Queiroz ya sauka daga muƙaminsa na kocin Ghana
Carlos Queiroz ya sauka daga muƙamin kocin Ghana bayan watanni uku yana jagorantar tawagar bayan sun fice daga gasar cin kofin duniya a zagaye na ƴan 32.
Kocin mai shekara 73 ya karɓi ragamar horas da tawagar a watan Afrilu kuma ya jagoranci tawagarsa zuwa matsayi na uku a rukunin L kafin Colombia ta doke su da ci 1-0 a zagaye na ƴan 32 na gasar cin kofin duniya.
Tsohon kocin Manchester United ya je gasar cin kofin duniya sau biyar a jere, bayan ya jagoranci Iran da Portugal da Masar a manyan gasanni.
Queiroz na ɗaya daga cikin kociyoyin tawagogin ƙasa biyu da suka bar muƙamansu a ranar Lahadi, inda ƙasar Jordan ma ta raba gari da babban kocinta Jamal Sellami bayan tawagar ta zo ta huɗu a Rukunin J.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Queiroz ya bayyana ɗan lokacin da ya yi tare da Ghana a matsayin tafiya mai cike da "alfahari," yana mai yan wasansa sun dawo wa tawagar Black Stars kimarta a fagen wasan ƙwallon ƙafa na duniya.
Tawagar Black Stars za ta koma fagen wasa a watan Satumba, lokacin da za a fara fafutukar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (Afcon) ta shekarar 2027.