafar cin abinci da shugaban China a Fadar White House.

    Ya bayyana Mista Xi da matarsa a matsayin mutane masu mutunci da ladabi, yana mai cewa ƙasashen biyu suna da tsarukan mulki daban-daban, amma dangantakar da ke tsakaninsu ta fi kowane lokaci kyau.

    Shi ma Xi Jinping ya ce bunƙasar China cikin lumana ba ya nufin koma bayan Amurka.

    Sai dai masu sa ido na nuna shakku kan ko taron zai haifar da wani gagarumin tasiri kan muhimman batutuwa masu sarkakiya kamar batun ƙirƙirarriyar basira ta AI, Rasha da kuma Iran.

  4. Ba za mu lamunci hari kan masallatan harami a Saudiyya ba - Pakistan

    Ka'aba

    Firaministan Pakistan ya ce tsaron Masallacin Harami da ke Makka da kuma Masallacin Annabi da ke Madina, wani jan layi ne da ba za a lamuncin ƙetare shi ba.

    Yayin da yake jawabi a babban taron MDD a New York, Shehbaz Sharif ya jaddada cikakken goyon bayan ƙasarsa ga Saudiyya tare da yin Allah-wadai da hare-haren Houthi kan ƙasar.

    Ya ƙara da cewa yarjejeniyar Makka ba ta nufin wata ƙasa guda ba, face nuna ƙudurin bai ɗaya na samar da zaman lafiya a yankin.

    Haka kuma ya yi kiran ci gaba da buɗe mashigarHormuz da kuma Bab al-Mandab domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa da kasuwanci.

    Firaministan ya kuma ce Pakistan ta ɗauki matakin gaggawa ta hanyar haɗin gwiwar diflomasiyya da sauran ƙoƙarin sasanci, domin cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ke addabar yankin Larabawa.

  5. Kotu ta ba Trump damar amfani da bayanan masu kaɗa ƙuriʼa

    Trump

    Kotun Koli ta Amurka ta ba gwamnatin Trump damar amfani da wata ma’ajiyar bayanan gwamnatin tarayya wadda ta jawo ce-ce-ku-ce, wadda ke amfani da bayanan zama ɗan ƙasa da sauran muhimman bayanai masu matuƙar sirri wajen gano masu kaɗa ƙuri’a da ake zargin ba ƴan ƙasar Amurka ba ne.

    Masu suka sun nuna shakku kan amincin waɗannan bayanai, suna gargadin cewa hakan na iya haifar da cire wasu ƴan ƙasar Amurka daga rajistar masu zaɓe bisa kuskure.

    A watan Yuni, wani alƙalin tarayya ya yanke hukunci cewa tsarin ya saɓa wa doka kuma tauye haƙƙin sirrin ƴan Amurka ne.

    Sai dai rinjayen alƙalan masu ra’ayin mazan jiya a Kotun Kolin sun ce Dokar Rajistar Masu Zaɓe ta Ƙasa ta haramta cire sunayen masu zaɓe daga rajista makonnin gabanin zaɓe, abin da ya sa ake ganin babu wani tasiri da wannan hukunci zai kafin zaɓen tsakiyar wa’adi.

    Sai dai har yanzu jihohi na da ikon tantance matsayin zama ɗan ƙasa na kowane mai zaɓe daban-daban.

    Alƙalai uku masu sassaucin ra’ayi a Kotun ƙoli sun nuna rashin amincewarsu da hukuncin.

    Ɗaya daga cikin alƙalan, Ketanji Brown Jackson, ta bayyana damuwarta cewa wannan matakin na iya tauye haƙƙin kaɗa ƙuri’a na wasu masu zaɓen da suka cancanta bisa kuskure.

  6. Iran ta saka sabbin sharuɗan buɗe mashigar Hormuz

    Ruwa

    Iran ta miƙa wa Amurka wata shawara kan sake buɗe mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi, ya shaida wa wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje.

    Araghchi, wanda ke birnin New York domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce ya isar wa wakilin Amurka Steve Wittkopf sharudɗan da Iran ta gindaya domin sake buɗe wannan muhimmiyar mashigar ruwa, inda zirga-zirgar jiragen ruwa ta yi matuƙar tangarɗa tun bayan fara yaƙin.

    Ministan ya shaida wa wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje, ciki har da The New York Times da The Guardian, cewa: "Idan aka cika wasu sharudɗa, za a buɗe mashigar cikin kwanaki bakwai, sannan a fara tattaunawa."

    Iran ta ce ta gabatar da sharudɗa bakwai domin kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.

