Abin da ya sa ake yin wasu ayyukan ibada a lokacin aikin Hajji

Mahajjata

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Aikin Hajji, ɗaya ne daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.

Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.

A duk shekara aƙalla mutum miliyan biyu ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, wanda ha kasancewa daya daga cikin taruka mafiga yawa a duniya.

Sai dai a duk shekara, akwai wasu tambayoyi da suke yawan maimaituwa, kuma waɗanda ba a cika neman amsarsu ba.

Wannan ya sa BBC ta tattaro wasu nuhimman rukunan Hajji tare da amsa tambayoyi game da asalin su da dalilin gudanar da su.

Sheikh Abdulgaffar Sheikh Nasiru Kabara, babban malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya amsa mana wasu muhimman tambayoyi game da aikin na Hajji.

Me ya sa ake kai-koma a Safa da Marwa?

A game da dalilin da ya da ake sassarfa, Sheikh Abdulgaffar Sheikh Nasiru Kabara ya ce abin da ya shafi sassarfa a wajen sa'ayi ya kunshi abin da ya zo a cikin Qur'ani mai gima.

Ya ce Allah ne ya ambaci duwatsun Saga da Marwa da ake dawafi a tsakaninsu.

Ya ce akwai maganganu da yawa a game da haka.

"Akwai cewa aikin ya samo asali ne daga aikin ita Sayyadi Hajaru, mahaifiyar Annabi Isma'il wato matar Annabi Ibrahim ta yi."

Ya ce akwai lokacin da ta bi Annabi Isma'il, ya je ya ajiye su ya tafi, sai ta fita neman ruwa da za ta sha saboda kishin ruwa, sannan ta shayar da jaririnta wato Annabi Isma'il.

"Sai da rinka wannan kai-komo tsakanin dutsen Safa da Marwa tana neman ruwa. Wana daga karshe Allah Ya aiko mala'ika Jibrilu ya karta dutse ya samar mata da ruwan sha. Wato asalin ruwan zamzam ke nan. Har yanzu wannan ruwa na nan."

Ya ce sai da ta yi wannan tafiya sau bakwai, shi ya sa aka shar'anta hakan

Sheikh

Asalin hoton, Aliyu Sufi

Bayanan hoto, Sheikh Abdulgaffar Sheikh Nasiru Kabara

Mene ne dalilin sassarfa?

A game da abin da ya sa ake sarrafa kuma, shehin malamin ya ce wannan aikin ya samo asali ne daga Annabi Muhammad.

"Manzon Allah, Annabi Muhammad ne yake yi, kuma ya ce ku yi koyi da ni na ayyukan Hajji daga gare ni."

Malamin ya ce wannan ne ya sa duk wanda ya je sai ya yi sassarfa kamar yadda Annabi ya yi.

Sai dai ya ce akwai wata riwayar da ta ce "mushrikai suna zuwa kallon masu Hajji suna ganin kamar Musulmai na samun rauni bayan dawafi."

Ya ce wannan ne ya sa Annabi Muhammad ya ce duk lokacin da aka zo daidai inda 'mushrikan suke, to a yi tafiya da sassarfa," in ji shi, sannan ya kara da cewa maza ne aka shar'anta musu banda mata.

Me ya sa ake jifa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da ibadar jifa da ake yi kuwa, malamin addinin Musuluncin ya ce shi ma ya samo asali ne daga lokacin da Allah Ya yi wa Annabi Ibrahim wahayi da ya yanka ɗansa.

"Ya samo asali daga faɗin Allah cewa Ibrahim ya yi mafarki ana masa wahayi ya yanka ɗansa Isma'il. Da ya tashi sai ya faɗa wa ɗan nasa cewa ga abin da ya gani, shi ma ɗan wato Annabi Isma'il sai ya ce wa mahaifin ya aikata abin da aka umarce shi."

Ya ce a lokacin da ya kama shi ya ɗaure shi ne sai Shaidan ya fito a daidai wajen da ake kira Jamtatul Akba.

"Sai Shaidan ya bullo yana so ya hana shi aikin da Allah ya umarce shi. Sai Allah Ya ganar da Annabi Ibrahim cewa Shaidan ne. Shi ne sai Annabi ya tsinci tsakuwa guda bakwai ya rinka jifar Shaidan yar ya gudu."

Malamin addinin ya kara haka aka yi a sauran wuraren jifar ma, domin a cewarsa, bayan jifar sai Shaidan ya canja wuri.

Malamin ya ce shi ne da suka yarda da umarnin su biyun, sai Allah Ya musanya musu da abin da ya fi alheri.

Ya ce a lokacin idon Annabi Ibrahim na rufe. Kawai dai ya bude ido sai ya ga rago.

Malamin ya kara da cewa saboda muhimmancin wannan ne sai asalin yanka .

Mene ne dalilin sanya Ihrami?

A game da sanya ihrami kuwa, Sheikh Abdulgaffar Sheikh Nasiru Kabara ya ce Allah ne ya shar'anta shi ne ta harshen Annabi Muhammad.

"Wato ana tunatar da mutane ne rayuwar lahira da kwanciyar kabari. Saboda duk girman mutum da darajarsa da ya rasu, a farin tufafi ake masa sutura. Shi ya sa kowa ke sanya ihrami fari. Kowa da kowa ya fito a farin kyalle a tsaya a gaban Allah a matsayin bayi," in ji shi.

Malamin ya ce wajabcin sanya fari a kan maza ne kawai, domin a cewarsa an saukake wa mata.

Me ya sa ake fara Hajji daga miƙati?

Wata tambayar da malamin addinin ya amsa ita ce me ya sa ake fara aiwatar da aikin Hajjin daga mikati

Malamin ya ce bayan addinin Musulunci ya yadu sosai ya kuma fadada zuwa gabas da kudu da yamma da arewa sai Manzon Allah Ya tsara cewa ba za a ce mutane tun daga garuruwan su su dauki niyya su sanya ihrami ba.

Ya ce idan aka ce dole kowa ya shirya tun a can, zai zama akwai wahala da takura.

"Amma sai Annabi ya ware misali a ce Zhuk Khulaifa na mutanen Madina. Duk wanda ya ratsa ta Madina dole a wajen ne zai sanya farin kyalle ya fara aikin Hajji."

Me ya sa ake ɗawafi?

Malamin ya kara da cewa abin a da ya shafi Dawafi da Sa'ayi, duk Qur'ani ne ya zo da su a aya daya.

Ya ce Annabi ne ya nuna yadda zake yi.

Allah na so ya nuna cewa shi ne Allah, sannan bayi bayinsa ne.

Shehin malamin ya ce haka Allah Ya tsara.