Yadda Netanyahu ya kai ƙarar shugaban Turkiyya wajen Trump

    • Marubuci, BBC Türkçe
    • Aiko rahoto daga, Londra
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Amurka Donald Trump da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun yi waya ranar 9 ga watan Yuli, bayan Trump ɗin ya koma gida daga taron ƙungiyar NATO da ya halarta a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya.

A lokacin da suka yi wayar, Netanyahu ya yi wa Trump ƙorafi game da Turkiyya.

Kamfanin dillancin labaru na Faransa – AFP, ya ruwaito cewa Netanyahu ya zargi shugaban Turkiyya Receb Tayyib Erdogan da ire-irensa da "yin kalamai waɗanda ke nuna adawa da wanzuwar ƙasar Isra'ila tare da neman a shata wani layin tsaro a iyakokin ƙasar ta Isra'ila."

Haka nan Netanyahu a farkon wannan mako ya yi kira ga Amurka da kada ta sayar wa Turkiyya jiragen yaƙin zamani na F-35.

Ma'aikatar harkokin waje ta Turkiyya ta fitar da wata sanarwa cewar "zarge-zargen da jami'an gwamnatin Isra'ila ke yadawa a kwanakin nan ba su da tushe, kuma an tsara ne domin yaɗa ƙarya."

"Netanyahu da mutanensa suna juya duk wani ƙorafi da aka yi a kansu da gangan a wani ɓangare na yada farfaganda," a cewar sanarwar.

A lokacin ganawarsa da Shugaba Erdogan ranar 7 ga watan Yuli, Donald Trump ya shaida wa manema labarai cewa za a ɗage wasu takunkumai a kan Turkiyya kuma Amurka na tunanin sayar wa Turkiyya jiragen yaƙi samfurin F-35.

Trump ya ce "wannan mataki ne da muke tunanin ɗauka. Jirgi ne mai kyau, ya ɗara sauran jirage sosai, kuma muna tunanin hakan (sayar wa Turkiyya)."

A ranar 8 ga watan Yuli, lokacin tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron ƙasashen NATO, Erdogan ya mayar da martani daga tambayar da wakiliyar kamfanin dillancin labarai ta Reuters ta yi masa cewa "Shugaban Amurka Donald Trump ya ce 'bai kammala yanke hukunci ba' game da sayar wa Turkiyya jirgin yaki samfurin F-35. Mene ne abin da ya faɗa maka?" sai ya amsa mata da cewa "ki saurari abin da zai biyo baya".

A shekarar 2019 ne aka cire Turkiyya daga shirin samar da jiragen F-35 duk kuwa da cewa tana daga cikin ƙasashen da suka assasa shi. An yi hakan ne bayan Turkiyyar ta sayi na'urar garkuwar hare-haren samaniya samfurin S-400 daga Rasha.

Amurka ba ta ce uffan ba

Har yanzu babu wata sanarwa da aka samu daga Amurka a hukumance game da batun.

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa tabbas an yi tattaunawara amma bai yi ƙarin haske kan abin da aka tattauna ba.

A ranar 9 ga watan Yuli, mujallar Wall Street Journal da ke Amurka ta ambato wasu majiyoyin da ba ta fayyace su ba, na iƙirarin cewa Isra'ila ta sanar da Amurka cewa hukumominta na tsaro da leƙen asiri sun gano wani shiri da gwamnatin Iran ke yi na kashe shugaba Trump.

Ana sa ran Netanyahu zai kai ziyara Amurka a mako mai zuwa domin ganawa da shugaba Trump a fadar White House.