Abubuwan da suka faru a zanga-zangar Faransa

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Laurent Nuñez, ya bayar da bayanin halin da ake ciki bayan zanga-zangar da ta gudana a sassan ƙasar a yau.
Ga muhimman abubuwan da ya bayyana:
- An ƙiyasta cewa aƙalla mutum 550,000 ne suka shiga zanga-zangar a faɗin Faransa, ciki har da mutum 110,000 a birnin Paris.
- Kimanin mutum 400 aka kama, inda Nuñez ya ce mafi yawansu manya ne, kuma ba su da alaƙa da ƙungiyoyin ɗaliban da suka shirya zanga-zangar.
- A yayin rikicin da ya ɓarke tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro, jami'an tsaro 60 sun jikkata, ciki har da biyu da aka kai asibiti a sume.
- Ministan ya ɗora alhakin tashin hankalin kan wasu mutane masu alaƙa da ƴansiyasa masu ra'ayin riƙau, yana mai cewa akwai wata manufa a kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati.
- Ya kuma ce an samu fashi da ƙwacen kaya ko yunƙurin yin hakan a wasu birane da dama, ciki har da Paris, Rouen, Nantes, Toulouse da Marseille.

Asalin hoton, Mick Tickner

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, AFP via Getty Images





























