Yadda za ku gane ƴaƴan itatuwan da aka nika da sinadarai

Wasu ƴaƴan itatuwa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ta yaya za ka iya sanin ƴayan itatuwan da ka saya a kasuwa ba su da guba?

Shin za a iya gane hakan ta hanyar kallon su kawai?

A daidai lokacin da ake yaɗa bayanai da shawarwari iri-iri a kafafen sada zumunta game da zaɓen ƴaƴan itatuwa, gwamnati a Sri Lanka ta sanar da wani shiri na ƙasa mai suna "Non-Toxic Fruits for Children" (Ƴaƴan Itatuwa Marasa Guba ga Yara)

An ƙaddamar da wannan shiri ne a ranar 1 ga watan Oktoba 2026, ranar da aka yi bikin Ranar Yara ta Duniya.

Gwamnatin ƙasar ta ce manufar hakan ita ce sauƙaƙa wa jama'a samun ingantattun ƴaƴan itatuwa masu lafiya da marasa guba.

Samantha Karunaratne, Mukaddashiyar Darakta Janar na Hukumar Kare Hakkokin Masu Amfani da Kaya, ta shaida wa BBC Sinhala yadda jama'a za su iya gano wuraren da za su sayi ƴayan itatuwa marasa guba ta hanyar wannan sabon shiri.

Ta bayyana cewa bincike da nazarin da cibiyarsu ta gudanar sun nuna akwai matsaloli a hanyoyin da ake amfani da su wajen saurin nuna cewa 'ya'yan itatuwa sun nuna lokacin ci ko sun yi laushi.

Ta kuma lura cewa an samu koke-koke daga masu amfani da kayayyaki cewa wasu lokuta ba za su iya cin ƴaƴan itatuwan da suka saya a matsayin waɗanda suka nuna ba.

"A wasu lokuta, cikin ƴaƴan itacen bai nuna ba, sai dai fatar waje ko ɓawon ne kaɗai ya sauya launi, kuma ƴaƴan itacen ba su da ɗanɗano ko ƙamshin da ake tsammani.

Lokacin da muka bincika, mun gano cewa masu tara su, da masu sayar da su a manyan kasuwanni da kuma dillalai, suna amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen sarrafa ko nunarsu," in ji Darakta Janar ɗin.

Ta ƙara da cewa duk da cewa hukumomi masu ruwa da tsaki kamar: Ma'aikatar Noma, da Ma'aikatar Lafiya, da Cibiyoyin binciken 'ya'yan itatuwa, sun fitar da ƙa'idoji da umarni kan hanyoyin da suka dace wajen sarrafawa da nunar ƴaƴan itatuwa, an gano cewa wasu ƴan kasuwa ba sa bin waɗannan ƙa'idoji.

Maimakon haka, suna amfani da hanyoyin da a suka dace ba wajen sarrafa ƴaƴan itatuwan kafin su kai su kasuwa.

Ya ya kamata a nuka ƴaƴan itatuwa?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana iya sa ƴaƴan itatuwa su nuna ta hanyar da ba ta ɗabi'a ba, ta amfani da gas ɗin ethylene, wanda ake samarwa daga sinadarin ethephon, idan aka bi ƙa'idojin da suka dace.

Sai dai, Samantha Karunaratne, ta ce wasu ƴan kasuwa suna karya waɗannan ƙa'idoji ta hanyar fesa sinadarin ethephon kai tsaye a kan ƴaƴan itatuwa ko kuma nunar da su cikin ruwan da aka gauraya da wannan sinadari.

Ta kuma jaddada cewa hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa yawan mu'amala da sinadarai da ake amfani da su wajen nunar da ƴaƴan itatuwa na dogon lokaci na iya haifar da cututtuka kamar nau'o'in cututtukan zuciya ko ciwon daji da makamantansu.

Kazalika, amfani da "kabidi" (calcium carbide), wanda a baya ake amfani da shi wajen hanzarta nunar ƴaƴan itatuwa ta hanyar da ba ta dace ba.

Tun a watan Oktoba 1993 gwamnatin Sri Lanka ta fitar da sanarwar haramta saida sinadarin a ɗaukacin ƙasar Sri Lanka, an kuma kafa doka mai lamba 788/7.

Saboda haka, amfani da wannan sinadari wajen sarrafa ko nuna ƴaƴan itatuwa laifi ne a ƙarƙashin doka.

Illa ga lafiya

Dokta Renuka Jayatissa, shugabar Sashen Abinci da Gina Jiki a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta shaida wa BBC Sinhala cewa, amfani da wasu sinadarai don nunar ƴayan itatuwa ta hanyar da ta saɓa wa ɗabi'a na iya yin illa ga lafiya idan mutum ya dade yana hulɗa da su.

Likitar ta kuma bayyana cewa dokar Abinci ta tanadi hanyoyin da suka kamata a bi wajen nunar ƴaƴan itatuwa a cikin muhalli mai tsafta da aminci, domin tabbatar da cewa sun dace da amfanin ɗan Adam.

"Sinadaran da ake amfani da su kan iya shiga hanta kuma su taru a cikinta. Hakan na ƙara haɗarin kamuwa da cutar daji," in ji ta.

Ta ya za ku gane ƴaƴan itatuwan da aka nuka da sinadari?

A cewar Upul Rohana, Muƙaddashin Shugaban Ƙungiyar Masu Binciken Lafiyar Jama'a ta Sri Lanka, akwai hanyoyi da dama da za a iya gane ƴaƴan itatuwan da akai amfani da nuna gaushinsu ta hanyar da ba ta dace ba.

"Ɗaya daga cikin hanyoyin gane hakan, ita ce hanyar kallo wato duba ko 'ya'yan itacen suna da ƙamshi da kuma launin da ya dace da su."

Ya kuma bayyana cewa: "A bincika ko akwai tabo, ko ragowar sinadarai, ko wata illa a jikin ƴaƴan itacen."

"A wasu lokutan, ko bayan an sa ƴaƴan itacen sun nuna ta hanyar da ba ta ɗabi'a ba, fatarsu kan koma rawaya. Amma tsarin canza sinadarin carbohydrates da ke cikin ƴaƴan itacen zuwa glucose ba ya gudana yadda ya kamata''.

Saboda haka, fatar wajen kaɗai ce ke zama rawaya alhali cikin bai nuna ba. Ana iya tabbatar da hakan ta hanyar yanka su."

Ya jaddada cewa ya kamata a yi amfani da ƴaƴan itatuwan da suka nuna yadda ya dace na ɗabi'a ba.

Muƙaddashin shugaban ya ƙara da cewa, duk da yake ana iya amfani da hanyoyin nunar da wasu daga cikin kayan itace da suka haɗa da ayaba da mangwaro, doka ta haramta amfani da irin waɗannan hanyoyi ga wasu nau'ukan ƴaƴan itatuwa da dama.