Fitattun ƴan siyasa huɗu da babu sunansu a ƴan takarar gwamna na INEC

Asalin hoton, Comr Aminu Abdussalam Gwarzo/FB/BBC
Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a zaɓen da za a gudanar a Najeriya a ranar 6 ga Fabrairu, 2027, lamarin da ya za a iya cewa ya bar baya da ƙura.
A cikin jerin sunayen, ba a ga sunayen wasu fitattun ƴan siyasa ba a jerin, lamarin da ya haifar da muhawara, musamman kafofin sadarwa tare da neman cikakken bayani kan abin da ya faru.
Sai dai rashin bayyana suna a jerin ba ya tabbatar da cewa an soke takarar ko kuma an cire ɗan takara baki ɗaya.
Hukumar ta fitar da jerin sunayen ne kamar yadda shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya yi alƙawari a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a farkon makon nan.
A daidai lokacin da ake tsimayen cikakken bayani kan batun, BBC ta rairayo wasu fitattun ƴan takara da ba a ga sunansu ba.
Ali Isa Pantami - PDP, Gombe
Daga cikin waɗanda suka fi jan hankali a jerin sunayen akwai tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda shi ma sunansa bai bayyana a cikin jerin sunayen ƴan takarar gwamna na ƙarshe da aka amince da su a Jihar Gombe ba.
A jeri sunayen da INEC ta fitar, akwai ƴan takara 16 da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Jerin ya nuna cewa Bala Bello Tinka na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) da Jamilu Isyaku Gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), da kuma Babayo Ardo Kumo na jam'iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC) suna cikin waɗanda aka tantance kuma aka amince da su domin shiga zaɓen.
Abdulsalam Grwazo - NDC, Kano
Wani wanda rashin ganin sunansa ya ja hankali shi ne tsohon gwamnan jihar Kano, Aminu Abussalam Gwarzo na NDC a Kano, wanda ya ja hankali wataƙil saboda tasirin Kwankwasiyya a siyasar Kano.
A cikin watan Maris na 2026 ne Aminu Abdussalam ya sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano bayan raba-gari da gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
A jerin da INEC ta fitar akwai ƴan takara 17, ciki har da Abba Kabir Yusuf na APC da Ibrahim Ali Amin na ADC da Muhammad Sani Abacha na PDP da sauran su.
Ladi Adebutu - PDP, Ogun
A jihar Ogun, sunan ɗan takarar jam'iyyar PDP, Ladi Adebutu da abokin takararsa, Yemi Sowunmi-Kolapo a cikin jerin sunayen ƴan takarar gwamna na ƙarshe da Hukumar INEC ɗin ta fitar.
Jerin sunayen da INEC ta fitar na ƴan takarar gwamnan jihar ya ƙunshi sunayen ƴan takara 13 na gwamna tare da mataimakansu.
Daga cikin waɗanda sunan su ya fito akwai ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Solomon Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, tare da abokiyar takararsa, Kudirat Abiodun Balogun, a cikin jerin sunayen.
Haka kuma, an sanya sunan Jimi Lawal, na hannun damar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).
Musa Shugaba-Abdullahi - NDC, Nasarawa
Haka kuma a cikin jerin babu sunan ɗan takarar gwamna na jam'iyyar NDC a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Kimanin mako uku da suka gabata ne jam'iyyar ta tabbatar da Musa Shugaba a matsayin ɗan takararta, kamar yadda jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito.
A cikin jerin mai ɗauke da ƴan takara 13, akwai Sanata Ahmad Wadada na APC da tsohon shugaban ƴansandan Najeriya, Muhammad Abubakar Adamu na jam'iyyar SDP da sauran su.
'Abin da ya faru da sunan Pantami'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da take mayar da martani, jam'iyyar PDP a Jihar Gombe ta ce tana da yaƙinin za a gyara rashin bayyana sunan ɗan takararta, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a jerin sunayen da INEC ta fitar.
A wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya fitar a ranar 10 ga Oktoba, 2026, ya ce jam'iyyar ta lura da rashin bayyana sunan Pantami, wanda ya lashe zaɓen fidda gwani da aka sake gudanarwa a ranar 29 ga Satumba, bisa umarnin Babbar Kotun Tarayya.
Sanarwar ta ce sashen kula da harkokin shari'a da hulɗa da hukumomi sun fara tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa na jam'iyyar da kuma INEC, domin ganin an gyara lamarin cikin wa'adin da doka ta tanada.
"Wannan ƙalubale ne na ɗan lokaci, amma lallai ba wai mataki na ƙarshe ba ne," in ji sanarwar.
Ta kuma buƙaci magoya bayan Pantami da na ƙungiyar Pantamiyya da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da tattara goyon baya, tare da mai da hankali kan manufofin da suka sa suka shiga siyasa.
Sanarwar ta ce ƙungiyar Pantamiyya na nan daram, cikin haɗin kai, kuma a shirye take ta ci gaba da fafutukar ganin an samar da shugabanci da zai yi wa al'umma hidima.
'Aminu Abdussalam zai shiga zaɓe'
A wani lamari makamancin haka, NDC a Jihar Kano ta ce rashin bayyana sunan ɗan takararta a jerin INEC kuskure ne da suke da yaƙinin za a gyara.
Aminu Abdulsalam Gwarzo, tsohon mataimakin gwamnan Kano, shi ne ɗan takarar gwamna da NDC ta tsayar a jihar.
Dokta Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata sakataren ƙungiyar kwankwasiya, ya shaida wa BBC cewa lamarin bai tayar masu da hankali ba.
''Na farko dai ɗan takararmu na gwamna a jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya riga ya yi rajista da jam'iyyar NDC kuma ya yi ta akan lokaci, sannan abu na biyu kuma shi ne bai yi rajista da jam'iyya biyu ba, a don haka wannan hukunci na kotun ƙoli ba zai taɓa shi ba,'' in ji shi.




























