Waɗanne ƙasashe ne suka mallaki jiragen yaƙin zamani ƙirar F-35?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce za a iya ɗage takunkumin da aka sanya wa Turkiya kan sayen makaman yaƙi.

Trump ya faɗi hakan ga ƴan jarida gabanin wata ganawa da zai yi da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdoğan, a birnin Ankara.

Amurka ta ƙaƙaba mata takunkumin ne a watan Disambar 2020 bayan da Turkiya ta sayi makaman tsaron sararin samaniya na S-400 daga Rasha.

Trump ya ce za su sake nazari kan mallakar jiragen yaƙi na F-35 da Turkiya ke son yi. Turkiya na cikin waɗanda suka taka rawa wajen ƙera jiragen F-35.

Sai dai saboda wannan dalilin ne ya sa aka cire ta daga shirin ƙera jiragen.

Sakamakon haka ne, Turkiya ke son yin watsi da na'urorin S-400 domin su samu damar komawa cikin shirin F-35.

Me ya sa jirgin yaƙi ƙirar F-35 ya fita daban?

Jirgin yaƙi na F-35 ƙirar zamani ne da ke da matukar sauri, kuma an ƙera shi domin gudanar da ayyukan yaƙi iri-iri ta hanyar amfani da fasahohi na zamani, ciki har da tsarin amfani da basirar AI da kuma aika bayanai cikin gaggawa.

Jirgin na iya yin gudun kusan kilomita 1,900 a sa'a guda, amma kuma abin da ya sa ya fita daban da sauran jiragen yaƙi shi ne ƙarfinsa na gano idan an kai hari da kai farmaki da kuma tattara bayanai, sannan ya tura su ga sauran jiragen yaƙi domin daƙile farmakin.

Ana ganin wannan fasaha na ƙara wa sauran jiragen yaƙi da ke aiki tare da shi ƙarfi a lokacin yaƙi. An ƙera F-35 da fasahar da zai yi wahalar ganowa ta na'urorin sanya ido a sararin samaniya, abin da ya sa ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin jiragen yaƙi mafi ci gaba a duniya.

Farashin jirgin guda ya kai kusan dalar Amurka miliyan 80, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin jiragen yaƙi mafi tsada a duniya.

Rundunar Sojin Sama ta Amurka ta ce jirgin F-35A na iya shawagi a ƙololuwar samaniya, wanda ke bai wa matuƙinsa damar sarrafa shi yadda yake so a sararin samaniya.

A halin yanzu, shirin ƙera jiragen F-35 shi ne shiri mafi girma kuma mafi tsada cikin shirye-shiryen ƙera makaman soja a duniya, kuma ana sa ran zai ci gaba na tsawon shekaru 30 zuwa 40.

Sai dai rahoton gwajin Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) da aka fitar a watan Nuwamban 2024 ya nuna akwai ƙalubale, ciki har da jinkirin samar da jirgin, daidaita shi da wasu makaman da ake ƙerawa, da kuma ƙarfin tsarin kariyarsa daga hare-haren intanet.

Waɗanne ƙasashe ne suka mallaki jiragen yaƙin F-35?

Bisa bayanan shirin ƙera jiragen F-35, ana sa ran nan da shekarar 2030 za a samu sama da jiragen F-35 guda 550 a nahiyar Turai.

Baya ga Amurka, akwai wasu ƙasashe 19 da suka mallaki jiragen F-35 ko kuma suka ba da odar sayensu.

Ƙasashen da suke cikin shirin ƙera jirgin F-35 sun haɗa da Amurka, Birtaniya, Italiya, Netherlands, Canada, Australia, Denmark da Norway.

Ƙasashen da suka riga suka karɓi jiragen F-35 sun ne:

  • Amurka
  • Birtaniya
  • Italiya
  • Netherlands
  • Norway
  • Australia
  • Japan
  • Koriya ta Kudu
  • Isra'ila
  • Denmark
  • Belgium
  • Poland

Akwai kuma ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar saye, kuma ake sa ran za su fara karɓar jiragensu cikin shekaru masu zuwa da suka haɗa da:

  • Jamus
  • Kanada
  • Finland
  • Switzerland
  • Singapore
  • Greece
  • Czech Republic
  • Romania

Me ya sa aka cire Turkiya daga shirin ƙera jiragen F-35?

Turkiya ta shiga shirin ƙera jirgin yaƙi na F-35A Lightning II a shekarar 2002, ƙarƙashin shirin Joint Strike Fighter (JSF). Kamfanin Lockheed Martin, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin ƙera makamai a duniya ne ke jagorantar shirin.

Ƙasashen da suka shiga shirin sun haɗa da Turkiya, Amurka, Birtaniya, Italiya, Netherlands, Australia, Denmark, Kanada da Norway.

Turkiya ta yi odar jiragen F-35 guda 100 domin ƙarfafa rundunar sojin samanta, sannan kamfanoninta suna aikin ƙera wasu sassan jirgin.

Tsohon Ministan Tsaron Turkiya, İsmet Yılmaz, ya bayyana a shekarar 2014 cewa jimillar kuɗin sayen jiragen za ta kai dala biliyan 25.

A shekarar 2018, an miƙa izinin mallakar jiragen F-35 guda huɗu ga Turkiya. Sai dai jiragen sun ci gaba da kasancewa a Amurka domin gudanar da horo, inda matuƙan jiragen Turkiya ma suka shiga shirin horaswar.

Daga baya, an sake miƙa wasu jiragen F-35 guda biyu ga Turkiya, inda suka zama shida.

Sai dai wasu 'yan majalisar dokokin Amurka sun fara yunƙurin dakatar da sayar wa Turkiya jiragen F-35 da sauran kayan aikin soja.

Dalilan da suka bayar sun haɗa da abin da suka kira koma baya ga dimokuraɗiyya a Turkiya, bayan tsare wasu 'yan ƙasar Amurka, da kuma sayen na'urar kariyar sararin samaniya ta S-400 daga Rasha.

A watan Agustan 2018, shugaban Amurka a wancan lokaci, Donald Trump, ya sanya hannu kan dokar da ta dakatar da miƙa jiragen F-35 ga Turkiya.

Daga bisani ba a kai wa Turkiya jiragen guda shida da ta mallaka ba, kuma aka cire ta gaba ɗaya daga shirin F-35.

A watan Disamban 2020, Amurka ta sanar da cewa ta samo wasu sabbin kamfanoni da za su maye gurbin Turkiya wajen ƙera sassa 1,005 na jirgin da kamfanonin Turkiya ke samarwa a baya.

Bayan an cire Turkiya daga shirin, jiragen F-35 da ta saya sunb ci gaba da kasancewa a Amurka, ba tare da an miƙa su ga rundunar sojin saman Turkiya ba.

Turkiya ta riga ta biya Amurka dala biliyan 1.7 domin sayen jiragen F-35A guda shida.