An sanar da kuɗin kujerar aikin Hajjin 2027 a Najeriya

Asalin hoton, Mansoreh Motamedi/Getty Images
Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sanar da kuɗin aikin Hajjin 2027 da maniyyatan Najeriya za su biya.
Farashin ya bambanta gwargwadon yankin da za a tashi zuwa Saudiyya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce gwamnatin tarayya ta amince da kuɗaɗen ne bayan tattaunawa da shugabannin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kuma masu ruwa da tsaki a Saudiyya.
NAHCON ta kuma sanya ranar 26 ga Satumba 2026 a matsayin ranar ƙarshe kuma ta kammala ɗora bayanan na dukkan maniyyatan Hajjin 2027.
Za a ɗora bayanan ne a tsarin intanet na Nusuk-Masar.
Hukumar ta ce ba za a ƙara wa'adin ba.
NAHCON ta ce dole ne jihohi su kammala tura dukkan kuɗaɗen aikin Hajjin 2027 zuwa 2 ga Disamba 2026.
NAHCON ta yi gargadin cewa rashin cika wa'adin da aka sanya na iya kai wa ga rasa kujerun Hajjin da aka ware wa jihar.
Ga muhimman bayanan da maniyyatan Hajjin 2027 ke buƙatar sani:
Nawa ne kuɗin Hajjin 2027?
NAHCON ta kayyade kuɗin ne bisa yankin da mahajjaci zai tashi:
- Yankin Maiduguri da Yola: N7,560,822
- Sauran jihohin Arewa: N7,672,822
- Jihohin Kudancin Najeriya: N7,882,822
Hakan na nufin waɗanda za su tashi daga Kudancin Najeriya ne za su biya mafi yawa, yayin da masu tashi daga Maiduguri da Yola za su biya mafi ƙarancin kuɗi.
Me ya sa kuɗin ya bambanta?
NAHCON ta ce an yi la'akari da abubuwa da dama wajen ƙayyade kuɗin, ciki har da:
- Farashin canjin kuɗaɗen kasashen waje.
- Kudin hidimomin da za a samar wa maniyyata a Saudiyya.
- Tattaunawa da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi.
- Shawarwarin kamfanonin da ke samar da hidimomin Hajji a Saudiyya.
Hukumar ta ce an yi hakan ne bisa ƙa'idar tabbatar da gaskiya, rage tsada da kuma kare jin daɗin maniyyatan Najeriya.
Waɗanda suka riga suka biya Naira miliyan biyar fa?
NAHCON ta ce maniyyatan da suka riga suka ajiye N5,000,000 dole ne su biya sauran kuɗin domin kammala rajistarsu.
Sabbin masu neman zuwa Hajji kuma za su iya yin biyan kuɗin ta hukumomin jin daɗin alhazai na jihohinsu, hukumomi ko kwamitocin da aka amince da su.
Haka kuma, za su iya amfani da tsarin adashin gata na Hajj Savings Scheme (HSS) ta bankunan da ke cikin tsarin.
Sabuwar ƙa'idar aikin hajjin 2026 da Saudiyya ta fitar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ma'aikatar kula da aikin Hajji da Umra ta Saudiyya ta saka ƙa'idar shekaru ga maniyyatan da za su je sauke farali a wannan shekara.
A yanzu Saudiyya ta haramta wa yara ƴan ƙasa da shekara 15 zuwa aikin hajjin, wanda ta gabatar a 2025, aka kuma fara aiki da dokar a bana.
Ma'aikatar ta ce ta saka sabuwar dokar ne domin tabbatar da kariya da kuma iya tafiyar da lamurran maniyyatan ba tare da tangarɗa ba, a lokacin aikin hajjin da miliyoyin mutane ke halarta a kowace shekara.
Hukumomin Saudiyya sun gabatar da wata sabuwar ƙa'idar aikin hajjin 2026 ga maniyyatan bana.
Tuni dai maniyyata daga ƙasashe daban-daban ciki har da Najeriya suka fara tashi zuwa Saudiyya domin sauke faralin.
Aikin hajji na ɗaya daga cikin shika-shikan Addinin Musulunci, da aka wajabta wa wanda yake da damar yi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.
A kowace shekara miliyoyin Musulmai ne daga ƙasashen duniya daban-daban ke sauke farali.
Ƙasar Saudiyya, wadda ake gudanar da aikin ibadar a cikinta kan fitar da ƙa'idojin aikin lokaci zuwa lokaci domin dacewa da dokokinta da kuma inganta aikin hajjin.











