Ko ƴan wasan bayan Spain za su iya takura ƴan wasan gaban Belgium?
Ƙwallaye 13 da Belgium ta ci su ne na uku mafi yawa a wannan gasar (bayan Argentina(14) da Faransa (16), kuma sun yi nasara a kan New Zealand, Senegal da Amurka a wasanni uku da suka gabata.
Romelu Lukaku ya zura ƙwallaye uku yayin da ya ke shigowa daga kan benci, yayin da Leandro Trossard na Arsenal ya zura ƙwallaye biyu ya kuma taimaka aka ci biyu.
Babu shakka Spain za ta kasance ƙalubale mafi wahala daga wasannin da ta yi a baya. Har yanzu ba a zura mata ƙwallo ko ɗaya ba a wannan gasar, kuma wasa shida da ta yi ba tare da an zura mata ƙawallo ba - ciki har da wasansu na ƙarshe a gasar 2022 - shi ne jerin wasanni mafi tsayi da kowace tawaga ta taɓa yi a tarihin gasar cin kofin duniya.
A ƙarƙashin jagorancin Luis de la Fuente, Spain ta samu tsallakawa daga duka wasannin shida da ta buga a zagayen kifa-ɗaya-ƙwala a gasar kofin duniya da kuma ta cin kofin nahiyar Turai. Wannan shi ne wasanta na farko a zagayen kwata-fainal tun bayan da ta lashe gasar a Afrika ta kudu a shekarar 2010.
Spain ba ta yi rashin nasara ba a wasanni 11 da ta ƙara da Belgium (ta ci guda tara an kuma yi canjaras biyu) Belgium za ta yi fatan cewa tarihi zai maimaita kansa shekara 40 bayan lokacin da ta doke Spain a bugun fenariti a zagayen kwata-fainal ɗin gasar Mexico '86.