Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne bambancin shugabannin Iran na yanzu da waɗanda aka kashe?
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran a Faransa, cikin watan da ya gabata, wasu sun kalli abin tamkar wata almara.
Tabbas mai masaukin baƙi, shugaban Faransa Emmanuel Macron zai so a hanzarta sanya hannu kan yarjejeniyar kafin Donald Trump ya canza ra'ayi.
To amma zaɓen wurin da za a sanya hannu kan yarjejeniyar, wato fadar Versailles da kusa da birnin Paris ya sanya ana kwatanta wannan ƴar gajeriyar yarjejeniya da kuma yarjejeniyar da aka yi wa laƙabi da Yarjejeniyar fadar Versailles, wadda aka sanya wa hannu a shekarar 1919 a ƙarshen yaƙin duniya na ɗaya.
Yarjejeniyar ta 1919 ita ce ta sauya nahiyar Turai, sai dai buƙatar ƙasashen Turai na samun diyya ta baƙanta wa Jamus rai da kuma haifar da gaba na tsawon shekara 20.
Shin ko makomar yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran za ta yi daya da wadda aka sanya wa hannun a baya?
Kimanin mako uku bayan yarjejeniyar mai rauni, har yanzu akwai alamun tana aiki.
To amma bayan bayan rikita-rikitar da aka samu a Mashigar Hormuz, da kuma ganin cewa har yanzu an kasa warware ko da ɗaya daga cikin matsalolin da suka haifar da yaƙin, da alama har yanzu akwai sauran rina a kaba game da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.
Yanzu Iran na tsakiyar gagarumin sauyi.
Ƙasar tana ban-kwana da tsohon jagoranta, Ayatollah Ali Khamenei wanda aka kashe kimanin wata huɗu da suka gabata sanadiyyar hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa ƙasar, wanda ya shafe shugabanninta.
Wani lokaci ne mai matuƙar muhimmanci: wata alama da ke nuna cewa tsoffin jagorori sun kau, yayin da sabbi suka karɓi ragama.
Kuma yayin da ake samun sabbin jagorori, za a samu sabon tsarin tafiyar da gwamnati, kuma hakan na da nasa tasirin.
Lallai Amurka ta kashe da dama daga cikin jagororin Iran, to amma ko ta samar da sabbin abokan gaba kenan?
Sabon salo
"Wannan yaƙin yana da matuƙar tasiri fiye da yadda muke gani a halin yanzu," in ji Vali Nasr, farfesa kan harkokin ƙasashen ƙetare da Gabas ta Tsakiya a sashen ilimin hulɗodin ƙasashen ƙetare a jami'ar John Hopkins.
"Duk wani yaƙi mai tasiri kamar wannan yana kawo sabbin sauye-sauye," in ji shi. Ya ƙara da cewa "wannan yaƙin zai sauya lamurra a Gabas ta Tsakiya."
A watan Janairu da ya gabata Iran ta yi fama da mummunara zanga-zanga wadda Shugaba Trump da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu suka yi hasashen cewa za ta kai ga durƙushewar gwamnatin ƙasar.
Tattalin arziƙin Iran ya lalace tsawon gomman shekaru sanadiyyar takunkumai. Haka nan an yi wa ƙasar mummunan rauni bayan yaƙin kwana 12 da aka gwabza tsakaninta da Amurka da Isra'ila watanni shida baya.
Shirin nukiliyar Iran, wanda shi ne ake ta takun saƙa a kansa, ba a lalata shi ba kamar yadda Trump ya yi ikirari, amma an yi masa illa.
Babu tabbas kan inda Iran ta taskace tarin sinadarin Yureniyom (uranium) da ta inganta wanda za a iya haɗa makaman nukiliya 10 zuwa 11 idan aka ƙara masa inganci, sai dai ana tsammanin yana ƙarƙashin ɓaraguzai a kusa da cibiyar nukiliya ta Isfahan.
A wani ɓangaren kuma, ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran, waɗanda suke a yankin Gabas ta Tsakiya, sun fuskanci koma-baya.
A Syria, an kawar da gwamnati mai ƙawance da Iran ƙarƙashin Basar al-Assad a ƙarshen shekarar 2024.
A Lebanon, Isra'ila ta kashe manyan jagororin ƙungiyar Hezbollah sannan ta kashe manyan mayaƙanta ta amfani da wayar salula.
