KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 12/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Litinin 12 ga watan Oktoban 2026.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Harin da 'yan bindiga suka kai jihar Zamfara ya hallaka sojoji 8 da fararen hula 4

    zanen hoton yan bindiga

    Wani hari da ƴan bindiga suka kai a jihar Zamfara ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 13, ciki har da sojoji, a lokacin da suke raka wasu ƴan kasuwa a hanyar Gwashi, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum.

    Bayanai sun ce ƴan bindigar sun yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna ne, inda suka buɗe musu wuta.

    Honarabul Hamisu A. Faro, ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Bukkuyum ta Kudu ya ce ƴan bindigar sun yi amfani da duhun daji ne wajen kai harin, inda suka hallaka sojoji takwas, da fararen hula huɗu, sai wani jami'in tsaro guda ɗaya da ya mutu a asibiti.

    Ya ce alummar yankin na cikin kaɗuwa ganin yadda lamarin ya shafi mutanen da ke taimakawa wajen basu tsaro.

    Ɗan majalisar ya ce kauyuka fiye da 5 da ke yankin na cikin firgici da tashin hankali, kuma manoma sun gaza zuwa gonakin su domin girbe abin da suka noma saboda tsoron sace su ko kashe su.

    Ya kuma ce hare haren ya raba kusan mutum 5,000 da muhallansu, yayin da ƴan bindigar suka toshe babbar hanyar da ke ɗaki takwas na tsawon kusan watanni biyu.

    Alummar yankin ta bakin ɗan majalisar da ke wakiltar su, sun bukaci gwamnati ta ɗauki mataki ta hanyar kai hari kai tsaye kan inda ƴan bindigar suke.

    Ya ce abinda ya sa lamarin ya kara ƙamari a baya bayan nan shi ne saboda gwamnati ta ƙi yin sulhu da 'yan bindigar, lamarin da ya ce ya sanya su ɗaukar alwashin tarwatsa alummomin da ke yankin na Bukkuyum.

  2. Mutum 72 sun mutu a harin da ake zargi Masar ta kai kan masu haƙar ma'adinai a Sudan

    masu hako ma'adinai

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Sudan, Emergency Lawyers, ta yi zargin cewa wani hari da sojojin saman Masar suka kai kan wani wurin haƙar zinare kusa da kan iyakar Sudan da Masar ya kashe aƙalla masu haƙar zinare guda saba'in da biyu.

    Duk da dai waɗanda suka tsira daga wurin haƙar ma'adinan na Al-Uqayadat sun ce akwai yiwuwar adadin ya zarta hakan.

    Wakilin BBC ya ce harin na ranar Asabar ya biyo bayan wani harin sama da aka kai a watan Yuni wanda shi ma ake zargin Masar da kai wa inda aka kashe ma'aikata 23.

    A wancan lokacin, rundunar sojin Masar ta bayyana cewa ta kai farmaki ne kan masu haƙar zinare ba bisa ƙa'ida ba.

    Ya zuwa yanzu dai Masar din ba ta yi wani martani kan sabbin zarge-zargen ba.

  3. Mutum 11 sun jikkata a harin da yan Houthi suka kai Saudiyya

    wuta na tashi a wurin da aka kai hari a Saudiyya

    Hukumomin Saudiyya sun ce harin da 'yan tawayen Houthi na Yemen suka kai a jiya Lahadi kan babban filin jirgin sama na Riyadh ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu mutane goma sha daya.

    Wannan shi ne karo na uku da aka kai hari kan filin jirgin saman a cikin kwanaki hudu.

    Harin da aka kai a ranar Asabar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha uku.

    Kungiyar Houthi ta ce ta kuma kai hari kan filin jirgin saman Dammam da ke gabashin Saudiyya, tare da wasu wuraren da ake sarrafa man fetur.

    Wakiliyar BBC ta ce wannan karin tashin hanklin zai kara asassa damuwar da ake da ita kan batun fitar da danyen mai daga wannan yankin zuwa sassan duniya.

  4. Assalamu Alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da safiyar Litinin.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya – musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da X da kuma Instagram domin kallon bidiyo da tafka muhawara.

    Sai ku kasance tare da mu.