Me ya sa wayoyinmu ke nuno mana abin da muke yawan magana a kai?

Asalin hoton, Getty Images
Ana iya cewa mafi yawanmu na amfani da wayoyin hannu a kowace rana. Wani bincike ya nuna cewa musamman matasa kan shafe matsakaicin lokaci na awa huɗu da minti 37 a rana suna amfani da wayoyinsu na zamani.
Sai dai duk da irin kulawar da muke bai wa wayoyinmu, akwai wata tambaya da ake yawan yi.
Shin su ma wayoyin suna kula da abin da muke yi ko faɗa?
Shin bayanan da ake yaɗawa a intanet game da su gaskiya ne? Shin da gaske wayoyin hannu na sauraron tattaunawarmu da kuma abin da muke faɗi?
Waɗannan wasu daga cikin tambayoyin da suka daɗe suna tayar da muhawara, musamman a wannan zamani da fasahar sadarwa da tattara bayanai ke ƙara samun gurbi a rayuwar yau da kullum.
Me ya sa mutane ke tunanin waya na jin maganganunsu?
A shafukan sada zumunta, ana yawan ganin saƙonnin da ke ikirarin cewa wayoyin hannu na iya jin abin da kake faɗa, ko ma su karanta abin da ke zuciyarka. Misali, ka taɓa yin magana da wani kan wani abu, sannan ba da jimawa ba ka fara ganin tallace-tallace game da wannan abu a ko'ina cikin shafukan sada zumuntarka?
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun daɗe suna bayyana damuwa tare da yaɗa ra'ayoyin ƙulle-ƙulle cewa wasu kamfanoni na bibiyar su ta hanyar manhajoji, lamarin da wasu mutane ke gaskatawa.
Idan ka fara ganin tallace-tallace kan wani batu da kai da abokanka kuka yi magana a kai, watakila kwatsam ne kawai ya faru. Amma hakan na iya sa mutum ya fara tambayar kansa dalilin da ya sa hakan ke faruwa.
A zahiri, gwargwadon yadda kake mu'amala da abubuwan da suka shafi wani batu a intanet, akwai yiwuwar ka ci gaba da ganin ire-irensu. Hakan na faruwa ne saboda tsarin da ke sarrafa abubuwan da shafukan sada zumunta ke nunawa masu amfani yana bibiyar halayenmu na amfani da intanet.
Wannan tsarin kan yi nazarin irin sakonnin da muke kalla, waɗanda muke so, ko kuma muke rabawa wasu, sannan ya yi amfani da wannan bayani wajen zaɓar irin abubuwan da zai ci gaba da nuna mana.
Saboda haka, abin da muke gani a intanet ba lallai ne ya kasance sakamakon sauraron tattaunawarmu ba, sai dai yana iya kasancewa sakamakon bayanan da tsarin ya tattara game da abubuwan da muke sha'awa.
Maganganun da ake yi game da waya a intanet
Wasu masu ƙirƙirar abubuwa a intanet kan yi ikirarin cewa manhajojin waya na tattara bayanan masu amfani, kuma ana iya dakatar da hakan ta hanyar sauya wasu saitunan waya. Sai dai kawo yanzu, babu wata hujja tabbatacciya da ta tabbatar da waɗannan ikirare.
Har ila yau, wasu mutane sun yaɗa ra'ayoyin ƙulle-ƙulle cewa kamfanoni ko ma gwamnatoci na yi musu leƙen asiri. Duk da haka, ba a fayyace ainihin dalilin da ya sa za a yi hakan ba, kuma babu cikakkiyar shaida da ke tabbatar da waɗannan zarge-zarge.
Saboda haka, muhawarar kan ko wayoyin hannu da manhajoji na sauraron tattaunawar mutane ko kuma suna bibiyar su fiye da yadda ake zato na ci gaba da kasancewa batu da ke jan hankali, duk da cewa masana na jaddada muhimmancin bambance tsakanin abin da hujjoji suka tabbatar da kuma abin da ake yaɗawa a matsayin hasashe ko ra'ayin ƙulle-ƙulle.

