Liverpool na son Schade, Haaland da Foden na ɗaukar hankula a Turai

 Kevin S.chade
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool na cikin sahihan ƙungiyoyin da ke kan gaba wajen ɗaukar dan wasan Brentford da Jamus Kevin Schade, yayin da da ake alƙanta ɗan wasan da Manchester United. (Teamtalk)

Barcelona ta tabbatar da cewar sun yi ƙoƙarin dauko dan wasan Ajantina da Inter Milan Lautaro Martinez, a kakar wasan nan. (Fichajes - in Spanish)

Real Madrid da Barcelona na cikin ƙungiyoyin da ke son daukar ɗan wasan Manchester City Erling Haaland, sannan a shirye yake ya ƙarbi dukkan watan dama da ta zo masa da zarar buƙatan hakan ta taso. (Sun)

Babbar ƙungiyar da ke Jamus Bayern Munich na harin ɗan wasan Ingila Phil Foden, inda har lokacin barinsa Manchester City, ya yi (Teamtalk)

Ɗan wasna Italiya da Atlanta Giorgio Scalvini, zai fuskanci yadda ake taka leda a wajen ƙasarsa, a tarhin rayuwar buga ƙwallon ƙafar tasa, inda Newcastle da Chelsea ke nuna sha'awarsu na ɗaukar ɗan wasan. (Football Italia)

Nottingham Forest, da Roma da Napoli na harin Dodo, daga Fiorentina a watan Janairu, a dai-dai lokacin da wasu ƙungitoti da ke turai ke harin ɗan wasan. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

Har yanzu ɗan wasan Brighton da Gambia Yankuba Minteh, 22, na son komawa Liverpool a wannan kaka, bayan da suka gasa cimma matsayar ya koma ƙasar a kakar wasanni. (GiveMeSport)