    A cewar abin da jaridar New York Times ta rawaito daga Araghchi, shawarar ta ƙunshi buƙatun da suka haɗa da:

    • Tsagaita wuta na kwanaki bakwai a dukkan yankunan Gabas ta Tsakiya da rikicin ya shafa, ciki har da Lebanon
    • Sakin aƙalla dala biliyan 12 na kadarorin Iran da aka ƙwace.
    • Janye takunkumin da aka ƙaƙaba kan man fetur ɗin Iran.
    • Kawo ƙarshen datse tasoshin ruwanta da sojojin ruwan Amurka ke yi.

    A wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi da kakakin dakarun juyin juya halin ƙasar, Hossein Mohebi, a ranar Talata, ya kuma nuna cewa kawo ƙarshen faɗace-faɗacen da ake yi a Yemen na daga cikin sharudɗan da Iran ta gabatar.

  7. PDP ta saka ranar zaɓen fitar da gwanin gwamnan Gombe

    Pantami

    Jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta tantance Farfesa Isa Ali Pantami da Khamisu Ahmed Mailantarki da kuma Usman Aliyu Garry domin shiga sabon zaɓen fidda gwani na gwamna da za a sake gudanarwa a jihar.

    A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran PDP na jihar, Abdulkadir Ahmed Dukku, ya fitar a ranar Juma'a, ya ce an tantance mutanen uku kuma an tabbatar da cancantarsu ta shiga zaɓen fidda gwanin da aka tsara sake yi.

    A ran ar Alhamis ne babbar kotun tarayya da Gombe ta soke takarar Pantami sakamkon ƙarar da Mailantakrki da Garry suka shigar gabanta suka ƙalubalantar hanyar da ta bai wa pantami takara.

    Dukk ya ce bayan hukuncin kotun, jam'iyyar PDP na sanar da dukkan mambobinta masu katin rajista cewa za a gudanar da sabon zaɓen fidda ɗan takarar gwamna a ranar Talata 29 ga Satumba, 2026.

    ''Ana sa ran dukkan masu kaɗa ƙuri'a da suka cancanta za su hallara a mazaɓunsu domin zaɓar ɗan takarar da suke so," in ji shi.

    PDP ta ce ta karɓi hukuncin kotun cikin mutunci kuma tana girmama matakin da kotun ta ɗauka.

    Jam'iyyar ta kuma yi maraba da ɓangaren hukuncin da ya tabbatar da sahihancin matakan da Pantami ya bi wajen shiga jam'iyyar PDP.

  8. Za mu ci gaba da matsin lamba kan ƴanbindiga - Gwamnatin Sokoto

    Gwamnan Sokoto

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da matsa lamba ga ƴanbindiga har sai an samu zaman lafiya domin mayar da waɗanda suka rasa muhallansu zuwa gidajensu.

    Jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da ƴanbindiga suka addaba da hare-hare, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Abubakar Bawa ya fitar, gwamnan ya ce haɗin gwiwar gwamnati da hukumomin tsaro na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga a sassan jihar.

    A cewarsa, gwamnati ta samar da sabbin motoci masu sulke da sauran kayan aiki ga jami'an tsaro, waɗanda zai taimaka wajen ƙarfafa wa jami'an tsaron gwiwa.

  9. Su wane ne za su jagoranci yaƙin zaɓen Atiku Abubakar?

    ..

    Jam'iyyar ADC ta bayyana waɗanda za su jagoranci yaƙin zaɓen tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a fafutikar da take yi ta samun galaba a kan APC ta Bola Tinubu.

    Daga cikin waɗanda suka fi jan hankali a jerin sunayen akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai wanda yake tsare yana fuskantar shari'o'i daban-daban daga wajen hukumomin Najeriya.

    A cikin sanarwar, wadda Phrank Shaibu, mai magana da yawun Atiku, wanda kuma aka naɗa a matsayin daraktan ɓangaren sadarwa na yaƙin zaɓen, ya ce Atiku ya amince da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe.

    Ya ce: "Atiku Abubakar ya amince da kwamitin yaƙin zaɓe na ƙasa na neman zaɓen shugaban ƙasa," in ji shi.

    INEC ta sanya ranar 20 ga Fabrairun 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun tarayya, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi kuma za su gudana ne a 6 ga Maris 2027.

    Ku latsa nan domin karanta cikakken labarin.

  10. Pakistan za ta tattauna da Turkiyya da Saudiyya kan ƴan Houthi

    Pakistan ta ce za ta tattauna da Turkiyya da Saudiyya don sanin hanyoyin da suka fi dacewa ta taimakawa Riyadh a ta'azzarar yaƙi tsakanin dakarun Saudiyya da mayaƙan Houthi a Yemen.