Asalin hoton, Getty Images
Da gaske wayata na jin abin da nake faɗa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Eh, kuma a'a. Amma ba ta hanyar da mutane da dama ke tunani ba.
Yawancin wayoyin hannu na kasancewa a shirye suna sauraron wasu kalmomin kunnawa domin fara aiki da mataimakan murya kamar Siri, Alexa da Google Assistant. Waɗannan na'urori kan jira su ji kalmomi irin su "Hey Siri" ko makamancinsu kafin su fara aiwatar da umarnin mai amfani ko neman bayani a intanet.
Haka kuma, wayoyi kan yi amfani da bayanan murya domin mataimakan muryar su iya ba masu amfani shawarwari na musamman, kamar ba da shawarar wasu manhajoji ko ayyuka da za su iya amfani da su. Sai dai babu wata hujja da ta tabbatar da cewa ana ɗaukar ko adana tattaunawar mutane ta yau da kullum.
A baya, kamfanin Instagram ya musanta zarge-zargen da ke cewa shafin sada zumuntar na sauraron tattaunawar masu amfani da manhajarsa.
Instagram ya ce akwai dalilai daban-daban da za su iya sa wani abu da ka yi magana a kai ya bayyana a shafinka. Wataƙila dai kwatsam ne, ko kuma ka taɓa mu'amala da wasu bayanai masu alaƙa da wannan batu a baya, ko ka taɓa neman bayani a kansa ta intanet.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa yana aiki tare da wasu masu talla da ke raba bayanai game da mutanen da suka ziyarci shafukansu da wannan dandali. Wannan bayanin ne ke taimakawa manhajojin su nuna wa masu amfani abubuwan da suka dace da abubuwan da suke sha'awa da kuma ayyukan da suke yi a intanet.
Saboda haka, idan ka ga tallan wani abu da ka yi magana a kansa, ba lallai ba ne hakan ya nuna cewa wayarka ta saurari tattaunawarka, domin akwai yiwuwar ya kasance sakamakon bayanan da aka tattara daga irin abubuwan da kake nema, kallo ko mu'amala da su a intanet.
Me zan yi idan ina tunanin wayata na jin abin da nake faɗa?
BBC ta tuntuɓi Ma'aikatar Kimiyya, Ƙirƙire-ƙirƙire da Fasaha ta Birtaniya domin jin ko akwai wani bayani a hukumance game da ikirarin cewa wayoyin hannu na sauraron tattaunawar masu amfani.
Wani kakakin ma'aikatar ya ce manhajoji da shafukan sada zumunta suna iya samun damar amfani ne kawai da wasu sassan wayarka da ka ba su izini su yi amfani da su, kamar kyamara domin ɗaukar hoto ko bayanan wurin da kake domin amfani da taswira.
''Dole ne su fara neman izininka tare da bayyana dalilin da ya sa suke buƙatar wannan damar. Haka kuma kana iya ƙin amincewa ko canja waɗannan izinin ta cikin saitunan wayarka," in ji shi.
Ma'aikatar ta kuma ba da shawarar cewa idan mutum na damuwa game da tsaron bayanansa na sirri, ya kamata ya ɗauki wasu matakai na kariya, waɗanda suka haɗa da:
- Amfani da kalmomin shiga masu ƙarfi, tare da kauce wa bayyana su ga kowa.
- Kunna tsarin tabbatar da shiga mataki biyu (two-step verification) ko amfani da passkeys domin kare muhimman asusu kamar na imel.
- Duba irin izinin da manhajoji ke nema kafin sauke su a waya.
- Raba bayanan sirri ne kawai da shafukan intanet da ake amincewa da su.
- Yin taka-tsantsan kafin wallafa bayanan kai a intanet.
- Amfani da saitunan kariyar sirri (privacy settings) da ke cikin shafukan sada zumunta.
Masana na cewa waɗannan matakai na iya taimakawa wajen rage haɗarin samun bayanan sirri a hannun waɗanda ba a so, tare da ba masu amfani damar ƙara iko kan yadda ake amfani da bayanansu a duniyar intanet.



























