Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa aka jinkirta jana'izar Khamenei duk da tanadin Musulunci na gaggauta binne mamaci?
Tun ranar Juma'ar makon da ya gabata ne aka fara gudanar da tarukan jana'izar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, har zuwa ranar Alhamis, inda za a binne shi a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.
An ajiye akwatunan gawar Khamenei da wasu mutum huɗu daga cikin iyalansa a wani wuri na musamman a Tehran a safiyar Asabar 4 ga Yulin 2026. An lulluɓe akwatunan da tutar Iran, inda aka sanya su cikin gilashi kuma makarar sun fi yadda aka saba yi tsawo.
Mahukuntan Iran sun ce ba don dalilan tsaro kaɗai aka sanya gawarwakin cikin gilashin ba, har ma domin amfani da tsarin sanyaya yanayi da zai taimaka wajen kiyaye su.
Har yanzu gwamnati ba ta yi cikakken bayani kan irin raunukan da suka yi sanadin mutuwar Khamenei ba, sai dai ta ce ya rasu ne sakamakon fashe-fashen abubuwa.
Bayan sanar da rasuwarsa da kuma jinkirin binne shi, an fara yin tambayoyi a kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta kan ko an bi ƙa'idojin Musulunci wajen shirya jana'izar.
A ƙoƙarin amsa waɗannan tambayoyi, jami'an Iran sun fitar da wasu bayanai kafin jana'izar.
Mai magana da yawun kwamitin shirya jana'izar, Iman Attarzadeh, ya ce: "An killace gawar cikin girmamawa da kulawa, bisa ƙa'idojin addini da na doka. Ba a binne ta ba, kuma ba a ajiye ta haka kawai ba."
Sai dai Imam Attarzadeh bai yi cikakken bayani kan abin da ya kira bin ƙa'idojin shari'a ba. Maimakon haka, ya fi mayar da hankali kan abin da ake kira "wadi'a" a Musulunci, wato ajiyar gawar mamaci na ɗan lokaci kafin a kammala shirye-shiryen jana'iza.
Jinkirin da aka samu tsakanin mutuwar Ali Khamenei da ranar binne shi ya sake haifar da tambayoyi kan abin da shari'ar Musulunci ta tanada game da jinkirta binne mamaci, da kuma ko hakan ya halatta a irin wannan yanayi?
Muhimmancin mutunta mamaci a Musulunci
Tun daga lokacin da ran mutum ya fita daga jikinsa, Musulunci na ɗaukar gawarsa a matsayin abin girmamawa. Saboda haka, ana gudanar da wasu ibadu da al'adu na addini har zuwa lokacin da za a binne mamacin. A wasu al'ummomi, waɗannan al'adu sun samo asali ne daga tatsuniyoyi.
Musulunci ya yi bayani mai muhimmanci kan "mutunta mamaci", kuma ana buƙatar a gaggauta binne gawar domin kiyaye wannan mutunci.
A lokacin wasu kashe-kashen da suka faru a watan Janairun 2026, inda aka tara gawarwakin masu zanga-zanga cikin kwantena da manyan motoci, sannan aka wallafa hotunan yadda aka kula da gawarwakin, an yi ta cece-ku-ce kan dalilan da suka sa ba a mutunta mamatan ba, daidai da koyarwar Musulunci.
Haka kuma, an yi ta muhawara kan takunkumai da matakan tsaro da aka sanya yayin jana'izarsu.
Malamin addini Hassan Fereshtian ya shaida wa BBC cewa: "A fiƙihun Shi'a, mamaci yana da irin mutuncin da mai rai yake da shi. Saboda haka akwai ƙa'idojin da ke kare mutuncin gawar mutum, har ma da ta abokin gaba."
A cewarsa, kafin zuwan Musulunci da kuma a wasu yaƙe-yaƙe a lokacin da al'adu ke tasiri, akan wulaƙanta gawar abokin gaba bayan kashe shi, kuma ana ɗaukar hakan a matsayin alamar nasara. Sai dai Musulunci ya haramta irin wannan ɗabi'a, inda ya ƙara da cewa ko gawar wanda aka kashe a yaƙi tana da mutunci, kuma bai halatta a wulaƙanta ta ba.
Malamin ya ce akwai dalilai uku da suka sa ake kare mutuncin mamaci. Na farko, mamaci yana da iyali da ƴan'uwa da ke ƙaunarsa, kuma cin mutuncin gawarsa na haifar musu da ƙarin raɗaɗi. Na biyu, mutunta mamaci na daga cikin ƙa'idoji da ɗabi'un da al'umma ke darajantawa, kuma raina gawar mutum na iya raunana wannan ƙima. Na uku kuwa shi ne, ko bayan mutuwar mutum, abin da ya rage daga gare shi yana ci gaba da samun girmamawa a wajen mutanen da ke raye.
Ya kuma ƙara da cewa shari'ar Musulunci ta tanadi hukunce-hukunce na musamman kan duk wani nau'in cin zarafi ko wulaƙanta gawar mamaci. Kamar yadda cutar da mai rai ke da hukuncinta a shari'a, haka ma cin zarafin gawar mamaci na da hukuncin da ya dace.
Wannan, a cewarsa, na nuna cewa mutuncin ɗan'adam na ci gaba da kasancewa ko bayan mutuwarsa.
Musulunci na so a gaggauta binne mamaci
A koyarwar Shi'a (Imamiyya), ana ba da muhimmanci sosai kan gaggauta binne mamaci. Malaman Shi'a sun bayyana cewa bai kamata a jinkirta binne gawar ba, ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba, kuma ya kamata a gudanar da jana'iza da wuri idan babu wani uzuri ko wani dalili na musamman.
Hassan Fereshtian, mai nazari kan harkokin addini, ya bayyana muhimmancin gaggauta binne mamaci a koyarwar Shi'a da Sunna, inda ya ce: "Gaggauta binne mamaci na daga cikin abubuwan da shari'a ta ke so a yi, amma a koyarwar Shi'a, wannan ba wajibi ba ne, ba kuma wani sharadi na shari'a ba ne."
Ya ƙara da cewa a koyarwar Shi'a, duk da cewa ana son gaggauta binne mamaci, wannan ba wajibi ba ne. Kamar ƙarfafa wa al'umma ne kawai kuma ya samo asali ne daga girmama mamaci da matsayin da yake da shi a cikin al'umma.
Sai dai ya ce wannan matsaya tana da ƙarfi sosai a wajen wasu malaman Sunna, inda wasu daga cikinsu ke ganin cewa idan hali ya yi, ya kamata a binne mamaci a ranar da ya rasu kafin faɗuwar rana.
Hassan Fereshtian ya ƙara da cewa a cikin ƴan shekarun nan, buƙatar gudanar da binciken gawarwaki, da kuma shirye-shiryen zaman makoki sun sa lokacin da ake ɗauka tsakanin mutuwa da binne mamaci yana ɗaukar kwanaki.