Da gaske Kannywood ta fi kwatanta 'nishaɗin halal'?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A tsawon shekaru, masana'antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood ta yi fice wajen samar da nishaɗin da suke cewa sun dace da al'adu da koyarwar addinin Musulunci.
Wannan ya sa masu sharhi kan fina-finai suke bayyana cewa fina-finan Hausa suna kama da abin da ake kira ''nishaɗin halal'' wato nishaɗin da ke koyarwa, faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa ba tare da karya ƙa'idodin ɗabi'a da addini ba.
Yayin da ake samun ƙaruwar buƙatar irin wannan nishaɗi mai ɗauke da kyawawan darussa a tsakanin al'ummomin Musulmi a duniya, masana'antun fina-finai kamar Kannywood na da damar cin gajiyar wannan kasuwa mai girma.
A fahimtar masana harkar, nishaɗin halal na nufin duk wani nau'in nishaɗi da ya dace da koyarwar Musulunci, wanda ke kauce wa ɓatsa da lalata tarbiya da kuma duk wani saƙo da zai iya lalata tarbiyyar al'umma.
Maimakon haka, irin wannan nishaɗi yana ƙarfafa kyawawan ɗabi'u, haɗin kai a cikin iyali, gaskiya, mutunta juna da kuma koyar da darussan rayuwa masu amfani.
Masana suna ganin cewa kasuwar nishaɗin halal tana ƙara bunƙasa a duniya, musamman saboda karuwar yawan Musulmi da kuma yaɗuwar kafafen kallon fina-finai na yanar gizo.
Rahotanni kan tattalin arzikin halal sun nuna cewa ɓangaren kafofin watsa labarai da nishaɗi na daga cikin fannoni masu saurin girma a kasuwar Musulmi ta duniya, lamarin da ke nuna akwai gagarumar dama ga masu shirya fina-finai masu bin wannan tsari.
Mene ne Nishadin Halal?
A cikin shirin "A Wata Mahangar", wanda Dokta Muhsin Ibrahim da Dokta Idris Yana ke jagoranta, marubuciya kuma mai bincike, Rahama Abdulmajid, ta bayyana cewa nishaɗin halal yana nufin duk wani nau'in nishaɗi da bai ci karo da koyarwar addinin Musulunci ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A taƙaice, halal na nufin nishaɗin da bai karya dokoki da tanade-tanaden addini ba. Wato mutum zai iya jin daɗin nishaɗi tare da kiyaye abin da Musulunci ya yarda da shi," in ji ta.
Ta ƙara da cewa kasuwar halal ta samo asali ne daga buƙatar samar wa Musulmai kayayyaki da ayyukan da suka dace da aƙidarsu, maimakon dogaro da abubuwan da ake samarwa gaba ɗaya ba tare da la'akari da buƙatunsu ba.
Rahama ta ce kasuwar halal a duniya ta girma sosai cikin ƴan shekarun nan, inda aka fi mayar da hankali a farko kan abinci, abin sha da kayan sawa, amma daga baya aka fahimci muhimmancin ɓangaren nishaɗi.
"Na fi damuwa da ɓangaren abinci da abin sha da tufafi, amma daga baya na fahimci cewa an manta da ɓangaren nishadi. A yanzu, nishaɗin halal ya zama babbar kasuwa da ake hada-hadar biliyoyin daloli a cikinta," in ji ta.
A cewarta, ƙasashe irin su Malaysia, Turkiyya da Saudiyya na daga cikin waɗanda suka fi amfani da tattalin arzikin halal, amma duk da haka babu wurin da ake kiyaye ƙa'idojin halal a harkar nishaɗi kamar yadda ake yi a Kannywood.
"Babu inda ake kiyaye halal kamar Kannywood, amma abin mamaki shi ne ba a cin moriyar wannan kasuwa yadda ya kamata."
Kannywood da nishaɗin halal
Duk da ƙoƙarinta wajen gudanar da nishaɗi cikin tsabta da, Kannywood na fuskantar ƙalubalen wajen samun tagomashi daga damarmakin da ke cikin ɓangaren.
Masana da masu bincike kan harkokin fina-finan Hausa sun ce Kannywood na daga cikin masana'antun shirya fina-finai da suka fi ba da muhimmanci ga ƙa'idojin addinin Musulunci wajen samar da nishaɗi.
Sai dai duk da haka, har yanzu masana'antar ba ta amfana yadda ya kamata daga babbar kasuwar "nishaɗin ɗin halal" da ke bunƙasa a duniya ba.
Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus kuma mai sharhi kan harkokin Kannywood, ya ce idan aka kwatanta Kannywood da sauran masana'antun shirya fina-finai a ƙasashen Musulmi, Kannywood ta fi ƙoƙari wajen kiyaye ƙa'idojin addini.
"Kannywood sun fi ƙoƙari wajen tsabtace fina-finansu sama da sauran masana'antun fina-finai a duniya, har ma da wasu ƙasashen Musulmi irin su Saudiyya, Iran da Turkiyya," in ji shi.
Masanin ya ce a wasu ƙasashen da suke iƙirarin kwatanta nishaɗin hala, "za ka ga ana nuna mace na taɓa namiji, ana runguma ko ma sumbata, abubuwan da a Kannywood ba a yin su. Wannan ya sa muke ganin babu kamar Kannywood wajen kwatanta nishaɗin halal," in ji shi.
Ya kuma ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki a masana'antar su nemi hanyoyin haɗin gwiwa da ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke aiki a ɓangaren tattalin arzikin halal domin faɗaɗa kasuwarsu.
Buƙatar sabon tunani da zuba jari
Rahama Abdulmajid ta nuna cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana bunƙasar nishaɗin halal a Najeriya shi ne rashin ƙirkire-ƙirkire da sabbin tsare-tsaren kasuwanci.
Ta ce maimakon a riƙa kallon sabbin kafofin yaɗa labarai da nishaɗi a matsayin barazana ga tarbiyya, ya kamata a yi amfani da su wajen samar da abubuwan da suka dace da ɗabi'u da addini.
"Da zarar an samu wata sabuwar tasha ko sabuwar hanyar yaɗa nishadi, sai a fara cewa za ta lalata tarbiyya. Maimakon a yi tunanin yadda za a samar da abin da ya dace da al'umma a kai," kamar yadda ta bayyana a shirin.
Ta ƙara da cewa Najeriya na da yawan matasa da ke neman aikin yi, kuma masana'antar nishaɗi na ɗaya daga cikin ɓangarorin da za su iya samar da ɗimbin guraben ayyuka idan aka tsara su yadda ya kamata.
Rahama ta yi nuni da ƙoƙarin da wasu ƙungiyoyi suka fara yi wajen bunƙasa tattalin arzikin halal, ciki har da Dar Halal wanda Alhaji Dikko ya kafa tare da haɗin gwiwar gwamnati.
Ta bayyana cewa ta taɓa gabatar wa asusun manufar nishaɗin halal, inda suka samu haɗin gwiwa a shirin fim ɗin Nana Asma'u.





