A Gaza, Hamas ma ta ji jiki. Isra'ila ta mayar da mummunan martani bayan harin da ƙungiyar ta kai wa Isra'ila a watan Oktoban 2023, inda ta lalata yankin Gaza tare da kashe dubun dubatar fararen hula.
A lokacin da mayaƙan Houthi na Yemen suka fara kai wa Isra'ila hari da miyagun makamai da kuma kai farmaki kan jiragen ruwa a tekun Maliya, Amurka da Birtaniya da Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare na ramuwar gayya a kan ƙungiyar da shugabanninta.
Bayan koma-baya a gida da waje, ana da yaƙinin cewa Iran ta yi rauni. Jaridar New York Times ta ruwaito cewa Donald Trump ya samu bayanan sirri da ke cewa Iran ta yi rauni sosai fiye da kowane lokaci tun bayan juyin juya hali na shekarar 1979.
Tunanin cewa ƙasar za ta iya yin galaba a kan Amurka da Isra'ila tamkar mafarki ne.
To amma kusan abin da ya faru kenan. An kasa durƙusar da Iran, wani abu da ya taka muhimmiyar rawa shi ne yadda ƙasar ke da ikon datse ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya, wato Mashigar Hormuz, lamarin da ya shaƙe tattalin arzikin duniya.
Shin Iran ce a sama?
Trump na yawan cewa ya kawo sauyin gwamnati a Iran. Vali Nasr bai yadda da hakan ba, ya ce a maimakon hakan, Iran ta ƙara ƙarfi ne.
“Yanzu an samu sabbin jini sun karbi jagoranci,“ in ji shi.
“Manufarsu a bayyane take karara. Sun tafiyar da kasar lokacin yaki kuma za su tafiyar da ita a lokacin zaman lafiya.”
Sabbin jagororin Iran ba irin wadanda Amurka ta sani ba ne, wadanda take kira “marasa tunani masu son halakar da duniya”, in ji Nasr, wadannan mutane ne da suka mayar da hankali kan dorewar kasar kuma za su iya daukar duk matakin da suka ga ya dace nan take fiye da magabatansu.
A shekara 56, jagoran addini na kasar Mojtaba Khamenei na da bambancin shekaru 30 tsakaninsa da mahaifinsa marigayi Ali Khamenei, wanda a bayyane take tsufa ta ci karfinsa gabanin kashe shi a farkon yaki.
Shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya girmi Mojtaba, shekarunsa 70, to amma daukacin mutanen da suka aiwatar da juyin-juya halin shekarar 1979 sun shude.
Wasu ginshikai a kasar, shugaban majalisar dokokin kasar kuma babban mai wakiltar Iran wajen cimma yarjejeniya Mohammed Bagher Ghalibaf da kuma shugaban rundunar juyin juya-hali ta kasar Ahmad Vahidi, dukkaninsu shekarunsu 60 da ‘yan kai.
Kamar jagoran addini na kasar, dukkaninsu suna da hulda ta kut da kut da dakaru na musamman na rundunar juyin juya hali na kasar (IRCG).
“Juyin juya-hali ne ya haife su,“ in ji Sanam Vakil, shugaban sashen nazarin yankin Gabas ta tsakiya da arewacin Afirka a Chatham House da ke birnin Landan.
“Yanzu ba dan shekara 86 ne ke jan ragamar Jamhuriyar Musulunci ba. Ali Khamenei ne turke da ya hana sauyawar tsarin.”
A tsawon gomman shekaru Khamenei ya yi amfani da dabarar “babu yaki, kuma babu zaman lumana.” Magadansa sun fi nuna karfin hali, sun kaddamar da hare-hare kan sansanonin Amurka a fadin yankin, sannan bayan makonni kadan suka amince su hau kan teburin tattaunawa bisa sharuddan da babu yadda za a yi a ce Iran ta ji kunya.
“Sun nuna cewa a shirye suke a tattauna gaba-gadi, da karfin gwiwa fiye da na wadanda suka gabace su,“ in ji Nasr.
Lokacin da Trump ya bayar da umarnin kai harin da ya kashe kwamandan rundunar juyin juya hali Qasem Soleimani a shekarar 2020, Iran ta aika sakon niyyarta ta daukar fansa kafin harba makamanta masu linzami 12 a kan sansanonin Amurka a Iraq.
Ba a kashe sojan Amurka ko daya ba.
