Da gaske an daina karɓar takardar naira 100 a Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A baya-bayan nan ƴan Najeriya sun shiga ruɗani game da sahihancin takardar kuɗi ta naira 100.

Rahotonni daga wasu yankunan ƙasar sun nuna cewa wasu a ƙasar sun daina karɓar tsohuwar takardar kuɗi ta naira 100.

Najeriya na amfani da nau'uka biyu na takardar kuɗi ta naira 100, waɗanda duk hukumomin sun amince da su.

Tun asali akwai takardar naira 100 da ake amfani da ita, sai dai a shekara ta 2014 babban bankin Najeriya ya fitar da wata sabuwar takardar naira 100 wadda aka yi wa sauye-sauye, a wani ɓangare na murnar cikar ƙasar shekara 100 da samuwa.

Me ya bambanta takardun naira 100 guda biyu?

Ta farko ita ce wadda Babban Bankin Ƙasar, CBN ya ɓullo da ita a shekarar 1999, a wani yunƙuri na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Haka a lokacin CBN ya ce ya ɓullo da takardar ne domin bunƙasa sauƙin musayar kuɗaɗe tsakanin al'umma.

Takardar na ɗauke da hoton fitaccen ɗan kishin ƙasar nan na Najeriya, Obafemi Owolowo a gabanta, da kuma hoton Dutsen Zuma a baya.

Sai kuma nau'i na biyu na takardar ta naira 100, da CBN ya ɓullo da ita a shekarar 2014.

Tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan ne ya ɓullo da ita ranar 12 ga watan Nuwamban 2014, wadda kuma ta fara aiki ranar 19 ga watan Disamban 2014.

A lokacin hukumomi sun ce an ɓullo da ita ne a wani ɓangare na murnar bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa.

Sabuwar takardar tana da hasken fari-fari- idan aka kwatanta da tsohuwar wadda ita ja ce.

Sannan tana ɗauke da sabbin alamomin da babu su a jikin tsohuwar, ciki har da wata koriyar alama a tsakiyarta.

Sannan kodayake an bar hoton Owolowo a jikinta, amma an cire hoton Dutsen Zuma da ke bayanta, tare da maye gurbinsa da wasu mutum biyar da ke nuna wasu ƙabilu da sana'o'i al'ummar ƙasar.

Bayan ɓullo da sabuwar, CBN ya bayyana a lokacin cewa za a ci gaba da amfani da duka nau'ukan takardun kuɗin biyu.

Me ya sa a yanzu aka fara shakka kan tsohuwar takardar?

Rahotonni sun ce wasu mutane da masu sana'o'i sun fara guje wa karɓar tsohuwar takardar ne saboda fargabar ko ta daina aiki a hukumance.

Kodayake babu wata takamammiyar hujja da masu ƙin karɓar tsohuwar takardar ke bayarwa, amma dai masu sharhi sun ce hakan ba ya rasa nasaba da rage buga ta da CBN ya yi.

A wasu wuraren ma an jima ba a ga takardar kuɗin ba, lamarin da masu sharhi ke ganin ya sa mutane fara tunanin an daina amfani da ita.

Me Babban Bankin Najeriya ya ce?

Babban Bankin Najeriyar, CBN ya ce har yanzu ana ci gaba da amfani da kuɗin a hukumance.

Cikin wata sanarwar da bankin ya fitar ya ce zuwa yanzu babu wani wa'adi da ya ɗiba na daina amfani da tsohuwar takardar ta naira 100.

''Mun samu rahotonnin cewa wasu ƴan Najeriya sun daina karɓar tsohuwar takardar naira 100, to muna son sanar wa al'umma cewa har yanzu ana amfani da ita a hukumance'', in ji sanarwar da daraktar riƙo ta sashen sadarwar bankin, Mrs Hakama Sidi-Ali ta fitar.

CBN ya kuma gargaɗi masu guje wa karɓar takardar cewa hakan babban laifi ne a ƙarƙashin dokokin ƙasar.

Babban bankin ya kuma ƙara da cewa zai ɗauki tsaurara matakan hukunci ga duk shago ko ɗan kasuwa ko bankin da aka samu da laifin ƙin karɓar takardar kuɗin.