Kura-kurai 8 da masu zaɓe ke yi da ke kawo shugabanni bara-gurbi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
"Da na sani da ban zaɓe shi ba." Wannan na daga cikin kalaman da ake yawan ji daga bakin masu zaɓe bayan kammala wa'adin wasu shugabanni a Najeriya.
A duk lokacin da aka zo lokacin zaɓe a Najeriya, mutane da dama kan ce sun yi da-na-sanin zaɓin da suka yi a baya, musamman idan sun ga yadda shugabannin da suka zaɓa suka gudanar da mulki.
Duk da haka, sau da yawa matsalar ba ta tsaya ga ɗan takara kaɗai ba, har da irin kuskuren da masu zaɓe ke yi kafin ranar zaɓe.
Masana na ganin cewa wasu kurakurai da masu zaɓe ke yi ne ke taimakawa wajen kai marasa cancanta kan madafun iko.
Ga wasu daga cikin manyan kurakurai takwas da masu zaɓen ke yi da ke haifar musu da shugabanni marasa inganci:
1. Zaɓe bisa ƙabilanci
Ɗaya daga cikin manyan kurakuran da masu zaɓe ke yi shi ne kaɗa ƙuri'a bisa alaƙar ƙabila maimakon cancanta. A lokuta da dama, wasu kan fifita ɗan takarar da ya fito daga ƙabilarsu ko yankinsu ko da kuwa sun san akwai wanda ya fi shi ƙwarewa da nagarta.
Masanin harkokin siyasa, Dakta Yakubu Haruna Jae, ya ce a wasu lokuta masu zaɓe kan amince da kalaman shugabannin al'umma ko masu ruwa da tsaki da ke ƙarfafa su su zaɓi ɗan takarar ƙabilarsu.
A cewarsa, duk lokacin da masu zaɓe suka fifita ƙabila fiye da cancanta wajen zaɓar shugabanni, akwai yiwuwar su fuskanci nadama daga baya idan wanda suka zaɓa ya gaza wajen cika alƙawuransa.
"A zaɓi wanda ya kamata, domin samun shugabancin da ya kamata," in ji Dakta Jae.
Ya ƙara da cewa yawancin ƴan siyasa kan yi amfani da siyasar ƙabilanci a matsayin wata dabara ta raba kan masu zaɓe da kuma karkatar da hankalinsu.
2. Zaɓe bisa addini
Addini ma na daga cikin abubuwan da ke tasiri da taka rawa wajen sauya ra'ayin masu zaɓe duk da yake dokokin Najeriya sun hana amfani da shi wajen yin siyasa.
Dakta Jae ya ce amfani da addini wajen jan hankalin masu zaɓe na daga cikin abubuwan da ke haddasa zaɓen ɗantakarar da jama'a ke nadama a kai daga baya saboda zaɓen tumun dare.
A cewarsa, wasu 'yan siyasa kan yi amfani da malamai da sauran fitattun jagororin addini wajen isar da saƙonnin da ke ƙarfafa mabiyansu su zaɓi ɗan takara saboda addini.
A wasu lokuta ma, akan nuna wa masu zaɓe cewa goyon bayan irin wannan ɗan takara wani nau'in aikin alheri ne ga addininsu har ma da kwaɗaita musu samun lada ko wata sakayya idan suka zaɓi mutumin da ya fito daga addininsu.
3. Sayar da ƙuri'a
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sayar da ƙuri'a na daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga zaɓen shugabanni nagari.
Kafin lokacin zaɓe, mutane da dama kan bayyana ra'ayinsu tare da nuna ɗan takarar da suke goyon baya. Sai dai idan ranar zaɓe ta yi, wasu kan sauya matsayinsu bayan sun karɓi kuɗi ko kayan masarufi daga masu neman takara.
Dakta Jae ya ce irin wannan ɗabi'a na sa masu zaɓe su kaɗa ƙuri'a ga ɗan takarar da ba shi ne zabinsu na gaskiya ba. A cewarsa, hakan kan jawo nadama daga baya idan wanda aka zaɓa ya gaza wajen cika alƙawuran da ya ɗauka.
Wasu masu zaɓe kan ɗauki batun a matsayin wata dama ta samun wani ɗan ƙaramin amfani a lokacin zaɓe, ba tare da la'akari da tasirin hakan ga makomar al'umma ba.
Sai dai masanin ya yi gargaɗin cewa abin da ake samu ta hanyar sayen ƙuri'a na iya zama sanadin samun shugabancin da ba zai anfani jama'a ba na tsawon shekaru masu zuwa.
Dr Jae ya ce sayar da ƙuri'a na raunana dimokuraɗiyya kuma idan masu zaɓe suka mayar da ƙuri'unsu tamkar haja da ake saye da sayarwa, to suna taimakawa wajen bai wa marasa cancanta damar hawa mulki.
