Ta yaya yarjejeniya da Iran za ta amfani Donald Trump?

Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa a shirye Amurka take domin sassauta takunkuman da ta ƙaƙaba wa Iran tare da sakin kadarorin ƙasar da ta ƙwace.
Shugaban Amurkan ya yi watsi da rahotannin yana mai kiran su "labaran ƙarya."
Sai dai wasu masu sharhi sun ce cimma yarjejeniya da Iran na iya zama abin da zai amfani Trump da jam'iyyar Republican yayin da ake tunkarar zaɓen rabin wa'adi.
CNN, ta ambato wani jami'in Amurka da ba a bayyana sunansa ba, na cewa Amurka a shirye take ta yi wannan rangwamen idan Iran ma ta ɗauki matakai na zahiri domin warware "batun nukiliya."
A nata ɓangaren kafar yaɗa labarai ta Axios ta wallafa irin wannan labari mai ɗauke da wannan bayani, wanda Mista Trump ya mayar da martani a kai.
Shugaban Amurkan ya wallafa a shafinsa cewa rahoton ba gaskiya ba ne, kuma bai yi wa Iran tayin sassauta takunkumi ko sakin kadarorinta ba.
Ya kuma bukaci Axios ta cire rahoton daga shafinta na intanet.
Wasu masu sharhi na ganin cewa cimma yarjejeniya da Iran, baya ga tasirin da zai yi wa Tehran, zai kuma iya amfanar Donald Trump da jam'iyyar Republican yayin da zaɓen rabin wa'adi ke ƙaratowa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jaridar The New York Times ta ruwaito ranar Litinin 28 ga Satumba cewa har yanzu kasuwanni ba su ga wata alama da ke nuna Iran da Amurka sun kusa da cimma yarjejeniya ba, lamarin da ya sa farashin mai ya sake tashi.
Tasirin yaƙi da Iran kan tattalin arzikin Amurka ya kuma sa mambobi da dama na jam'iyyar Republican ke adawa da shi.
Ana sa ran za a gudanar da zaɓen majalisar dokokin Amurka cikin kimanin makonni biyar, kuma masu lura da harkokin siyasar Amurka na ganin damar samun nasarar mambobin jam'iyyar Trump ta ragu yayin da tasirin yaƙin kan tattalin arzikin Amurka ke ƙara bayyana.
Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Amurka John Thune ya shaida wa Fox News cewa babban abin da zaɓen rabin wa'adi ya fi mayar da hankali a kai shi ne batutuwan rayuwar yau da kullum da kuma hauhawar farashin mai.
Ya ƙara da cewa yaƙin Iran ya ƙara tsananta waɗannan matsaloli.
Ya kuma shawarci 'yan takarar Republican su mayar da hankali a kamfen ɗinsu kan jam'iyyar Democrat, wadda ya ce tana adawa da tsare-tsaren zaɓe da jam'iyyar Republican (GOP) ke goyon baya.
'Takun-saƙar Amurka da Iran da kuma Isra'ila'

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa wani sabon littafi a Amurka wanda Brett McGurk, wani babban jami'i a Kwamitin Tsaron Ƙasa na Amurka a lokacin gwamnatin Joe Biden, ya rubuta.
Littafin mai taken "Threshold" ya tattauna, a cikin wasu batutuwa, rawar da Iran ta taka da abubuwan da suka biyo bayan harin Hamas kan Isra'ila na ranar 7 ga Oktoba, da kuma ƙoƙarin Amurka na ganin an saki waɗanda aka yi garkuwa da su daga Isra'ila.
McGurk ya rubuta cewa a kwanakin da suka biyo bayan ranar 7 ga Oktoba, Iran ta yi ƙoƙarin matsa wa sojojin Amurka a yankin lamba ta hanyar amfani da ƙungiyoyin da ke kawance da ita domin tilasta musu janyewa.
A cewarsa, ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya a Yemen da Syria da Lebanon ne suka kai waɗannan hare-hare.
McGurk ya gabatar da wani ɓangare na labarin littafinsa a cikin wata maƙala da aka wallafa a mujallar The Atlantic.
A cikin wannan maƙalar, ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta ɗora masa alhakin gudanar da tattaunawa a asirce da jami'an Iran, wadda ya shiga tsakani a Oman, amma ba ta haifar da wani sakamako ba.
Jim kaɗan bayan waɗannan ƙoƙarin diflomasiyya, an kashe sojojin Amurka uku a wani hari a Jordan, wanda Washington ta ɗora alhakinsa kan ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya, kamar yadda Brett McGurk ya rubuta.
Bayan wannan hari, Joe Biden ya ba da umarnin kai hare-haren ramuwar gayya, inda Amurka ta kai farmaki kan wuraren da mayaƙan da ke ƙawance da Iran suke.
A cewar McGurk, waɗannan hare-hare daga ƙarshe sun sa hare-haren da waɗannan ƙungiyoyi ke kai wa sojojin Amurka suka ragu.
McGurk ya kuma ce kafin wasu jami'an Isra'ila su gana da Biden, jakadan Isra'ila a Washington ya ja shi gefe ya shaida masa cewa Isra'ila na shirin kai hari kan ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, inda za ta hari Mohammad Rida Zahedi, wani kwamanda a rundunar Quds Force ta Revolutionary Guard Corps na Iran (IRGC).
A cewarsa, jami'an Isra'ila sun tabbatar wa Amurka kafin harin cewa ginin suna ne kawai na ofishin jakadanci, amma a zahiri yana ƙarƙashin ikon sojojin Iran.
A wani sashe na maƙalarsa, ya rubuta cewa rahotannin da ke cewa ana hana agajin jin ƙai isa Gaza, ko kuma hare-haren da ake kai wa ayarin motocin agaji, sun sa Joe Biden ya ɗauki tsauraran matakai kan Isra'ila.
Sai dai a cewar McGurk, takun-saƙa kai tsaye da Iran da hare-haren ƙungiyoyi masu kusanci sosai da Tehran sun sa gwamnatin Amurka ta rage matsin lambar da take yi wa Isra'ila a aikace.
Ya rubuta cewa a wani lokaci an yi magana kan ƙara matsa wa Isra'ila lamba da kuma sake duba wasu fannoni na goyon bayan da Amurka ke bai wa ƙasar.



