A wannan shekarar Iran ba ta yi irin wannan taka tsantsan ba sa’ilin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hari a kanta, inda kasar ta mayar da maryani ta hanyar kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan sansanonin sojin Amurka da dama a fadin yankin, ciki har da manyan sansanonin kasar a Bahrain da Qatar.
An kashe sojojin Amurka shida a Kuwait sannan an raunata daruruwa a lokacin yakin.
Karfin halin Iran na kai farmaki kan kawayen Amurka a yankin Gulf da datse Mashigar Hormuz - wata hanyar sufurin jiragen ruwa mai matukar muhimmanci - kuma abin da ya bai wa fadar shugaban Amurka mamaki.
A tsawon gomman shekaru Amurka ta yi ta bin hanyoyin tsoratar da Iran ta hanyar karfafa sansanoninta da kuma huldar dangantaka da kasashen yankin Gulf.
Matakin da Iran ta dauka na mayar da martani kan hare-haren Amurka da Isra’ila ya nuna cewa a yanzu dabarar ta Amurka ba za ta yi aiki ba.
”Da dama daga cikin kasashen na yankin Gulf sun yi tsammanin cewa sansanonin sojin Amurka da ke cikinsu za su zamo masu garkuwa, ba su janyo musu hare-hare ba,” in ji Ali Vaez, daraktan da ke kula da sashen Iran a kungiyar International Crisi Group.
“A halin yanzu kasashen Gulf na tababa kan kariyar da suka yi tsammani daga Amurka da kuma dabarunsu na hana kai musu farmaki.
Rahotanni na nuna cewa da yawa daga cikin kasashen yankin Gulf a yanzu na kokarin ganin yadda za su gyara alakarsu da makwafciyarsu.
Ga Iraniyawa, wannan yaki ya ruda su. Tsoron da suke yi na zaluncin gwamnati ya kau sa’ilin suka fada cikin wani taoron lokacin da Isra’ila da Amurka suka rika yi ruwan bama-bamai a kan kasar, inda suka kashe fararen hula da kuma lalata cibiyoyi masu muhimmanci.
Kashe dalibai da dama a makarantar Minab a ranar farko ta yakin ya sanya wasu sun fara tunanin shin wane ne babban azzalumi tsakanin gwamnatin kasar fa kasashen da ke kai masu farmaki.
Bayan sun yi alkawarin ceto su, abin da ya bayyana a fili shi ne manufar Amurka da Isra’ila ita ce su wargaza kasar.
To amma bayan dagewar da gwamnatin kasar ta yi wajen yin fito na fito da kasashen Amurka da Isra’ila, ko jagororin kasar za su yi amfani da wannan lamari wajen wanke kansu a idon al’umma?
Yayin da take sa ran za a dage mata takunkumai domin ta jingine shirinta na nikiliya, idan har gwamnatin kasar ta iya tafiyar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, kila hakan ya sanya ta dawo da kimarta a cikin gida.
Tun bayan sanya hannu ka yarjejeniyar, Iran ta amfana da jingine wasu takunkuman Amurka da ke kanta, inda aka bar ta, ta fitar da danyen man fetur tsawon kwana 60.
Akwai alamun za ta kara samun sauki a cikin kwanaki 60 na yarjejeniyar, ciki har da batun sakar mata kudinta da aka rike na biliyoyin daloli, sannan kuma idan aka cimma babbar yarjejeniyar a dage mata dukkanin takunkuman da ke kanta.
Yarjejeniyar da aka cimma ta kunshi wani shirin sake gina kasar da ya kunshi kudi dala biliyan 300, duk da har yanzu babu tabbas kan ko wane ne zai samar da kudin.
Wannan tayi mai tsoka ana ganin zai kwadaita wa shigabannin Iran karfin gwiwa domin cimma babbar yarjejeniya.
Babu wani daga cikin masu sharhin da zai iya cewa ga takamaiman makomar Iran.
Gomman shekaru da aka kwashe na sabani tsakanin Iran da makwaftanta na yankin Gulf da kuma Amurka, ya bar mummunan tasiri, wanda ya haifar da rashin aminci da kuma zargin juna.
Akwai abubuwa da dama da za su iya yin kafar-ungulu: rashin samun matsaya kan makomar shirin nukiliyar Iran, makomar Mashigar Hormuz, rikicin kasar Lebanon da kuma ra’ayin masu ra’ayin rikau.
Bayan wata shida na rikici, yanzu yankin ya fara sauyawa. To amma dole sai an gyara abubuwa da dama kafin a cimma wani abin a zo a gani.