Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohin Najeriya da za a iya samun ambaliyar ruwa a wannan mako
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (Nimet) ta yi gargaɗin cewa ruwa mai ƙarfi na barazanar haifar da ambaliyar ruwa a jihohin ƙasar da dama daga farkon watan Yuli zuwa 10 ga watan.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, hukumar ta ce ruwan sama da aka samu a sassan ƙasar cikin watan Yuni ya sa ƙasa ta ɗuri ruwa sosai, kuma hakan zai rage yadda ƙasa ke tsotse ruwan sama da zai ci gaba da sauka a wannan wata.
Hukumar ta ce "saboda haka, yankunan da ke a wuri mai kwari da birane da wuraren da ke kusa da rafuka da kuma wuraren da babu isassun magudanan ruwa za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a cikin kwanaki masu zuwa."
Najeriya na da tarihin ambaliyar ruwa mai muni a sassa daban-daban na ƙasar.
A makonnin da suka gabata ma wasu biranen yammacin Afirka sun yi fama da matsalar ambaliyar ruwa, wadda ta yi sanadiyyar rayuka da dukiyoyi.
A Accra da ke Ghana an tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 13 yayin da mutane da dama suka mutu a Ivory Coast sanadiyyar mamakon ruwa.
Waɗanne jihohi ne ke cikin háɗarin ambaliya?
Sanarwar da hukumar Nimet ta fitar ya bayyana cewa jihohi da dama, daga kudanci zuwa arewacin ƙasar na cikin hadarin ambaliyar ruwa:
Arewa: Taraba, Sokoto, Borno, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Nasarawa, Plateau, Adamawa, Kwara da Kogi.
Kudu: Oyo, Ogun, Lagos, Osun, Ekiti, Delta, Edo, Abia, Imo, Anambra, Enugu, Akwa Ibom, Cross River, Rivers da Bayelsa.
Matsalolin da ambaliyar za ta haifar
Hukumar ta Nimet ta yi gargaɗin cewa ambaliyar za ta iya haifar da matsaloli daban-daban, wadanda suka hada da:
- Hana zirga-zirga
- Katsewar lantarki
- Lalata hanyoyi da gadoji
- Lalata amfanin gona
- Ƙaruwar hatsarin kamuwa da cutuka
Yadda za ku kare kanku a lokacin ambaliya
Ƙwararru sun zayyana abubuwan da ya kamata a yi idan ambaliya ta faru:
- Idan akwai barazana ga rayuwar wani ko wata, to a gagguta kiran lambobin agajin gaggawa domin samun ɗauki
- Kada ku yi tafiya ko tuƙi cikin ruwan da yake ambaliya ko kuma neman shiga cikin ruwan domin tsallakewa. Ruwan yana zuwa da ƙarfin gaske ta yadda zai iya janye mota.
- Kada a yi tafiya a kan katangar da ta kange rafi, ko kuma a gaɓar rafin
- A guji duk wani abu da zai a shiga cikin ruwan da ke ambaliya domin kuwa zai iya yaɗa cutuka. Idan kuma har aka taɓa ruwn, to a gaggauta wanke hannu ko wajen da ruwan ya taɓa da ruwa mai tsafta.
- Kada a bari ƙananan yara su yi wasa a kusa da wajen da ake mbaliya.
Yadda ruwan sama mai ƙarfi ke janyo ambaliya
Idan rafi zai yi ambaliya, yana ɗaukar lokaci yana nuna alama saboda a hankali yake cik har ya shanye gaɓar da aka tsara tare ruwan rafin.
Amma idan ruwan sama ne ya haddasa ambaliyar, tana faruwa ne cikin ƙanƙanin lokaci daga fara ruwan saman zuwa lokacin da wurare za su cika nhar a samu ambaliyar.
Hukumar hasashen yanayi ta Birtaniya ta ce "Ambaliyar ruwa ta fi faruwa a wuraren da rafi baya da faɗi sosai, yanayin da ke bai wa ruwa damar kwarara cikin sauri. Tana kuma faruwa a ƙananan ƙoramu da a gefen su akwai ko dai titin mota da aka yiwa kwalta, ko ginin kankare musamman a birane, inda yake da wahalar gaske a samu ƙasar wajen ta shanye ruwan da ya kwararo.''
Ta ƙara da cewa "A haka ne sai ruwan ya ci ƙarfin magudanan da aka yi, har ya yi ambaliya.''
Shuka bishiyoyi da ciyawa na taimakawa sosai wajen hana ambaliya, musamman a birane domin kuwa suna tsotse ruwan.