'Wasu matan ba su san suna ɗauke da cutar da ke sa mace gemu ba'
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Gemu ko gashin bakin da kuke gani a fuskar wasu mata, ba haka kawai ba ne. Larura ce!
An ware duk watan Satumba domin faɗakar da mutane cewa kimanin kashi 10% na mata suna da larurar rikicewar sinadaran jiki wato PCOS a taƙaice.
Albarkacin wannan wata, mun zanta da wata mai wayar da kai kuma da ke da wannan cuta domin jin suke fama.
Abin da Mufti Menk ya cewa Rahama Sadau
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta koka kan salon
wasu kamfanonin tsara tafiye-tafiye na ɗaukar bidiyon masu ibadar Umrah da suka
je ƙasa mai tsarki ta kamfaninsu a wani ɓangare na tallata kamfanonin nasu.
Rahama Sadau ta bayyana damuwarta ne a wani saƙo da ta
wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana sha’awar zuwa Umra cikin
rukunin jama’a amma salon kamfanonin da ke nema zama ruwan dare na matuƙar
sanyaya gwiwa.
Ta ce ya kamata Umrah ta kasance ibada maimakon mayar da ita
wata dama ta samar da hotuna ko bidiyon da za a wallafa a shafukan sada
zumunta.
Saƙon nata ya ja hankalin mutane da dama inda fitaccen
malamin addinin Musulunci Mufti Menk, ya yi martani kan saƙon nata inda kuma ya
ba ta shawarar kamfanin da za ta iya zuwa umarah ta hannunsu wanda ya ce yana
bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin sirri.
Sai dai y ace a zamanin da ake ciki, mutane da dama kan samu
ƙwarin gwiwar zuwa Umrah ne bayan sun ga wasu sun je amma a caerwa shi “abin da
ya fi dacewa shi ne kada ɗaukar hotunan ya zama abin da aka fi mayar da hankali
a kai.”
Rukunin ƙarshe na sojin Amurka na ficewa daga Iraƙi
Sojojin Amurka na ƙarshe na janyewa daga Iraki, abin da ke kawo ƙarshen kasancewar dakarun Amurka a ƙasar tsawon sama da shekara 20.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yaba da rawar da sojojin suka taka, tana mai cewa sun yi nasarar murƙushe ƙungiyar ISIS a Iraki da ma yankin baki ɗaya.
Pentagon ta ce janyewar sojojin ta kuma nuna sauyin da ake samu zuwa tsarin tsaro da Iraki za ta jagoranta, tare da samun goyon bayan Amurka ta hanyar hulɗar ƙasashen biyu kamar yadda aka saba.
Sai dai masana harkokin tsaro a Iraki na gargadin cewa Iran da ƙungiyoyin da take marawa baya za su iya amfani da kafar da janyewar sojojin Amurka za ta haifar domin ƙara faɗaɗa tasirinsu.
Sojojin Amurka sun fara mamaye Iraki ne shekara 23 da suka gabata, inda suka jagoranci ƙawancen ƙasashe wajen hambarar da gwamnatin Saddam Hussein.
Daga bisani sojojin Amurka sun sake komawa ƙasar a shekarar 2014 domin yaƙi da ƙungiyar IS.
Ina cikin ƙoshin lafiya kuma na shirya yin aiki gadan-gadan - Tinubu
Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce yana cikin ƙoshin lafiya kuma a shirye yake ya koma bakin aiki.
Ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan isarsa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas bayan kammala hutun aiki na tsawon wata ɗaya a Turai.
Da yake magana da manema labarai, Shugaba Tinubu ya kuma yi watsi da jita-jitar da ake yi cewa yana fama da rashin lafiya bayan shafe tsawon lokaci yana hutun aiki a Turai.
Manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi cikinsu har da gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila, kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, da kuma manyan jami’an tsaro.
Ya kuma ce jita-jita wani abu ne da aka saba gani a siyasa, amma ya jaddada cewa yana nan cikin koshin lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki.
A cewarsa, ya ji daɗin hutun nasa, kuma babu wata matsala da yake fama da ita.
Rasha ta sake kai gagarumin hari kan Kyiv
Rasha ta sake kai wani mummunan hari ta sama kan yankin Kyiv
babban birnin Ukraine cikin dare, inda ta yi amfani da makamai masu linzami da
jirage marassa matuƙa.
Wani babban jami'i ya ce gidaje da dama sun rushe a wata
gunduma sakamakon harin, kuma an gano gawar wani yaro a ƙarƙashin baraguzan
gine-ginen.
Ya ce an ceto wasu daga cikin iyalan yaron da suka samu
raunuka a harin.
Rahotanni sun ce harin ya kuma lalata rumbunan ajiya da wasu
muhimman kayayyakin more rayuwa, lamarin da ya haifar da katsewar wutar
lantarki da kuma tangarda wajen samar da ruwa.
A baya-bayan nan dai
Rasha ta ƙara yawan hare-haren da take kai wa birnin Kyiv cikin dare da kuma
rana.
Dangote zai ƙaddamar da aikin gina matatar mai a Kenya
Asalin hoton, Getty Images
Nan gaba a yau ne, Attajirin Afirka Aliko Dangote, zai aza harsashin gina wata matatar man fetur a gabar tekun Kenya.
Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya ce matatar wadda za a gina a yankin Lamu za ta taimaka wajen kare kasar daga sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya.
Wakilin BBC ya ce ginin matatar ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da ke ikirarin cewa filin da za a gina matatar mallakinsu ne.
Masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwa kan yiwuwar illa ga muhalli da aikin zai iya haifarwa.
Sai dai kuma duk da haka, Dangote na ci gaba da fara aikin ginin duk da umarnin wata kotu da ya bukaci a dakatar da aikin.
Asalin hoton, State House Kenya
Asalin hoton, State House Kenya
Asalin hoton, State House Kenya
Barka da Hantsi
Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Laraba - tabawa ranar samu daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku tafka muhawara.