    Sun gana ne ƙarƙashin wata yarjejjniyar tsaro da aka ƙulla a baya-bayan nan.

    Ana kuma tsara gudanar da wani taron gaggawa na manyan hafsoshin tsaro.

    Tun da farko, Babban mai fatawa na Saudiyya ya yi kira ga sojojin ƙasar da su shirya yaƙar ƴan Houthi da ke samu goyon bayan Iran har sai an kawar da su daga kan mulki.

    Mayaƙan Houthi sun zafafa hare-hare kan Saudiya ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami yayin da Saudiyya kuma ke mayar da martani ta hanyar kai musu hari ta sama.

  11. Jirgi maras matuƙi ya kashe sojojin Isra'ila biyu a Gaza

    Jirgi maras matuƙi

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta biyu sun mutu a arewacin Gaza bayan wani jirgin maras matuƙi da suke sarrafawa ya fashe bisa kuskure.

    A cewar rundunar sojin Isra'ilar, jirgin ya faɗi ne a cikin sansaninsu na soja a jiya saboda wasu dalilai da har yanzu ba a gano ba.

    Sojojin sun ɗauko jirgin bayan ya faɗi, amma ya fashe bayan ɗan wani lokaci kaɗan.

    Rundunar sojin Isra'ilar ta ce ta dakatar da amfani da dukkan ƙananan jirage marasa matuƙa da ake ɗora musu abubuwan fashewa har sai an kammala bincike kan lamarin.

  12. An samu ƙaruwar ƴangudun hijirar Sudan a Chadi

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an samu ƙari sosai na yawan ƴan gudun hijirar Sudan da ke tserewa yaƙi zuwa Chadi mai maƙwabtaka.

    MDD ta ce fiye da mutum 400 ne suke tsallaka iyaka a duk rana.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an samu ƙaruwar ’yan gudun hijirar Sudan da ke tserewa daga yaƙin basasar ƙasar zuwa makwabciyarta Chadi a wannan makon.

    Ta ce sama da mutum 400 ne ke tsallaka iyaka a kowace rana, adadin da ya kai kusan ninki 20 na yawan da aka saba gani.

    Hukumar kula ta ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tallafin da ake bayarwa ya yi ƙaranci matuƙa, yayin da ake samun ƙaruwar waɗanda ke yunƙurin tsallakawa zuwa Turai a matsayin baƙin haure saboda rasa muhallansu.

    Sudan ta shiga cikin rikicin shugabanci tsakanin Rundunar Sojin ƙasar (SAF) da dakarun RSF yayin da yaƙin ke shiga shekara ta huɗu.

  13. Wane zaɓi ya rage wa Pantami bayan kotu ta soke takararsa?

    ..

    Har yanzu jama'a na ci gaba da muhawara kan makomar takarar gwamnan jihar Gombe da Farfesa Ali Isa Pantami ke yi a zaɓen da ke tafe.

    A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Gombe ta soke tikitin fitaccen malamin Addinin Musuluncin, wanda ke yi wa jam'iyyar adawa ta PDP takara a zaɓen 2027.

    Usman Aliyu Garry ne ya shigar da ƙarar Pantami a gaban kotun yana ƙalubalantar halascin hanyar da ya bi wajen samun takarar.

    A watan Yunin 2027 ne jam'iyyar PDP ta tsayar da tsohon ministan sadarwar Najeriyar takarar gwamnan jihar, kwanaki kaɗan bayan komawarsa jam'iyyar daga APC.

    Tun da farko Pantami ya tsaya takarar gwamnan ne a jam'iyyar APC, amma da bai yi nasara ba ya fice daga cikinta.

    Me hukuncin kotun ya ƙunsa?

    A hukuncin da ta yanke babbar kotun tarayyar ta buƙaci jam'iyyar PDP ta sake zaɓen fitar da gwanin gwamnan jihar.

    Mai shari'a Amina Mohammed ta ce tsarin da PDP ta bi wajen bai wa Pantami takara ya saba wa ƙa'idojin jam'iyyar da kuma dokokin zaɓe da suka dace ba.

    A cewar kotun hakan ya haifar da cire wasu masu neman takarar da aka tantance kuma aka amince su shiga zaɓen fidda gwani.

    Ga ƙarin bayani a nan.

  14. Ƴan Najeriya 105 sun sake komawa gida daga Afirka ta Kudu

    ..

    Wasu ’yan Najeriya 105 sun sake komawa gida daga Afirka ta Kudu, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa game da tsaron ’yan ƙasashen waje gabanin wa’adin 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka ayyana.

