Manyan zaɓaɓɓun kujeru da mata suka riƙe a mulkin Najeriya

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja.
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Duk da kusan shekara 25 da aka yi ana mulkin dimokuraɗiyya a jere a Najeriya, har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan irin rawar da mata suke takawa a siyasar ƙasar, musamman samun damar riƙe madafun iko.

Zuwa yanzu dai za a cewa babbar kujerar siyasa a Najeriya da mace ta riƙe ita ce shugabar majalisar wakilai a zamanin Patricia Eteh.

Haka kuma an samu mata kusan 20 da suka yi mataimakan gwamnoni a jihohi daban-daban a faɗin ƙasar, har ma aka samu wadda ta ɗare kujerar gwamna bayan an tsige gwamnan jihar.

Haka kuma akwai mata da suka riƙe shugabanni a majalisar wakilai, sannan akwai waɗanda suka zama sanatoci, kamar marigayiya Aisha Alhassan.

A watannin baya ne gamayyar ƙungiyoyin mata masu kaɗa ƙuri'a a ƙarƙashin ƙungiyar Nigerian League of Women Voters (NILWV) ta miƙa takardar ƙorafi ga majalisar dokokin ƙasar, inda suka yi kira da a ware wa mata wasu kujeru na musamman a Najeriya.

Shugabar majalisar wakilai

A matakin tarayya, zuwa yanzu za a iya cewa macen da ta riƙe kujera mafi girma a tsarin mulkin Najeriya ita ce Patricia Etteh.

Ta kasance shugabar majalisar wakilan Najeriya daga Yuni zuwa Oktoban shekarar 2007 kafin aka cire ta.

Patricia Olubunmi Foluke Etteh, ta kasance ƴar majalisa cem ai wakiltar mazaɓar Ayedaade/Isokan/Irewole ta jihar Osun.

Shugabanni a majalisar wakilai

Ita ma Mulikat Akande ta taɓa babban matsayi a majalisar wakilan ƙasar, inda ta zama shugabar masu rinjaye a shekarar 2011.

Ta wakilci mazaɓar Ogbomoso North/South/Orire na jihar Osun daga 2007 zuwa 2015.

Akwai kuma Nkeiruka Onyejeocha da ta zama mataimakiyar mai tsawatarwa a majalisar ta 9, da kuma Oriyomi Onanuga ita ma ta riƙe muƙamin mataimakiyar mai tsawatarwa majalisar ta 10.

Gwamnar jihar Anambra

Mace ta farko da ta zama gwamna ita ce Dame Virginia Ngozi Etiaba, wadda ta zama gwamnar jihar Anambra daga Nuwamba 2006 zuwa Fabrairu 2007.

Ta ɗare kujerar mulkin ne bayan an tsige gwamnan jihar Peter Obi.

Sai dai daga baya, kotun ta soke tsigewar, wanda hakan ya sa aka mayar masa da kujerarsa.

Mataimakiyar gwamnan Filato

Pauline Tallen tsohuwar ministar harkokin mata ce daga shekarar 2019 zuwa 2023, sannan ta taɓa yin minista a shekarar 1999 a zamanin Olusegun Obasanjo.

A shekarar 2007, ta zama mataimakiyar gwamnan jihar Filato, inda ta kasance mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami a arewacin Najeriya.

Ta kuma tsaya takarar gwamnan Jihar Plateau a shekarar 2011, amma ta sha kaye a hannun Jonah David Jang.

Mata huɗu mataimakan gwamnan Legas

Akwai jihar Legas, wadda daga shekarar 1999 zuwa yanzu ta yi mataimakan gwamna mata guda huɗu: Oluranti Idiat Adebule daga 2015 zuwa 2019 da Adejoke Orelope-Adefulire daga 2011 zuwa 2015 da Sarah Adebisi Sosan daga 2007 zuwa 2011 da Kofoworola Akerele-Bucknor daga 1999 zuwa 2003.

Haka kuma yanzu APC ta tsayar da Damilola Sonayon-James a matsayin wadda za ta yi takarar mataimakiyar gwamnan jihar domin tsayawa takara tare da mataimaki na yanzu, Obafemi Hamzat.

Haka kuma akwai Alhaja Sinatu Aderoju Ojikutu wadda ta riƙe mataimakiyar gwamna a jihar Legas daga 1992 zuwa 1993.

Wasu matan da suka yi mataimakan gwamna sun haɗa da:

  • Stella Odife – Jihar Anambra.
  • Ada Okwuonu – Jihar Imo.
  • Salmot Badru – Jihar Ogun.
  • Erelu Olusola Obada – Jihar Osun.

Matan da suke riƙe da muƙamin mataimakan gwamna a yanzu

  • Hadiza Balarabe – Jihar Kaduna
  • Akon Eyakenyi – Jihar Akwa Ibom
  • Josephine Piyo – Jihar Plateau
  • Ngozi Nma Odu – Jihar Rivers
  • Noimot Salako- Jihar Oyedele – Ogun
  • Patricia Obila – Jihar Ebonyi
  • Christiana Monisade Afuye – Jihar Ekiti
  • Chinyere Ekomaru – Jihar Imo
  • Kaletapwa Farauta – Jihar Adamawa

Mata shigabannin majalisun jiha

Zuwa yanzu mata 9 ne suka taɓa zama shigabannin majalisar dokokin jiha tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a 1999.

Jihar Anambra ce ta fi kowace jiha yawan matan da suka riƙe wannan muƙami, inda mata uku suka jagoranci majalisar.

Margaret Icheen ta Jihar Benue ita ce mace ta farko da ta zama shugabar majalisar dokokin jiha bayan dawowar dimokuraɗiyya, daga 1999 zuwa 2003.

Mojisola Meranda ta Jihar Legas ita ce mace ta baya-bayan nan da ta zama jagoranci majalisar Legas a shekarar 2025.

  • Margaret Icheen – Jihar Benue (1999–2003)
  • Eucharia Azodo – Jihar Anambra (2003)
  • 3Titi Oseni-Gomez – Jihar Ogun (2003–2008)
  • Chinwe Nwaebili – Jihar Anambra (2011)
  • Monsurat Jumoke Sunmonu – Jihar Oyo (2011)
  • Jumoke Akindele – Jihar Ondo (2014)
  • Rita Mmaduagwu – Jihar Anambra (2015)
  • Olubunmi Adelugba – Jihar Ekiti (2022)
  • Mojisola Meranda – Jihar Legas (2025)

Zaɓaɓɓun kujeru a mulkin Najeriya

A matakin tarayya:

  • Shugaban ƙasa
  • Mataimakin shugaban ƙasa
  • Sanata (Akwai shugaban majalisar dattawa da mataimaki)
  • Majalisar wakilai (Akwai shugaban majalisar wakilai da mataimaki)

A matakin jihohi kuwa akwai:

  • Gwamna
  • Mataimakin gwamna
  • Majalisa (Akwai shugaban majalisar dokokin jiha da mataimaki)

A matakin ƙananan hukumomi kuma akwai:

  • Shugaban ƙaramar hukuma
  • Mataimakin shugaban ƙaramar ukuma
  • Kansiloli (Akwai shugaban majalisar ƙaramar hukuma da mataimaki)