Ƴan ƙwallo biyar da burinsu na lashe Kofin Duniya ya dusashe a gasar bana

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka a wasansa na ƙarshe na kofin duniya a ranar Litinin yayin da burinsa na lashe kyautar mafi girma ya ƙare da rashin nasara a hannun Spain da ci 1-0.

Kyaftin ɗin Portugal mai shekaru 41 kuma ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa na duniya ya ce yanzu zai tafi ya yi tunanin abin da zai biyo baya.

Ya lashe duk wata kyauta da ƴan ƙwallo ke da burin lashewa ya kuma taka leda manyan ƙungiyoyin Turai.

Amma baya ga Christiano Ronaldo akwai fitattun ƴan wasa da suka taka leda a matakin duniya suka kuma lashe kyaututtuka da dama amma suka kasa lashe kofin duniya musamman ganin yadda aka yi waje da tawagogin ƙasashensu daga gasar bana, kuma ana kyautata zaton cewa ba za su sake dawowa su fafata a gasar nan da shekara hudu masu zuwa ba.

Wasu daga cikinsu ma sun riga sun sanar da cewa wannan ita ce gasar kofin duniyarsu ta ƙarshe.

Cristiano Ronaldo - Portugal

Zaman Ronaldo a gasar bana ya ƙare ne a ranar Litinin bayan da Portugal ta sha kashi a hannun Spain da ci 1-0. Tauraron ɗan wasan Portugal yana da shekaru 21 lokacin da ya fara buga gasar cin kofin duniya. Wannan gasar ta kasance ta shida - wani abin da shi da Lionel Messi na Argentina kaɗai suka iya yin hakan.

Yayin da yake da shekaru 41, Ronaldo shi ne ɗan wasa na biyu mafi tsufa a gasar cin kofin duniya ta wannan shekarar. Duk da haka, ya zura kwallaye uku - wanda ya tabbatar da cewa har yanzu yana da rawar da yake iya takawa a fagen ƙwallon ƙafa na duniya.

Yanzu ya koma gida ba tare da ya lashe kambun gasar cin kofin duniya ba.

Fitaccen ɗan wasan na Portugal ya shafe shekaru sama da ashirin, yana hankoron lashe kofi ɗaya da ya bayyana a fili a matsayin babban burinsa. Bayan gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022, Ronaldo ya yarda cewa ɗaga kyautar da ya fi so a ƙwallon ƙafa ita ce "burinsa mafi girma."

Wannan mafarkin ya ƙare yanzu, kuma bisa ga dukkan alamu kambun gasar cin kofin duniya ya kuɓuce wa ɗaya daga cikin manyan fitattun ƴan wasan kwallon ƙafa na duniya, wanda za a dade ba a manta rawar da ya taka wajen nishadantar da masoya kwallon kafa ba.

Neymar - Brazil

Burin Neymar na lashe gasar kofin duniya ya ƙare cikin baƙin ciki yayin da tauraron na Brazil ya fashe da kuka bayan da Norway ta fitar da zakarun gasar kofin duniya sau biyar a zagaye na ƴan16 a filin wasan New York New Jersey.

Hotunan da aka nuna a talabijin sun nuna Neymar yana kuka ba kakkautawa bayan kayen da Brazil ta sha da ci 2-1. Wannan hoto ya zame mai tayar da hankali, ba wai kawai saboda Brazil ta fice daga gasar cin kofin duniya ba, amma saboda wataƙila wannan shi ne lokaci na ƙarshe da za a ga Neymar a babban matakin ƙwallon ƙafa.

Baya ga zama babban ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil, Neymar ya ci ƙwallo sama da 100 a ƙungiyoyi uku daban-daban: Santos, Barcelona da Paris Saint-Germain.

Tsohon ɗan wasan Brazil Romario da Cristiano Ronaldo ne kawai suka cimma irin wannan bajinta a ƙwallon ƙafa ta zamani ta maza, amma Neymar shi ne na farko da ya yi hakan a nahiyoyi uku daban-daban.

Neymar ɗan wasa ne mai matuƙar baiwa inda ya lashe kofunan lig a Spain da Faransa da kuma lashe gasar zakarun Turai ta UEFA a 2015.

Luka Modric - Croatia

Luka Modric da Croatia sun sha kashi a gasar cin kofin duniya ta 2026 a hannun Portugal. Wannan rashin nasarar nan take ta haifar da rashin tabbas game da makomar shahararren ɗan wasan ƙwallon kafa na duniya mai shekara 40.

