Iran na ƙara kaimin shirin hari kan Amurka da aminanta

Asalin hoton, Reuters
Wasu rahotanni na cewa ƙasar Iran na ƙarfafa ƙarfin tsaronta,da tattara masumara ma ta baya, tare da yin barazanar mayar da kakkausan martani ga Amurka da ƙawayenta a yankin Tekun Fasha.
Rahoton da Jaridar Wall Street Journal ta wallafa, na ya bayyana cewa Tehran na shirye-shiryen tunkarar yiwuwar kai hare-haren da Amurka za ta iya kaiwa bayan zaɓen tsakiyar wa’adi na ƙasar, kuma tana ɗaukar waɗannan matakai ne domin hana irin waɗannan hare-hare.
Za a gudanar da zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka a makon farko na watan Nuwamba.
Jami’an Iran sun yi gargaɗi, a cikin jawabai na fili da kuma tattaunawa ta sirri da hukumomin yankin, cewa idan Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare, Jamhuriyar Musulunci za ta ƙara rura wutar rikici a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Jaridar ta kuma ce hotunan tauraron ɗan adam sun nuna cewa Iran na ƙara tsaurara matakan kariya a wurare masu muhimmanci, ciki har da cibiyoyin nukiliya da yankunan kan iyaka.
Rahoton ya ƙara da cewa wannan na iya zama yunƙurin karkatar da hankalin jama’a daga matsanancin halin tattalin arzikin da al’ummar ƙasar ke fuskanta, musamman bayan Amurka ta tsaurara takunkuminta kan Iran.
Ko a ranar Lahadin ƙarshen mako, an jiyo sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa a Iran, Mohsen Rezaei, na cewa idan Amurka ta sake kai hari, sojojin Iran za su kai farmaki kan dukkan cibiyoyin adana bayanai ciki har da na ƙirkirarriyar basira ta AI da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
