4. La'akari da jam'iyya kawai
Wani kuskuren da masu zaɓe ke yi shi ne zaɓar ɗan takara saboda jam'iyyarsa kaɗai, ba tare da duba cancantarsa da nagartarsa ba. Masu sharhi kan harkokin siyasa na cewa irin wannan ɗabi'a na iya kai wa ga zaɓen shugabannin da ba su da ƙwarewar da ake buƙata.
Dakta Jae ya ce masu zaɓe su kauce wa bin jam'iyya zalla, domin wasu ƴan siyasa kan yi amfani da farin jinin jam'iyya ko wani fitaccen mutum wajen fakewa a wajen.
"Da yawa akan samu bara-gurbi su je su shiga jam'iyyar da mutane ke so ko su shiga guguwa da farin jinin wani mutum," in ji shi.
A cewarsa, ya kamata masu zaɓe su fi mayar da hankali kan ɗan takarar da kansa, tarihinsa da abin da zai iya yi idan aka ba shi dama, maimakon alamar jam'iyya kaɗai.
5. Rashin binciken tarihin ɗantakara
Wani kuskuren da wasu masu zaɓe ke yi shi ne kaɗa ƙuri'a ba tare da binciken tarihin ɗan takara ba.
"Yana da muhimmanci a duba asalinsa, halayensa da kuma yadda ya gudanar da rayuwarsa da mu'amalarsa a tsakanin al'umma," in ji Dr Jae.
Ya ce wannan muhimmin abu ne da ya kamata masu zaɓe su mayar da hankali a kai domin ta haka ne za su fahimci irin mutumin da suke shirin ɗora wa alhakin jagorancinsu.
A cewarsa, binciken tarihin ɗan takara kan taimaka wa masu zaɓe wajen gano ko mutum ne mai gaskiya, riƙon amana da ƙwarewar shugabanci, ko kuwa akasin haka.
6. Rashin fitowa zaɓe
Rashin fitowa zaɓe ma na daga cikin kura-kuran da kan bai wa waɗanda ba su dace ba damar samun mulki. Masana sun ce idan jama'a suka zauna a gida suna zaton wasu ne za su zaɓa musu shugabanni nagari, akwai yiwuwar sakamakon ya kasance ba yadda suke so ba.
Dakta Jae ya ce wasu mutane kan yi tunanin cewa ƙuri'arsu ba ta da tasiri ko kuma ba lallai a samu wanda suke so ba, shi ya sa suke ƙin fitowa zaɓe.
"Akwai waɗanda ke ganin ko sun fito zaɓe ba zai canza komai ba, amma hakan babban kuskure ne," in ji Dakta Jae.
A cewarsa, kowace ƙuri'a na da muhimmanci, kuma rashin fitowa zaɓe na rage damar jama'a wajen zaɓar shugabannin da suke ganin sun cancanta.
7. Mantawa da abubuwan da shugabanni suka yi a baya
Wani kuskuren da masu zaɓe kan yi shi ne mayar da hankali ga sabbin alƙawuran yaƙin neman zaɓe tare da manta yadda ɗan takara ya gudanar da ayyukansa a baya. Masana sun ce abin da mutum ya yi a baya na iya ba da haske kan yadda zai gudanar da mulki idan aka sake ba shi dama.
Dakta Jae ya ce sau da yawa 'yan siyasa kan yi romon baka ga masu zaɓe idan suka fahimci cewa ba sa binciken tarihin ayyukansu ko irin gudunmawar da suka bayar a baya.
"Idan masu zaɓe suka manta abin da shugabanni suka yi a baya suka rungumi alƙawurai kawai, akwai yiwuwar su sake faɗawa irin matsalolin da suka fuskanta a baya," in ji shi.
8. Zaɓe don huce takaici ko saboda tausayi
Masana sun ce wasu masu zaɓe kan yanke hukunci cikin fushi ko takaicin da suke yi wa wani ɗan takara, maimakon duba irin aikin da ya yi da kuma cancantarsa.
A wasu lokuta, masu zaɓe kan ƙi sake zaɓar shugaba duk da kyakkyawan aikin da ya gudanar, saboda wani abu da ya ɓata masa rai.
Haka kuma, akwai masu zaɓen ɗan takara saboda tausayi ko halin wahalar da ya taɓa shiga, suna ganin hakan wata hanya ce ta saka masa. Sai dai masana na gargadin cewa tausayi kaɗai ba ya tabbatar da cewa mutum zai iya shugabanci yadda ya kamata.
Dakta Jae ya ce ya kamata masu zaɓe su yanke hukunci bisa nagarta, ƙwarewa da abin da ɗan takara zai iya yi wa al'umma, ba wai saboda fushi ko tausayi ba.



