    ’Yan Najeriyar sun isa Lagos cikin jirgin South African Airways da misalin ƙarfe 8:30 na daren Alhamis, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana.

    Ma’aikatar ta shaida wa BBC yau Juma’a cewa gwamnati ta taimaka wajen dawo da ’yan Najeriya 1,821 tun daga watan Yuni, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin sake ɓarkewar hare-hare kan baƙi da ’yan Afirka.

    Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Femi Adeniyi, ya ce: “Ana ci gaba da ƙoƙarin kwashe ƙarin ’yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali sakamakon fargabar tsaro a Afirka ta Kudu.”

    Dawowar ta baya-bayan nan na zuwa ne ’yan kwanaki kafin 30 ga Satumba, ranar da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka ce ya kamata ’yan ƙasashen waje da ba su da takardun zama su fice daga Afirka ta Kudu.

    An taɓa sanya makamancin wannan wa’adi a ranar 30 ga Yuni. Dubban mutane sun shiga zanga-zangar adawa da baƙin haure a faɗin ƙasar, inda aka bayar da rahoton aukuwar tashin hankali da sace-sace a wasu wurare. ’Yan sanda sun ce an kama kusan mutum 900, galibinsu bisa laifukan da suka shafi shige da fice da sace-sace.

    Hukumomin Afirka ta Kudu sun jaddada cewa gwamnati ce ke da alhakin aiwatar da dokokin shige da fice kuma sun gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu da kai hare-hare kan ’yan ƙasashen waje.

    Ba Najeriya kaɗai ce ke taimaka wa ’yan ƙasarta ficewa daga Afirka ta Kudu ba.

    Malawi ta ce ta dawo da ’yan ƙasarta fiye da 38,000 tsakanin watan Yuni da farkon Yuli, yayin da Zimbabwe ta ce sama da mutum 21,000 sun koma gida. Uganda, Ghana da Mozambique ma sun dawo da wasu daga cikin ’yan ƙasarsu.

    Hukumomin Afirka ta Kudu sun ce zuwa ranar 11 ga Yuli, an kammala shirye-shiryen mayar da ’yan ƙasashen waje fiye da 53,000 zuwa ƙasashensu, inda ’yan Malawi da Zimbabwe da Mozambique suka fi yawa.

  15. An bankaɗo ɓoyayyen ɗakin sarrafa ƙwayar Methamphetamine a Najeriya

    ..

    Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta tarwatsa wani ɓoyayyen dakin sarrafa ƙwayar methamphetamine da ake zargin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ’yan Najeriya da Mexico.

    An kama wasu ’yan Najeriya biyu masu shekaru 45 da 60, kuma an gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin hannu a lamarin a Jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

    NDLEA ta ce mutanen biyu, Chukwu Obumneme Christopher, wanda aka fi sani da Brown, da Chukwu Georginus Monday, wanda aka fi sani da George, sun yi aiki tare da wani ɗan Mexico.

    Mutanen biyu sun gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Enugu bisa tuhume-tuhume biyar, ciki har da haɗa baki, ɗaukar nauyin ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar sinadarai da ake amfani da su wajen haɗa methamphetamine.

    Sun amsa aikata zargin da ake yi musu. Ana sa ran fara shari’arsu ranar 21 ga Oktoba.

    NDLEA ta ce wasu mutum uku da aka ambata a shari’ar, ciki har da wanda ake zargi ɗan Mexico ne, sun tsere.

    Masu bincike sun ce sun bibiyi zirga-zirgar Christopher tsakanin jihohin Lagos, Enugu da Anambra a watan Disamban 2025, kafin daga bisani suka samu gano ɗakin sarrafa ƙwayar a wani gida da ke Obeagu, Jihar Enugu.

    Hukumar ta ce an tanadi kayan aikin da za su iya samar da methamphetamine da yawa domin kasuwanci. An kuma ƙwace sinadarai da kayan aiki masu yawa.

    Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya ce wannan samame ya nuna cewa Najeriya ba za ta bari ƙasar ta zama mafaka ga ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa ba.

    Ya ce: “Gano wannan dakin sarrafa ƙwayoyi a Enugu ƙarin shaida ne cewa ba za a bari Najeriya ta zama mafaka ga ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa ba.”

  16. Babban mai fatawa na Saudiyya ya buƙaci sojin ƙasar su yi shirin yaƙar Houthi

    ...

    Babban mai fatawa na Saudiyya ya buƙaci sojojin ƙasar da su kasance cikin shirin yaƙi har sai an kawar da 'yan Houthi masu samun goyon bayan Iran daga mulki a Yemen.