Amma, kamar yadda ya ambata kafin gasar cin kofin duniya, hakan ya tabbatar da ritayar Luka Modri daga taka wa Croatia leda, bayan ya tabbatar da matsayinsa na gwarzon ɗan wasa a tarihin ƙwallon kafa wanda ya taimaka wa Real Madrid ta mamaye fagen ƙwallon ƙafa a Turai, kuma ya jagoranci Croatia zuwa ƙololuwar fagen ƙwallon ƙafa na duniya.

Bayan zaman da ya yi a Real Madrid inda ya lashe kyautuka dama da kuma zaman da ya yi a AC Milan a kakar wasa da ta gabata, Modric ya yanke shawarar rataye takalmansa a hukumance.

Modric wanda nan ba da jimawa ba zai cika shekaru 41 ya lashe manyan kofuna da dama a lokacin da yake taka leda a Real Madrid.

Shi ne wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2018 wanda ya karya mamayar da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suka yi wa kyautar na tsawon shekaru 10.

Ya lashe gasar zakarun Turai sau shida, kuma ya lashe manyan kofuna 28, wanda ya sanya ya zama ɗan wasa mafi lashe kyautuka da ya taɓa saka rigar Real Madrid.

Riyad Mahrez - Algeria

Riyad Mahrez ya sanar da yin ritaya daga buga wa Algeria wasa bayan da Algeria ta sha kashi a hannun Switzerland da ci 2-0 a zagayen ƴan 32 na gasar cin kofin duniya ta 2026.

Tsohon ɗan wasan gefen Manchester City ya bayyana cewa ya shafe shekaru 12 yana buga wa ƙasarsa wasa, wanda ya haɗa da lashe gasar kofin nahiyar Afrika (AFCON).

Mahrez ya sanar da hakan ne a lokacin da yake magana da kafar yada labarai ta beIN SPORTS bayan da aka fitar da Algeria daga gasar. Dan wasan gefen ya ce rashin nasarar da aka samu a gasar cin kofin duniya ya kawo ƙarshen wasansa na ƙasa da ƙasa bayan shafe fiye da shekara 10 yana wakiltar ƙasarsa inda ya buga wasa 119.

Babbar nasarar da Mahrez ya samu da Algeria ta zo ne a shekarar 2019 lokacin da ya jagoranci ƙasarsa wajen lashe gasar cin kofin Afirka. Nasarar ta tabbatar ƙasar ta lashe kofin nahiyar a karo na biyu a tarihin gasar.

Tsawon shekaru 12 da ya kwashe yana tare da tawagar ƙasar, Mahrez ya kafa kansa a matsayin babban jagora, kuma ritayarsa ta kawo ƙarshen wani zamani mai cike da nasara ga ɓangaren ƙwallon ƙafar Algeria.

Edin Dzeko - Bosnia

Ƴan wasa ƙalilan ne kawai za su iya goga kafaɗa da ɗan wasan Schalke Edin Džeko ta fannin cin ƙwallaye.

Ɗan wasan dai ya murmure daga raunin da ya yi fama da shi ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da matsayin ƙasarsa a gasar.

Džeko, ɗan wasan Bosnia mafi hazaka da yawan zura ƙwallaye, ya shafe shekara 20 yana taka leda a matakin mafi girma a fagen ƙwallon ƙafa a duniya.

Ɗan wasan mai shekaru 40 ya nuna cewa har yanzu yana iya buga wasa a matakin mafi girma. Ikonsa na sarrafa ƙwallo da iyawarsa ta neman sarari da kuma iya zura ƙwallaye sun kasance masu mahimmanci ga cancantar shigar ƙasarsa gasar cin kofin duniya ta bana.

Dzeko, wanda ya buga wa tawagar ƙasarsa wasa 148, ya buga wasanni bakwai daga cikin takwas da ƙasarsa ta yi a rukunin H na neman gurbin shiga gasar ta bana.

Ƙwallo 65 da ya ci sun tabbatar da shi a matsayin ginshiki a tarihin ƙwallon ƙafa na ƙasarsa.

tasirin da ya yi a manyan gasannin Turai daban-daban - a Jamus da Ingila, da Italiya - ya nuna cewa yana da ƙwarewa wadda ƴan wasa ƙalilan ne daga cikin takwarorinsa na yankin za su iya gogayya da shi.