Bowen: Trump ba shi da wani zaɓi da ya wuce tattaunawa da Iran

    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sabbin kalaman Donald Trump game da Iran da yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu ta hanyar tattaunawa ya kamata a ɗauke su da muhimmanci, domin shi ne shugaban ƙasar Amurka.

Ga abin da ya faɗa a taron ƙasashen Nato da aka gudanar a Turkiyya:

"Ba na son mu ci gaba da mu'amala da su. Su miyagu ne. Kun san abin da ake nufi da miyagu? Miyagu ne. Mutane ne marasa hankali. Mutane marasa hankali ne ke jagorantarsu. Kuma mutane ne masu mugunta da tashin hankali.

Kuma da sun mallaki makamin nukiliya, da sun yi amfani da shi. A gare ni, komai ya ƙare."

Amma shin waɗannan ne kalamansa na ƙarshe kan wannan batu? Ko kaɗan ba haka ba ne. Ya ci gaba da yin tsokaci akai-akai kan yaƙin da kuma takardar fahimtar juna da ake tattaunawa a kanta.

Kalaman nasa sun kasance suna sauyawa tsakanin iƙirarin nasara da barazanar rusa wayewar Iran gaba ɗaya, da kuma goyon bayan tattaunawar sulhu.

Daga baya ya sake jaddada sabbin barazanarsa, yana cewa Amurka "mai yiyuwa ne ta sake kai musu hari mafi ƙarfi a daren yau", sannan ya ƙara da cewa:

"Na ba su ɗan gargaɗi kaɗan. Za mu sake kai musu hari mai tsanani a daren yau."

Babu shakka kan ikon Amurka na kai wa Iran hare-hare da kuma haddasa babbar illa. Amma abin da har yanzu ba ta iya yi ba shi ne karya ƙudurin gwamnatin Iran domin ta yi watsi da muhimman buƙatunta, musamman batun kula da zirga-zirgar jiragen ruwa na Mashigin Hormuz.

A cikin sabbin kalaman da Trump ya yi cikin fushi da suka, akwai wani abu da ya nuna cewa har yanzu tattaunawar za ta ci gaba.

An dakatar da tattaunawar ne yayin da Iran ke gudanar da kwanaki na zaman makoki da jana'izar tsohon Jagoran Juyin-Juya Halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, wanda Isra'ila da Amurka suka kashe a ranar farko ta yaƙin da ya fara a ranar 28 ga Fabrairu.

An tambayi Trump ko musayar hare-haren da ake yi tsakanin Amurka da Iran – da kuma shigar wasu ƙawayen Amurka na Larabawa a yankin Tekun Fasha – na nufin cewa tattaunawar ta ƙare.

Yana magana ne kan manyan masu jagorantar tattaunawarsa, Steve Witkoff da Jared Kushner, inda ya ce:

"Ban damu ba, za su iya ci gaba da magana. Amma ina ganin suna ɓata lokacinsu ne kawai."

Sannan game da gwamnatin Iran ya ce:

"Su tarin maƙaryata ne."

Me hakan yake nufi?

Ana iya fassara hakan a matsayin wata alama cewa shugaban Amurka, duk da zafafar kalamansa, ba shi da wata hanya mafi kyau da ta wuce tattaunawa.

Tare da taimakon Isra'ila, Amurka ta yi ƙoƙarin rusa gwamnatin Iran amma ta gaza.

Sai dai tsarin tattaunawar yana cikin mawuyacin hali. Wata majiya daga cikin masu shiga tsakani da ke ƙoƙarin ganin an samu nasarar tattaunawar ta bayyana abin da ya faru:

"Tabbas babban koma baya ne."

An kuma ce yanayin yanzu "yana da matuƙar cike da tashin hankali."

Wannan wata hanya ce ta diflomasiyya ta bayyana cewa abubuwan da suka faru a kwanakin baya sun sanya tattaunawa tsakanin ɓangarori biyu da ba su amince da juna ko kaɗan ba ta zama mai wahala ƙwarai.

A tsakiyar sabbin musayar hare-haren soja tsakanin Iran da Amurka akwai ƙudirin gwamnatin Tehran na cewa ba za ta koma yanayin da ake ciki kafin harin Amurka da Isra'ila na ranar 28 ga Fabrairu ba.

Gwamnatin Iran ta ƙuduri aniyar ci gaba da riƙe ikon Mashigin Hormuz. Ikon dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa masu ɗauke da muhimman kayayyaki, ciki har da kusan kaso ɗaya cikin biyar na arzikin mai da iskar gas na duniya, yana ba ta wata babbar dama ta matsa lamba ga tattalin arzikin duniya.

Wannan wata dabara ce da za a iya amfani da ita cikin sauƙi fiye da yiwuwar ta ƙera makamin nukiliya.

Ko Iran za ta miƙa iko da Mashigar Hormuz?

Iran ba za ta amince da miƙa ikon Mashigar Hormuz ba. Saboda haka ne take shirye ta sanya yarjejeniyar fahimtar juna cikin haɗari – duk da irin alfanu da za ta iya samu daga gare ta – domin ta nuna cewa babu komawa baya.

Haka kuma tana shirye ta ci gaba da fuskantar yaƙi domin kare abin da take ganin haƙƙoƙinta ne na dabarun tsaro da iko a mashigin.

Gwamnatin Tehran ta ƙara samun ƙarfin gwiwa bayan gazawar Amurka da Isra'ila wajen rusa ta.

Tarukan jana'izar jagoran da aka kashe a farkon yaƙin sun nuna cewa gwamnatin Musulunci har yanzu tana da wani babban rukuni na magoya baya.

'Yan adawa a cikin gida ba su ɓace ba. Amma munanan matakan da gwamnati ta yi amfani da su wajen murƙushe zanga-zanga, inda aka kashe dubban mutane a watan Janairu, ya sa masu adawa suka rage fito-na-fito da gwamnati.

Masu shiga tsakani da ke cikin tattaunawar sun yi imanin cewa idan aka samu dakatar da wannan sabon tashin hankalin, har yanzu akwai yiwuwar a cimma yarjejeniya da Iran wadda za ta ba da damar jiragen ruwa su rika wucewa ta Mashigin Hormuz.

Amma hakan zai buƙaci wata faffaɗar yarjejeniya da za ta haɗa da:

  • Sakin wasu kadarorin Iran da ke taskace a ƙasashen waje.
  • Ba Iran damar sayar da man fetur dinta.
  • Kuma mafi muhimmanci ga gwamnatin Iran, amincewa da ikonta a kan Mashigin Hormuz.

A madadin haka, Iran za ta amince da:

  • Takaita tace da inganta sinadarin uranium.
  • Barin masu binciken nukiliya na Majalisar Ɗinkin Duniya su koma aiki a ƙasar.
  • Bayyana adadin abin da Trump ya kira "ƙurar nukiliya", wato uranium ɗin da aka riga aka tace zuwa matakin da zai iya kusantar amfani wajen ƙera makamin nukiliya.

Sai dai abubuwan da suka faru cikin sa'o'i 24 da suka gabata sun nuna irin wahalar da cimma irin wannan yarjejeniya za ta fuskanta.