    Wannan saƙo da ba kasafai ake ji daga Sheikh Saleh bin Fawzan Al-Fawzan, ya zo ne bayan shafe makonni ana samun ƙaruwar rikici, inda 'yan Houthi ke kai wa Saudiyya hare-hare da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami, yayin da Saudiyya ke mayar da martani da hare-hare ta sama.

    Turkiyya ta tura babban hafsan sojojinta zuwa Riyadh domin tattauna hanyoyin tallafa wa Saudiyya a ƙarƙashin yarjejeniyar tsaron juna ta Makka, wadda aka rattaba hannu a kai baya-bayan nan.

  17. Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

    ..

    Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da kafa kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa, wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin Kashim Ibrahim-Imam sai Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa.

    Naɗin na zuwa ne yayin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumomi bisa tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi masa.

    Daraktan yaɗa labarai na kwamitin, Phrank Shaibu, wanda kuma shi ne babban mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

    Sanarwar ta ce an tsara kwamitin ne bisa la'akari da halin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da tashin farashin kayan masarufi da tsadar sufuri da kuma raguwar kudaden shiga.

    An nada Sanata Austin Akobundu a matsayin babban daraktan yakin neman zaben, wanda zai jagoranci aiwatar da dabarun kwamitin cikin tsari.

    Haka kuma, mataimakan babban darakta shida za su kula da harkokin gudanarwar kwamitin, inda za su yi aiki tare da daraktoci 30 da aka ɗorawa nauyin kula da fannoni daban-daban.

    Dele Momodu ne zai shugabanci harkokin yaɗa labarai da sadarwa yayin da Dino Melaye kuma zai jagoranci sashen tuntuɓa.

    Shi kuma Mohammed Hayatudeen zai jagoranci kwamitin tsara manufofi tare da Farfesa Mohammed Sagagi da wasu mambobi kamar Farfesa Kingsley Moghalu.

  18. Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600

    Aliko Dangote

    Attajirin Afirka Aliko Dangote da gwamnatocin Habasha da Djibouti sun cimma yarjejeniyar gina bututun man fetur da rumbun ajiyarsa da za su haɗa ƙasashen biyu, a wani aiki da zai laƙume dala miliyan 600.

    Aikin zai haɗa da gina bututun mai mai tsawon kilomita 120 da zai haɗa tashar jiragen ruwa ta Damerjog a Djibouti zuwa cibiyar rarraba mai da ke Dewele a Habasha. Haka kuma, za a gina rumbunan da za su iya ɗaukar kusan lita miliyan 400 na man fetur.

    Ana sa ran fara aikin cikin watanni 18.

    Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce bututun zai rage lokacin da ake ɗauka wajen jigilar mai daga tashar jiragen ruwa ta Djibouti zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha, daga kwanaki biyar zuwa kwana ɗaya.

    A matakin farko, za a riƙa jigilar muhimman albarkatun man fetur, ciki har da man jirgin sama, dizal da fetur.

    Da yake jawabi a bikin ƙaddamar da aikin, Dangote ya ce aikin zai ƙarfafa makamashi a Habasha tare da inganta tsarin samar da man fetur na ƙasar.

  19. Fashewar jirgi mara matuƙi ta halaka sojin Isra'ila biyu a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojinta biyu sun mutu a arewacin Gaza bayan da jirgi mara matuƙi da suke aiki da shi ya fashe bisa kuskure.

    Jirgin ya tarwatse ranar Alhamis a sansanin sojoji amma ba a san dalilan faruwar hakan ba.

    Sojojin sun ɗauko jirgin mara matuƙi, kwatsam kuma sai ya fashe.

    Rundunar sojin ta dakatar da amfani da ƙananan jirage mara matuƙa da ke ɗauke da abubuwan fashewa.

  20. An samu ƙaruwar masu fama da talauci a Argentina

    Adadin 'yan kasar Argentina da ke fama da talauci ya karu a bana, yayin da gwamnatin shugaba Javier Milei ke kokarin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, abin da ya kasance daya daga cikin muhimman alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

    A yanzu, kusan mutum daya daga cikin kowane mutum uku a kasar yana fama talauci wanda ke nuna karuwar kashi hudu cikin dari.

    Masu suka sun ce tsare-tsaren tattalin arzikin shugaban kasar da kuma rage shirye-shiryen tallafawa al'umma da ya yi sun kara ta'azzara matsalar matsin rayuwa.

    Argentina ta ga karuwar shigo da kayayyaki daga waje, wanda hakan ya haifar da asarar ayyukan yi a masana'antun cikin gida